Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kare ya kashe yar shekara daya a Australia
Wata yarinya mai shekara daya ta rasu bayan wani kare ya kai mata hari a Ostraliya, in ji 'yan sanda.
Karen ya farwa yarinyar ne inda ya rika cizonta a wani gida da ke unguwar Neerin Junction a gabashin garin Melbourne da ke jihar Victoria..
An kira 'yan sanda da ma'aikatan jinya zuwa gidan da safiyar ranar Laraba sai dai sun kasa farfado da yarinyar .
Kafofin watsa labarai a Ostraliya sun ce karen ya farwa yarinyar ne a fuska.
Mahaifiyar yarinyar ta yi kokarin kubatar da yarta daga hannun karen amma hakarta ba ta cimma ruwa ba in ji kafar watsa labarai ta Seven News.
'Yan sanda sun ce tuni jamian karamar hukuma suka kwace karen domin tsare