Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan bindiga sun kashe 'yan canjin kudi hudu a Fatakwal
'Yan sandan jihar Rivers na gudanar da bincike dangane da kisan gillar da ake zargin an yi ma wasu masu hada-hadar musayar kudaden waje a Fatakwal, babban birnin jihar.
Ana zargin wannan al'amarin wani cune ne, domin kisan ya biyo bayan wata takaddamar rufe wata kasuwa ne tsakanin mamatan, da wasu jam'ian gwamnatin Ribas, domin maharan ba su dauki komai ba bayan kisan da suka kaddamar.
Sai dai jami'an ma'aikatar muhallin da ake zargi ba su kai ga cewa komai ba tukunna, inda BBC ta yi kokarin tuntubarsu amma hakan bai samu ba.
Amma rundunar 'yan sandan ta ce bincike ne kawai zai fayyace ainihin abin da ya auku.
Wadanda aka kashen sun hada da Yusuf Zaki da Muhammad Rabi'u da Ahmad A. Tukur da Abubakar Tugga.
An dai kashe mutanen ne gidansu da ke layin Orazu na karamar hukumar Obiako da ke Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.
Tuni dai aka yi jana'izar mutanen a kauyensu da ke Jugudu a karamar hukumar Giade ta jihar Bauchi, da ke arewa maso gabashin kasar.
Adamu Usman, daya daga cikin mutanen da aka kai wa harin, wanda kuma ya tsallake rijiya baya, ya yi karin bayani, game da lamarin ya auku a daren Laraba:
"Wannan lamari ya auku ne bayan wata takaddama a kan rufe wata kasuwa da muke harkokinmu na canji kudin waje, da kuma furta wata barazana da wani jami'in gwamnati ya yi mana."
Ya kara da cewa: "Muna zaune muna hira a barandar gidan yusuf sai kawai muka ga mutum uku a kanmu dauke da bindigogi, suka bude wuta suka fara harbi. Ni dai na tashi na zura da gudu suka biyo ni sai na fada wata kwata,
"Sun ci gaba da harbi amma Allah ya taimake ni wani langa-langa ya kare ni don haka ba su same ni ba. Da aka jima sai na fito lokacin sun tafi, amma na tarar sun kashe sauran 'yan uwana hudu.
"Daga nan sai muka sanar da 'yan sanda," in ji Adamu Usman
DSP Omoni Nnamdi, shi ne kakakin rundunar 'yan sandan jihar Rivers, kuma ya shaida wa BBC cewa rundunar ta dukufa a kokarinta na zakulo mutanen da suka kashe mutanen hudu:
"Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kashe wasu mutane hudu, kuma bayan aukuwar hakan aka anakarar da mu. Nan da nan muka tura jami'anmu wajen, amma lokacin da suka isa maharan sun tsere."
Ya kara da cewa "Kwamishinan 'yan sanda ya sa a shiga gudanar da bincike kan lamarin, tare da neman mutanen da ake zargi ruwa a jallo."
Mista Nnamdi ya kara da cewa, "Bincike zai fayyace yadda lamarin ya kasance, ba ma so mu yi kintace, ko mu ambata abin da ba shi kenan ba. Amma dai na san a karshen binciken za a gano gaskiyar ainihin abin da ya auku."
Jami'in 'yan sandan dai ya bayar da tabbacin ba za su yi kwance da sirdi kan lamarin ba.
Yusuf Zaki, wanda dan takarar dan majalisar jiha ne karkashin jam'iyyar APC, ya bar mata biyu da 'ya'ya takwas, shi kuma Muhammad Rabi'u ya mutu ya bar matarsa daya da 'ya'ya hudu.
Adamu A. Tukur da Abubakar Tugga kuwa kowannensu ya bar mata daya ce amma babu 'ya'ya.