Lafiya Zinariya: Magungunan tazarar haihuwa da illolinsu

Bayanan sautiLafiya Zianariya kan magungunan tazarar haihuwa da illolinsu

Ku latsa hoton da ke sama don sauraron shirin:

Kungiyar likitocin mata ta Amurka Acog, ta yi bayani kan muhimmancin samun kulawa ga mace tsakanin haihuwa da daukar ciki.

Samun kulawa a wannan tsakani, yana da tasiri matuka ga sauran rayuwar mace, musamman ta fuskar kiwon lafiyar.

Daukar ciki na farko a cewar makalar, zai iya kasancewa zakaran gwajin dafi, na abin da ka iya je ya dawo.

Domin a lokacin da mace ke da ciki ta kan iya gamuwa da wasu matsaloli na kiwon lafiya, wadanda za su iya shafar rayuwarta nan gaba.

Cututtuka kamar cutar jijjiga da ciwon suga da hawan jini da rashin girman dantayi a ciki, duka matsaloli ne da mace ke iya gamuwa da su a lokacin goyon ciki.

Sannan dukkansu ana alakanta su da wasu matsalolin kiwon lafiya da mace kuma za ta iya samu nan gaba a rayuwarta.

Haka kuma wasunsu matsaloli ne da za su iya zarcewa bayan ta haihu.

Makalar ta bayyana cewa don haka yana da muhimmanci mace ta samu kulawar da ta dace bayan haihuwa.

A wannan tsakanin na bayan haihuwa kuma kafin daukar wani cikin ne za a magance matsalolin da suka taso.

Sannan a wannan dan tsakanin ne ya kamata mace ta samu ingancin lafiyar kwakwalwa da na jikinta baki daya.

Wanda hakan na taimakawa gaya, wajen daukar lafiyayyen ciki nan gaba, da kuma kasancewar jaririn cikin koshin lafiya.

A don haka makalar wadda aka wallafa a watan janairun shekarar 2019, ta jaddada muhimmancin bayar da kyakkywar kulawa ga dukkanin matan da ba su wuce shekarun daukar ciki ba.

Wadanda suka hada da macen da ta yi bari ko ta haihu lokaci bai yi ba, ko wadda 'dan ya zo ba rai ko kuma wadda ta haihu lafiya.

Hanyoyi biyu da miliyoyin mata ke bi don yi tazarar haihuwa su ne na gargajiya da kuma ta asibiti.

Sai dai har ila yau ga wasu matan ba cinya ba kafar baya, domin na asibitin ba ya karbarsu.