Mo Farah ya yi nasara a karo na biyar

Zakaran tsere dogon zango na Burtaniya Mo Farah ya yi nasara a karo na biyar a jere a tseren kilomita dubu goma da aka yi a ranar Litinin a birnin Landan.
Dan tseren wanda yake da lambar zinari biyu a wasanni Olympics da aka yi a bara a birnin London ya yi nasara ne a tseren cikin mintuna 29 da dakikai 13.
Shine dai kan gaba a tseren na tsawon shekaru biyu a gasar tseren duniya da aka yi a Daegu.
Ya ce yayi amfani da tseren ne domin shirin gasar tsere ta duniya da za a yi a watan Agusta a birnin Moscow.






