Arsenal ta taka wa United burki

Arsenal United

Asalin hoton, Getty Images

Wannan wata babbar hobbasa ce da Arsenal din ta yi a kokarinta na samun gurbin zuwa gasar zakarun nahiyar Turai.

A bangare guda kuma rashin nasarar da Manchester United ta yi shi ne na farko a filin wata kungiya, tun bayan kama aikin sabon kociyanta Ole Gunnar Solkjaer.

Yanzu haka kungiyar ta Arsenal na a matsayi na hudu ne da maki 60, inda take bin kungiyar Tottenham mai maki 61, bayan buga wasa 30 a gasar kofin Premier.

Wannan ne karo na biyu da kungiyoyin suka kara a gasar Premier kuma karo na uku da suka yi gumurzu a kakar bana, wasa na 230 da suka kece raini a tsakaninsu.

Cikin wasannin da suka yi a a dukkan karawar tsakaninsu, United ta yi nasara a karawa 97, Arsenal ta ci 82 da canjaras 51.

A wasan farko na kakar bana tsakanin United da Arsenal sun, an tashi ne 2-2 a gasar Premier da suka fafata a Old Trafford ranar 5 ga watan Disamba, sai dai United ta doke Arsenal 3-1 a Emirates a FA Cup.

Yanzu haka dai United tana ta biyar a kan teburin Premier da maki 58.