C'wealth: Za a fara wasanni Laraba

Commonwealth Games
Bayanan hoto, Wannan ce gasa mafi girma da Scotland zata karbi bakunci

Birnin Glasgow ya shirya karbar bakuncin wasannin Commonwealth, da za'a bude ranar Laraba 23 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Agusta.

Birnin Edinburgh ya taba daukar bakuncin wasannin 1970 da 1986, sai dai wannan ne karon farko da Scotland za ta karbi bakuncin gasar wasanni mafi girma.

Gasar wasannin bana da aka yiwa lakabi da "al'umma, wurare da kayatarwa" za ta sami bakuncin 'yan wasa 4, 084 daga kasashe 71 da zasu barje gumi a wasanni 17.

Filin wasa na Celtic Park ne zai karbi bakuncin bude wasanni ranar 23 ga watan Yuli, yayin da Hampden Park ya karbi bikin rufe gasar wasannin ranar 3 ga watan Agusta.