Ogenyi Onazi ya bar kungiyarsa kan rashin albashi

Dan wasan Najeriya Ogenyi Onazi ya soke kwantiraginsa da kungiyar Trabzonspor ta kasar Turkiyya saboda rashin biyansa albashi.

Onazi mai shekara 24, ya yi wa kungiyar wasa a watanni biyu na karshen kakar da ta kare ba tare da albashi ba, lamarin da ya saba ka'idar kwantigarinsa, kuma yanzu yana neman sabuwar kungiya.

Wata 11 da ya gabata ne Onazi ya koma Trabzonspor daga kungiyar Lazio ta Italiya a kan yarjejeniyar zaman shekara hudu.

A kwanan nan ne dan wasan Algeria Carl Medjani da kuma dan wasan gaba na Ghana Majeed Waris su ma suka bar kungiyar ta Turkiyya a kan irin wannan matsala.