Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da gaske EFCC na farautar 'ya'yan Atiku?
Hukumar EFCC ta musanta zargin da PDP ta yi cewa ta kai samame a gidan 'ya'yan dan takararta na shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar.
A wasu jerin sakwanni da ta wallafa a Twitter, EFCC ta ce ta kai farmaki ne a gidan 'ya'yan tsohon gwamnan jihar Abia Theodore Orji a Maitama wanda take gudanar da bincike a kansa.
Kuma 'ya'yan tsohon gwamnan na Abia suna makwabtaka ne da Aliyu da Mustapha Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam'iyyar PDP a zaben 2019.
Sai dai kuma Jam'iyyar PDP ta yi zargi cewa, EFCC ta kai samamen ne a gidan 'ya'yan na Atiku bisa umurnin fadar shugaban kasa.
Fadar shugaban kasa ta musanta zargin, inda mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya soki PDP da yada labaran karya.
"A Najeriya yanzu babu wanda ya fi yada labaran karya kamar jam'iyyar PDP," in ji Garba shehu a sakon da ya wallafa a Twitter.
EFCC ta ce binciken da take yi kan tsohon gwamnan Abia Theodore Orji, kan halatta kudaden haramun ne ya shafi 'ya'yansa.
Hukumar ta ce ta kai ga kama 'ya'yan tsohon gwamnan ne ta hanyar bin sawun wasu manyan motocin da aka ce nasu ne.
Kuma a lokacin da take tatsar bayanai ne suka bayyana mata gidan da suke zama a Abuja da ta kai samame a ranar Asabar.
EFCC ta ce bincikenta da ta gudanar bai shafi bangaren gidan 'ya'yan Atiku ba.
Sai dai a cikin bayanan da ta wallafa a Twitter, hukumar ba ta ce ko ta leka sashen gidan 'ya'yan Atiku ba da suke gida guda da 'ya'yan tsohon gwamnan na Abia da ta kama.