Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari da Atiku: Amurka da EU na son a rungumi zaman lafiya
Amurka da Tarayyar Turai da kuma wasu gwamnatocin kasashen waje sun bukaci jam'iyyun siyasar kasar bin tsarin da zai kai ga tabbatar da zaman lafiya da gudanar da sahihin zabe da adalci.
Sanawar da aka aika wa BBC ta kunshi sa hannun jakadancin kasashe 25 a Najeriya da suka hada da Birtaniya da Faransa da Jamus, inda suka yi kira da kuma gargadi ga 'yan siyasa da 'yan Najeriya baki daya bayan soma yakin neman zaben 2019.
Kasashen sun bukaci 'yan siyasa su kaucewa kalaman batanci da nuna kiyayya ga abokan hamayya da kuma duk wani abu da zai kai ga haifar da tashin hankali.
Sun kuma jaddada muhimmacin sake kulla yarjeniyar 2015 ta zaman lafiya da ta kai ga sauyin shugabanci daga jam'iyya mai mulki zuwa ta hamayya ba tare da an samu wani tashin hankali ba.
Kasashen sun ce a matsayinsu na aminnan Najeriya da mutanen kasar, za su sa ido sosai ga yakin neman zabe, kuma ga wanda zai lashe zaben, 'yan Najeriya ne za su tantance haka.
Amma sun ce damuwarsu ita ce bin tsarin da zai kai ga gudanar da sahihin zabe ba tare da tashin hankali ba.
Sun yi kira ga 'yan siyasa da magoya bayansu su kaucewa kalaman batanci da nuna kiyayya ga abokan hamayya da zai kai ga haifar da tashin hankali inda suka ce yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a zaben 2015 ta taka rawa sosai wajen kaucewa haka, kuma za su yi maraba idan za a sake daukar irin wannan matakin.
Kasashen sun bayyana matukar damuwa kan barazana da katsa-landan da sayen kuru'u a wasu zabukan gwamnoni da aka gudanar kuma sun ga irin rashin adalci da aka yi a rikici a zabukan fitar da gwani da jam'iyyun siyasa suka gudanar, sannan sun ga yadda aka shiga gaban mata aka hana ma su tsayawa takara.
Sun bayyana cewa dole a bar hukumar zabe ta INEC ta gudanar da aikinta kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar ba tare da matsin lamba daga waje ba.
Sun kuma yin kira ga Jami'an tsaro wajen tabatar da tsaro da kuma yin adalci ba tare da tauye wani bangare ba.