Kenya za ta hukunta masu sayar da kayan marmari a leda

Mutum 11 aka kama da laifin mallakar ledar da aka haramta yin amfani da ita wajen sayer da kayan marmari a birnin Mombasa da ke Kenya, kamar yadda jaridar Business Daily ta bayyana.

Jaridar ta kara da cewa, an kama mutanen da suka hada da masu sayar da kayan marmari da kuma rake a bakin hanya wadanda suke amfani da ledar, bayan da jami'an ma'aikatar kula da muhalli suka yi musu dirar mikiya.

Sai dai Mai shari'a Martin Rabera ya yi musu afuwa tare da bayyana cewa:

"Kotu ta muku afuwa ne saboda ku ne masu laifi na farko da aka kama. Kodayake muna jan kunnenku wadanda ake tuhuma, idan muka kara samunku da karya wata doka ba za ku ji da dadi ba".

Har ila yau jaridar ta ruwaito mai shigar da kara Jane Alango yana cewa: "Baya ga gurbata da muhalli da ledar take yi, tana sanadiyyar kashe dabbobi da dama. Mutane suna iya yin amfani da kwanduna da sauran mazubi ba leda ba."

Wadannan mutanen za su zama "darasi a wurin wadanda har yanzu suke amfani da haramtacciyar ledar.

A watan Agusta ne kasar Kenya ta saka dokar haramcin yin amfani da ledar.

Sabuwar dokar ta tanadi tarar da ta kai dala 38,000 ko kuma daurin shekara hudu a gidan yari ga duk wanda aka kama yana sayar da ledar ko yinta ko kuma aka same shi da ita.