Dalilan da za su hana Mbappe barin PSG

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Kylian Mbappe daya ne daga cikin fitattun 'yan wasan tamaula da kungiyoyi da dama za su so mallaka a kaka mai zuwa.

An dade ana ta rade-radin cewar Mbappe zai bar Paris St Germain. Shin ko dan wasan na tawagar Faransa zai koma wata kungiyar nan kusa domin murza-leda? Muhammed Abdu Mamman Skipper ya tattaro dalilan da za su iya hana dan wasan matsawa ko'ina.

Paris Saint-Germain ta shirya hanyoyin da za ta yi nasara a fagen kwallon kafa a nahiyar Turai musamman gasar cin kofin Zakarun Turai, inda ta gina kungiyar kan kokarin da Neymar da Mbappe za su yi mata.

Mbappe ya koma Parc des Princes a matsayin dan wasa mafi tsada bayan Neymar a tarihin tamaular duniya, kuma nan da nan ya zama tauraro a birnin Paris.

Ana kaunar yadda yake murza-leda domin yana da magoya baya da dama a ciki da wajen kasar, sannan ya taimaka wa tawagar kwallon kafar Faransa lashe kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018.

Real Madrid ta fada karara cewa ba za ta yi zawarcin Mbappe ba idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon kafa ta Turai, yayin da a Paris ake hasashen ba na sayarwa ba ne.

Hatta a wajen filin wasa, PSG na bin duk wata hanya da za ta rike Mbappe, duk kuwa irin kudin da za a taya dan kwallon tare da abokin wasansa Neymar.

'Yan wasan biyu sun zama kamar David Beckham a Real Madrid a lokacin da ya taka leda a Spaniya, suna samar wa da kungiyar kudi da gasar Lique 1 da kasar Faransa baki daya.

Duk da cewar 'yan wasan na da matsaloli da buri a gabansu, amma kudin shiga da ake samu kan tallace-tallace da kuma karuwar sabbin 'yan wasa na kara wa gasar ta Faransa kudi da kima.

A baya-bayan nan PSG ta saka hannu kan kwantiragin tallar wani Otal Accor, wanda zai maye gurbin yarjejeniyar da suka kulla da Emirates a rigunan da 'yan wasa ke sakawa.

PSG za ta rika karbar Yuro miliyan 60 a kowacce kakar tamaula a sabuwar yarjejeniyar, kuma babbar yarjejeniya mai tsoka da aka taba yi a tarihin kwallon kafar Faransa.

Haka kuma kungiyar tana sa ran karin tallace -tallace da za su shigo mata a kaka mai zuwa ta dalilin zakakuran 'yan wasa kamar Mbappe.

Shugaban PSG, Nasser al Khalaifa ya tabbatar cewa Mbappe fitaccen dan wasa ne a fagen kwallon kafa a duniya, amma ba zai bari ya yi ragaita tsakanin gasar kasashen Turai ba.

Shi kansa Mbappe ya tabbatar wa da magoya baya cewa zai ci gaba da zama a PSG, kuma ba ya maganar makomarsa a kungiyar domin hankalin kowa ya kwanta a kansa.

Sai dai wasu ba za su yadda cewa Mbapppe ba zai bar PSG ba, domin dadi ba ya zaunar da dan kwallo a kungiya.

Duk da cewa dan wasan ya ce zai ci gaba da wasa a Paris, lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan.