Dangantakar da ke tsakanin shaƙuwa da mutane da kuma sha'awar jima'i

Asalin hoton, Sounds fake but okay podcast
- Marubuci, Daga Jessica Klein
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Worklife
A farkon wannan shekarar, a lokacin da 'yar gwamnan birnin New York Governor Andrew Cuomo, Michaela Kennedy-Cuomo, ta fito ta nuna karara cewa 'rashin sha'awar mutumin da ba a shaƙu da shi ba' yana tasiri kan jima'i an yi ta caccakarta.
Mutane da dama sun rika zaginta suna yi mata habaicin cewa ba ta sha'awar jima'i. Daidaiku ne kadai suka amince akwai irin wannna abun a zahiri.
Duk da cewa ba a waye da batun rashin sha'awar jima'i da wanda ba ka shaku da shi ba, mutanen da ke fama da wannan matsala suna da yawa a duniya.
Rashin sha'awar wanda ba ka da shakuwa da shi dai, na taka rawa wajen sanya mai matsalar jira na tsawon lokaci har sai ya ji irin wannan yanayin ya ragu kafin amincewa da yin jima'i tsakaninsu.
Amma ga wasu lamarin ba haka yake ba, ya fi kama da ra'ayi - idan ba na ra'ayinka babu abin da zai sanya na hada jiki da sunan jima'i da kai, sannan wadanda ba sa jin hakan, kai-tsaye suke fara yin jima'in cike da fatan wannan shakuwar za ta zo nan gaba.
Kayla Kaszyca ta ce a lokacin da Kennedy-Cuomo ta sanar da halin da take ciki, sai aka dauka karya ce kawai, amma shirin na podcast din ya kewaya sosai inda daya mai gabatarwa Sara Costello ta tattauna a kan soyayya, da alaka, da jima'i kan bigiren sha'awar rashin shakuwa.
A wasu lokutan Kaszyca ta ce bayanin Kennedy-Cuomo ya dago batun sha'awar da bude fagen sake tattaunawa akai.

Asalin hoton, Elle Rose
A wani bangaren kuma, yawan tattaunawa kan batun a sarari ya ba da wata kafa ta yada labaran karya.
"Ina ganin kalmar 'Sha'awar shakuwa' tana nufin lamari mai girma, amma ba lallai ne mutane su fahimci ainihin yadda ya kamata a fassara ta ba," in ji Kaszyca, mai shekara 24.
Misali, yawancin mutane suna watsi da batun rashin sha'awar shakuwa da abin da hakan ke nufi da kuma haifarwa, wasu na ganin ba wani bakon abu ba ne a wayi gari wani ba ya sha'awar yin jima'i da wanda bai kwanta masa a zuciya ba, ko wanda babu wata alaka tsakaninsu.
"Wani zai iya cewa, ai kowa ma haka yake ko?'"
Amma Kaszyca ta ce "dole ka fara nuna hakan ba mai yiwuwa ba ne".
Mutanen da suka gane sha'awar shakuwa, kamar Kaszyca da sauransu, wadanda suke musayar bayanai kan halin da suka samu kansu a ciki, na aiki tukuru domin gano ainihin kalmar da ta dace su fassara "sha'awar shakuwa".
Lamari ne mai sarkakiya idan ana tattaunawa akai, abin da tuntuni ba shi da takamaimai suna, sannan ma'anar na dagulawa masana lissafi.
Aikin nasu na daukar sabon salo, kuma cikin shekarun da suka gabata, an samu ci gaba matuka musamman a shafukan sada zumunta irin su Facebook da Instagram, kuma kungiyoyi na shiga lamarin ana fadada bayanai, ta haka aka samu mutane daga sassa daban-daban na duniya suna tattaunawa akai.
'An dauki dogon lokaci ban fahimci abin ba'
Mutane sun yi kokarin bibiyar ta inda suka kai batun wani taro da aka yi kan wayar da kai game da jima'i a shekarar 2006.
