Afcon 2019: Najeriya ta kai zagayen gaba

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta zama ta farko da ta kai zagayen gaba a gasar cin Kofin Kasashen Afirka da ake yi a kasar Masar.

Super Eagles ta yi nasara ne a kan Guinea da ci daya mai ban haushi a wasa na biyu na rukuni na biyu da suka fafata a Alexandria.

Najeriya ta ci kwallon ne ta hannun Kenneth Omeruo a minti na 73.

Da wannan sakamakon Najeriya ta hada maki shida a wasa biyu, bayan da ta ci Burundi 1-0 ranar Asabar.

Najeriya za ta buga wasa na uku da Madagascar ranar Lahadi 30 ga watan Yuni a filin wasa na Alexandria.

Ita kuwa Guinea tana da maki daya a wasa biyu ne, bayan da ta tashi 2-2 da Madagascar a ranar Asabar a karawar rukuni na biyun.

Guinea za ta fafata da Burundi ranar Lahadi 30 ga watan Yuni a wasa na uku na cikin rukuni na biyu.

A ranar Alhamis 27 ga watan Yuni ne Burundi za ta kara da Madagascar a daya wasa na biyu a rukuni na biyu a Alexandria.