Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kashe jagoran IS na yankin Asia
Dakarun soji a kudancin Philippines sun ce sun kashe Isnilon Hapilon, wanda aka fi sani da Abu Sayyaf kuma jagoran mayakan IS a kudu maso gabashin Asiya.
Sojoji sun ce an kashe Hapilon wanda ke cikin jerin 'yan ta'adda da Amurka ke nema ruwa a jallo ne a Marawi tare da wani dan ta'adda mai suna Omar Maute.
Wani yanki na birnin ya na karkashin ikon mayakan ne tun lokacin da aka kai wani mummunan hari a watan Mayu.
An samu rahotanni kashe mayakan ne yayin da dakarun soji ke kara kaimi don kawo karshen fadan da aka shafe watanni ana gwabzawa da mayakan.
Yankin ya kasance tamkar sansani ga kungiyoyin masu kaifin kishin Islama, wadanda da dama daga cikin su suka kafa kungiyar IS a shekarun baya-bayan nan.
Janaral Ano ya ce har yanzu dakarun sojin na yaki da mayakan IS da dama a yankin, kuma sun ceto kimamin mutum 20 da aka yi garkuwa da su.
Ya kara da cewa kwararru da kuma tsofaffin mayakan ne suka tabbatar da gawar shugabannin mayakan biyu.
Sakataren tsaro Delfin Lorenzana ya shaida wa manema labarai cewa bayan an bayar da rahoton mutuwar Hapilon, za su bayar da sanarwar takaita zirga-zirga a yankin na tsawon kwana biyu.
Ya kara da cewa, yanzu dai ana ci gaba yi wa gawar mutanen biyu bincike don tabbatar da kwayoyin halittar su.