Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutum fiye da 270 aka kashe a harin Mogadishu
Yawan mutanen da suka mutu sanadiyyar mummunan harin bam din da aka kai kasar Somaliya ya kai 276, kamar yadda 'gwamnati ta bayyana.
Ministan watsa labarai na Somaliyar ya ce mutum 300 sun ji raunuka a fashewar da ta faru a wani wuri da ba ya rabuwa da cunkuson jama'a,wadda ta lalata otel -otel da ofishoshin gwamnati da kuma wurin cin abinci.
Gwamnati ta dora alhakin harin kan mayakan Al shabaab wanda shi ne mafi muni tun bayan da kungiyar ta fara tada kayar baya shekaru goma da suka gabata.
A ranar Asabar ne wata babbar motar kaya da aka daura wa bama-bamai ta fashe da su a kofar shiga wani otel a birnin Mogadishu.
Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin tukuna, amma birnin ya saba fuskantar hare-haren kungiyar al-Shabab wadda take yaki da gwamnatin kasar.
Yawan wadanda suka "mutu zai iya ci gaba da karuwa", kamar yadda wani jami'in dan sanda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Wannan ne hari mafi muni a kasar tun bayan wani hari da kungiyar al-Shabab ta kai a shekarar 2007.
Shugaban Kasar Mohamed Abdullahi Farmajo ya ayyana kwana uku na makokin wadanda harin ya rutsa da su.
'Yan sanda sun ce mutum biyu sun mutu a wani hari na biyu a wata unguwa mai suna, Madina wadda take birnin.
An ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su sun taru, suna neman 'yan uwansu a wurin da aka kai harin a safiyar ranar Lahadi, kamar wata kafar yada labaran kasar ta ruwaito.
Bayan harin farko, jami'in dan sanda Mohamed Hussein ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa:
"An yi amfani da wata babbar mota ne wajen kai harin. Ba mu san adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba tukuna saboda wuta ce ke ci gaba da ci a wurin."
Wakilin BBC ya ce ginin Safari Hotel ya ruguje, kuma ana zaton ya danne mutane da dama.
Wani mazaunin unguwar Muhidin Ali ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: "wannan ne harin bam mafi muni da na taba gani, harin ya lalata duka wurin".
Karanta wadansu karin labarai