"Ina ganin kalma ce da ta samo asali daga jima'i kamar yadda wasu ke da wannan ra'ayi," in ji Anthony Bogaert, mai bincike kan jima'i kuma farfesa a Jami'ar Brock da ke Ontario, a Canada, wanda ya rubuta maƙala kan jima'i tsakanin bil'adam.
A wannan lokacin an yi ta wallafa makaloli kan jima'i, bayan gano yadda ake kamfar bayanai kan batun, a lokacin sabbin bayanai suka yi ta bulla, kowa na fassara kalmar da yanayin fahimtarsa.
"Akwai wata al'ada ta barin mutane yin bayani kan yadda suka fahimci abu, ta haka ka samu abubuwa da dama kuma masu muhimci," in ji Bogaert.
Wadannan mutanen sun taimaka wajen share fagen tattaunawa kan sha'awar shakuwa, da shi kanshi jima'in. A wannan yanayin, ana samun bayanan da a baya ba a da su musamman a intanet.
Elle Rose, mai shekara 28, da ke zaune a kasar Indiya da Amurka, ta fara gano ma'anar sha'awar shakuwa bayan tattaunawa da abokanta shekarun da suka gabata.
"Ya zuba mata ido, tare da cewa, 'Elle, kina magana ne fa a kan sha'awar rashin shakuwa'," in ji Rose.
"Har lokacin ban aminta da hakan ba, an dauki lokaci kafin na tabbatar da hakan." Tsoron makomar soyayyar da suke yi matukar suka samu bambancin ra'ayi kan sha'awar shakuwa, Rose na bayyana kansu da wadanda ke soyayya', tare da jingine sha'awar shakuwa a gefe.

Asalin hoton, Sounds fake but okay
'Daga karshe mutane na ganin an san da zamansu'
Rose ya taka rawa wajen watsi da batun sha'awar shakuwa a Amurka domin tsarkake al'ada, inda aka bai wa mata damar tattaunawa kan batutuwan jima'i a kafafen sadarwa, amma kuma ana fatan za su killace kan su har sai sun yi aure musamman ta fuskar addinai.
Wannan wata kafa ce da aka bude da ta wayar da kai da kuma kawar da batun jima'i barkatai, har sai an samu cikakkiyar shakuwa ko soyayya mai karfi tsakanin mace da namiji.
Rashin fahimta na haddasa kadaici. Cairo Kennedy, mai shekara 33 a Saskatchewan, Canada, ta ce ta girma "ba tare da ta san wani abu game da jima'i ba, kuma hakan na sanya mutum ya ji kamar an baro shi a baya", in ji ta.
"Yana zama babban sirri kuma wata hanyar abin kunya."
A lokacin da ta gano akwai wata ma'ana da ake yi wa abin da take ji, sai ta samu "sa'ida", amma kuma sai babu wani karin bayani kan hakan", in ji ta - akalla ba a batun sha'awar shakuwa musamman kan yadda wasu suka fahimta, da kuma suka taba shiga ko ma suna cikin lamarin.
Bayanan da ake wallafawa a shafukan intanet sun wadata ta yadda take samun karantawa, tare da tunanin, "'kai, wannan ai kamar ni ce', amma ba dai ba sosai ba, 'toh, ashe akwai mutane da dama kamar ni'."
Kennedy ta yanke shawarar cike gibin, ta hanyar samar da dandalin da ake tattaunawa kan 'rayuwa da sha'awar shakuwa'. Duk da cewa masu irin matsalar da dama sun tuntube ta, tun daga matasa a shekarun balaga, har zuwa 'yan shekaru 50, yawancinsu mazauna kasashen Turai da Amurka. "Na yi matukar mamaki, kan yadda mutane suka yi ta kwararowa," in ji ta.
"Ina ganin lamarin ya fi kamari a shafukan sada zumunta," in ji Hawaii-kwararriya kan abin da ya shafi jima'i tsaknin bil'adam.
