Man United za ta farfado - Luke Shaw

Asalin hoton, Others
Luke Shaw ya ce nan da wani dan lokaci Manchester United za ta sake farfadowa, bayan da ya kulla sabuwar yarjejeniya ta shekara biyar wadda zai rika karbar albashin fam dubu 150 a duk sati.
A bazara ta gaba ne kwantiragin dan wasan mai shekara 23 zai kare, inda rashin kokari da kuma rauni suka sa sau 75 kawai ya taka wa kungiyar leda.
Shi kansa ya yarda cewa kusan abu ne mai wuya a wasu lokutan a shekarar da ta wuce, a ce kungiyar ta sabunta kwantiraginsa.
Sai dai kuma dan wasan na baya ya farfado har ake sa shi a wasa kusan a ko da yaushe a bana, har ma wasu ke kiran da a sake dawo da shi cikin tawagar kasarsa.
Shaw ya nuna farin cikinsa kan yadda ya ce Mourinho ya taimaka masa yake dawowa kan ganiyarsa, wanda kan haka yake ganin nan da dan lokaci kungiyar tasu za ta sake dawowa kan nasara.
Ya ce suna da tarin 'yan wasa masu kyau sosai, wadanda kuma akwai matasa a cikinsu da dama da suka zaku su ci kofuna.
A shekara ta 2014 ne dan bayan na Ingila ya koma United a kan fan miliyan 27 bayan da ya zama daya daga cikin gwanayen matasan 'yan baya a gasar Premier a kungiyar Southampton.







