Buhari da Atiku sun taya Super Falcons murna

Lokacin karatu: Minti 1

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Super Falcons nasarar lashe kofin Afirka a kasar Ghana.

Matan na Najeriya sun lashe kofin Afrika ne karo na uku a jare kuma karo na tara a tarihi bayan sun doke matan Afirka ta kudu Banyana Banyana ci 4-3 a fanareti.

Shugaban Najeriya ya taya Super Falcons murna a wani sakon da ya wallafa a Twitter.

A cikin sakon, shugaban ya ce yana ma su murna sun tsallake zuwa gasar cin kofin duniya a Faransa a badi bayan sun lashe kofin Afirka karo uku kuma karo na tara a tarihi.

Dan takarar shugaban kasa a Jam'iyyar hamayya ta PDP Alhaji Atiku Abubakar shi ma ya taya Super Falcons murna a Twitter.

Najeriya da Afrika ta kudu da kuma Kamaru ne za su wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya da za a yi a badi a Faransa bayan sun zo matsayin na daya da na biyu da kuma uku a gasar cin kofin Afirka da aka kammala a Ghana