Ta fara jin kalmar sha'awar shakuwa a karon farko lokacin da take karatun Digirin Digirgir a Jami'ar Minnesota, da ke Amurka a shekarar 2014, "duk da cewa ana bayani ne [kan jima'i] kuma an dauki lokaci kan hakan".
Duk da cewa Brito ta yi amanna da cewa yawancin mutanen da take hulda da su da suke bayani babu shamaki, 'yan tsakanin shekaru 20 ne.
"Sun waye kwarai da shafukan sada zumunta," in ji ta, "wurin da aka fi samun sakewa da amincin tattaunawa."
"Shafukan sada zumunta na bude kafar da muryoyi da dama za su shiga a dama da su, da bayanai fiye da lokutan baya," ta kara da bayani. "a karshe [mutane] na samun gamsuwar an san da zamansu."
Klaus Roberts, mai shekara 30, mazaunin wajen Helsinki, ya yaba wa intanet wajen taimakawa yada gidauniyarsa da ya kafa shekaru biyar da suka gabata.
"Kasar Finland na sawun baya kan abubuwa da dama, saboda kasarmu kankanuwa ce," in ji shi.
An bayyana shi da mutamin da bai damu da abin da ya shafi sha'awa ko jima'i ba, amma yana mu'amala da kungiyar LGBTQ+ ta intanet, sun taimaka masa da bayani kan sha'awar shakuwa, ta nan ya gano rukunin da ya fito.
"Mutanen da suka san komai game da hakan, sun fi saurin fahimta ta idan na yi magana."

Asalin hoton, Cairo Kennedy
'Karin fahimta kan abin da ake nufi da jima'i da sha'awa'
Yayin da aka gagara samar da bayanai ingantattu game da kashe-kashen ko inda wani ya karkata kan jima'i da jinsi, wadannan matan da ke yada labaransu ta kafafen intanet sun taimaka wajen ilmantar da mutane da wayar da kai.
Kaszyca da abokiyar gabatar da shirin Sarah Costello, sun fara shirin podcast tun kafin su kammala Jami'ar Michigan da ke Amurka, inda abokansu ne kadai ke saurare da ba su kwarin gwiwa.
A yau, sun fadada zuwa wasu kasashen da suke amfani da turancin Ingilishi. Kaszyca ta yi kiyasin sama da mutane 7,000 da ke sauraren shirinsu na Sounds Fake But Okay a duk mako.
Ta kara da cewa ba wai ana magana a kan wadanda ke bayani kan sha'awar shakuwa ne kawai ba, iyayensu, da abokan zama na saurare domin su fahimci wani abu da daukar darasi.
"Kashin shirin mu da aka fi sauraro shi ne 'Rashin sha'awar jima'i kashi na 101'," in ji Kaszyca.
"Mutane na cewa sun turawa aminansu ko 'yan uwa bayan sun saurara, domin su ma su ilmantu da abin da ke faru, su kuma saukaka ilimantarwa."
Wani ilimantarwar da ake yi, na kara yawaita cikin al'umma, misali kan batun samartaka. Misali, Kaszyca ta ce manhajojin da aka samar ta intanet sun saukaka batunsha'awar shakuwa, akwai furbin da za ka sanya rukumnin da ka fito idan ka na rubuta bayanan ka.
Wannan na taimakawa wajen rashin fara na shigar sauri a soyayya ta hanyar tattauna batun jima'i, saboda mutum ya san rukunin da ka fito, ta nan za a gane ko abota ce kawai ko ana son fadada ta zuwa soyayya da sauransu, saboda har yanzu ba kowa ya san wani batun sha'awar shakuwa ba," in ji ta.
An karkare da cewa, "tattaunawa kan batun jima'i, ko rashin son yin sa cikin al'umma na taimakawa wajen gano bakin zaren," in ji mai bincike Bogaert, kuma hakan na sanyawa a kaucewa masu sa ido kan jima'in.
Sai dai fa batu ne mai cike da sarkakiya da wuyar sha'ani.










