Mohamed Salah: Kun san Balaraben da ya 'gagari' Turawa?

Asalin hoton, Getty Images
Kwanaki biyu bayan Mohamed Salah ya karbi kyautar gwarzon dan wasan Ingila na bana, dan wasan na Masar ya sake nuna kansa a Turai, a matsayin wanda zai iya zama gwarzon dan wasan duniya.
Salah ya kayatar da magoya bayan Liverpool da duk wani masoyin kwallon kafa a duniya a yayin da Liverpool ta lallasa Roma da ci 5-2 a gasar zakarun Turai a karawar farko na zagayen daf da na karshe.
Kwallo biyu Salah ya ci sannan ya bayar aka ci biyu a daren da magoya bayan Liverpool ba za su taba mantawa ba a Anfield.
Yanzu kwallo 43 Salah ya ci a wasa 47 a kakar bana, kwazon da ya sa wasu ke kwatanta dan wasan da fitattun 'yan kwallo irinsu Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da kuma Neymar.
Wannan ya sa wasu ke ganin Salah ya cancanci ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya ta Ballon d'Or.
Abin mamaki shi ne yadda wannan Balarabe, dan kasar Masar, ya zo ya daga tuta a cikin Turawa, a cewar wasu masu sharhi kan al'amuran wasanni.
Babu wani Balarabe da ya taba yin irin bajintar da Mo Salah yake yi.
Tsohon dan wasan Wales, Robbie Savage ya shaida wa BBC cewa: "Dole ne a ba shi Ballon d'Or," bayan kwallo biyun da Salah ya jefa a ragar Roma.
Ya ce Salah yana da kyau, "Kada a damu da kyautar PFA da ya lashe, kawai a ba shi Ballon d'Or."
Tsohon dan wasan Liverpool Robbie Fowler wanda aka taba zaba domin lashe kyautar a 1996, ya bayyana Salah a matsayin "dan wasa mai ban mamaki".
Kishirwar wasan karshe a Kiev zai tabbata idan har Liverpool ta kammala aikinta a Rome a karawa ta biyu.
Idan an kammala gasar zakarun Turai ne kuma, Salah zai sake nuna kansa a duniya, a yayin da zai jagoranci Masar a gasar cin kofin duniya a Rasha.
Salah ne dan wasan Afirka na farko da ya ci kwallo akalla tara a kakar wasa a tarihin gasar zakarun Turai.
Salah ya jefa kwallo a raga a wasa biyar a jere da aka fara da shi a gasar zakarun Turai.
Ta yaya za a kwatanta Salah da su Ronaldo?
Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo da Lionel Messi na Barcelona da kuma Neymar na Paris St-Germain su ake gani mafiya shahara a duniyar tamaula a yanzu, amma ta yaya za a kwatanta kwazonsu a bana da Salah?












