Lafiya Zinariya: Wayewa ce ta sa mata suka fi maza zuwa ganin likitan kwakwalwa?

Bayanan sautiLafiya Zinariya: Wayewa ce ta sa mata suka fi maza zuwa ganin likitar kwakwalwa?

Ku latsa hoton da ke sama don sauraron shirin:

Likitoci a fannin lafiyar kwakwalwa sun ce matsananciyar damuwa na janyo kisan kai da shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin al'umma.

Sai dai wasu mata masu dubban mabiya a shafin sada zumunta na da ra'ayin dandalin na kawo mafita ga matan da ke fuskantar rashin lafiyar kwakwalwa.

Masana a fannin kiwon lafiya sun ce mata sun fi maza fuskantar matsalar matsananciyar damuwa.

Hakan na zuwa ne yayin da ake nuna bukatar karin fadakarwa ga al'umma cewa, rashin lafiyar kwakwalwa matsalar kiwon lafiya ce da ke bukatar ganin likita.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce rashin lafiyar da ke samun kwakwalwar bil'adama ta kasu kashi-kashi.

Sai dai matsananciyar damuwa ita ce ke kan gaba a fadin duniya.

Inda hukumar ta yi kiyasin cewa, mutane miliyan 264 na fama da matsananciyar damuwa a duniya.

Haka kuma matsalar da hukumar ta bayyana a matsayin gama-gari, ta kasance cikin jerin matsalolin kiwon lafiya da ke kan gaba, wajen nakasa mutane a duniya.

A cewar hukumar matsananciyar damuwa na kai wa ga kisan kai, kuma ana samun fiye da mutane dubu 700 da ke kashe kansu duk shekara a duniya.

Yayin da 'yan shekara 15 zuwa 29 kuma kisan kai ya zamo hanya ta hudu da suka fi mutuwa.

Sai dai hukumar ta ce rashin lafiyar kwakwalwa matsaloli kiwon lafiya ne da za a iya magance su ba tare da kashe makudan kudade ba.

Amma kuma ana samun wagegen gibi a tsakanin masu samun kulawa da kuma wadanda suke bukatarta.