Commonwealth: Okagbare ta kafa tarihi

Asalin hoton, AFP
'Yar Nigeria Blessing Okagbare ta kafa sabon tarihi a tseren mita 100 na gasar Commonwealth inda ta lashe tseren a cikin dakikoki 10.85.
Okagbare ta samu nasara a tseren inda ta shiga gaban Veronica Campbell-Brown da kuma Kerron Stewart wacce ta samu kyautar tagulla.
'Yar Ingila, Asha Philip ce ta zama ta hudu a tseren.
Okagbare na da damar samun nasara a tseren mita 200 da kuma tsallen badake a nan gaba.
A halin yanzu Nigeria ce ta goma a jadawalin lambobin yabo inda ta samu kyautuka 10 ciki hadda zinare uku.






