Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Alex Ferguson ya jinjinawa Wenger
Tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya jinjinawa kocin Arsenal mai barin gado Arsene Wenger.
A ranar Juma'a ne kocin dan kasar Faransa ya bayyana cewa zai bar Gunners a karshen kakar bana.
Wannan na nufin zai tafi shekara guda kafin kwantiraginsa ta kare.
Ferguson ya ce Wenger na "daya daga cikin kociyoyi mafiya kwarewa a tarihin gasar Premier".
Ya kara da jinjinawa "basirarsa, da kwazonsa da kuma jajircewarsa".
Ferguson da Wenger sun shafe shekaru suna hamayya a lokutan da kungiyoyinsu suka mamaye gasar Premier na tsawon shekaru.
Wenger ya lashe gasar Pemier uku da kuma kofin FA bakwai - wanda babu wanda ya kaishi lashe kofin na FA.
A nasa bangaren Ferguson ya lashe gasar Lig sau 13 a shekara 26 da ya shafe a Manchester United kafin ya yi ritaya a 2013.
Henry na daya daga cikin wadanda ake hasashen za su iya maye gurbin Wenger.
A yanzu shi ne mataimakin koci na biyu a tawagar kwallon kafa ta kasar Belgium.
Tsohon dan wasan Arsenal Thierry Henry ya ce Wenger ya bar "tarihin da ba za a iya gogewa ba".