Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United ta dauki Wan-Bissaka
Manchester United ta cimma yarjejeniyar daukar dan kwalllon Crystal Palace, Aaron Wan-Bissaka.
Cinikin dan wasan mai tsaron baya mai shekara 21, zai kai fam miliyan 50, kuma dan kwallon tawagar Ingila ta matasa 'yan shekara 21 zai je a gwada lafiyarsa kafin ya fara hutu.
United ta bai wa Wan-Bissaka kwantiragi mai tsawo da zai dunga karbar fam dubu 80 a duk mako.
Dan wasan na karbar fam dubu 10 a kowanne mako, albashi mafi karanci a kungiyar Palace ga dan wasan da ke buga mata kwallo akai-akai.
Idan United ta kammala cinikin, Wan-Bissaka zai zama na biyu da Ole Gunnar Solskjaer ya dauka a bana, bayan Daniel James daga Swansea kan fam miliyan 15 a farkon watan Yuni.