Real Madrid ta doke Fenerbahce 5-3

Asalin hoton, NurPhoto
A karshe dai Real Madrid ta samu nasara a wasa biyar din da ta fafata tun lokacin da ta fara atisaye, inda ta doke Fenerbahce da ci 5-3 a wasan neman na uku na cin kofin Audi a Jamus.
Wannan ce nasara ta farko da ta yi tun da ta fara atisayen tunkarar kakar wasanni ta bana.
Karim Benzema ne ya zura kwallo uku rigis a wasan, wanda ya zo kwana guda bayan Tottenham ta doke Madrid din da ci daya mai ban haushi.
Spurs ce dai ta lashe kofin bayan doke mai masaukin baki Bayern Munich da ci 5-6 a bugun fanareti bayan da suka tashi wasa 2-2.
Garry Rodrigues ne ya fara ci wa Fenerbahce, wadda Bayern ta lallasa 6-1 a ranar Talata, kwallo jim kadan da fara wasan.
Benzema ne ya rama wa Madrid sannan ya kara wata.
Nabil Dirar ya sake ci wa Fenerbahce kafin Benzema ya ci ta uku bayan da Lucas Vazquez ya bugo masa kwallo.
Ozan Tufan ya sake zura kwallo a ragar Madrid kafin Nacho da Mariano suka sake ci wa Real Madrid kwallo daya-daya.











