Su waye 'ya'yan Putin mata? Abubuwan da muka sani game da iyalansa

Putin and family in an archive family photo

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto, Putin da iyalansa cikin wannan hoton a shekarar 2002, wanda ke boye fuskokinsu

A ko da yaushe ana bai wa shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin kariya idan aka zo batun tambaya game da iyalansa.

A shekarar 2015, lokacin daya daga cikin tarukansa na manema labarai, ya riƙa kauce wa tambayoyi game da ƴaƴansa mata.

"Ya'yana mata na zaune a Rasha kuma sun yi karatu a Rasha kawai, ina alfahari da su," ya ce. "Suna magana da harsuna uku na kasashen waje sosai. Ban taba tattaunawa da kowa kan batun iyalina ba."

Ya kara da cewa "Kowa yana da 'yanci game da makomarsa, suna tafiyar da harkokin rayuwarsu kuma suna yi cikin mutunci."

Ba lallai ne ya so bayyana sunayensu ba, amma wasu sun bayyana. Sabbin jerin takunkuman Amurka sun fada kan Maria Vorontsova mai shekaru 36, da Katerina Tikhonova mai shekaray 35.

"Mun yi amanna, kadadorin Putin da dama na boye a hannun iyalansa, kuma shi yasa muka saka su a gaba," a cewar wani jami'in gwamnatin Amurka.

A yayin da kadan ne aka tabbatar game da rayuwar iyalan Putin, takardu, da rahotannin kafafen yada labarai da yawan ayyana maganganun ga jama'a sun wadatar wajen samar da ko su wane ne mutanen biyu.

Su biyun 'ya'yan Shugaban Putin ne da kuma tsohuwar matarsa Lyudmila.

Sun yi aure a shekarar 1983 lokacin tana aiki a matsayin mai lura da fasinjojin jiragen sama shi kuma jami'an leken asiri a hukumar KGB. Aurensu ya shafe shekaru 30.

A shekarar 2013 ne suka rabu, Mista Putin ya ce "matakin hadin gwiwa ne: ba mu cika ganin juna ba, kowannenmu na da rayuwarsa da yake tafiyarwa". Ta ce ya kasance "a koda yaushe cikin aiki."

Sun haifi babbar 'yarsu Maria Vorontsova, a shekarar 1985. Ta yi karantu a kan nazarin Kimiyyar Halittu a Jami'ar St Petersburg da kuma karatun Likita a Jami'ar Moscow.

Maria Vorontsova, Vladimir Putin and his wife Lyudmila

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Maria (daga can gefen hagu) ta kada kuri'arta a zabukan kasar Russia na shekarar 2007 tare da iyayenta

Yanzu Mrs Vorontsova malamar jami'a ce, da ta ƙware a fannin Tsarin Kwayoyin Halittar Dan Adam.

Ta jagoranci rubuta littafi kan tawayar halittun kananan yara, kana an saka ta a jerin sunayen masu bincike a Cibiyar Nazarin Kwayoyin Halitta a birnin Moscow. Kana ita 'yar kasuwa ce.

BBC ta gano ta a matsayin daya daga cikin wadanda suka mallaki kamfainin da ke shirin gina wata katafariyar cibiyar kiwon lafiya.

Mrs Vorontsova ta auri wani dan kasuwa dan asalin kasar Holland Jorrit Joost Faassen, wanda ya taba aiki a cibiyar makamashi ta Gazprom a kasar Russia, duk da cewa an bayar da rahoton rabuwarsu.

Mutanen da suka yi magana da ita tun bayan kutsawar Russia cikin Ukraine sun ce tana goyon bayan mahaifinta, kana ta nuna shakku game da rahotannon kafafen yada labaran kasashen waje game da tashin hankalin.

Idan aka kwatanta ta da kanwarta Katerina Tikhonova, tafi kasancewa a idanun jama'a, saboda kwazo da basirarta na zama mai rawar salon kidan rock n' roll.

Ita da abokin sana'arta sun zo na biyar a gasar rawan ta kasa da kasa a shekarar 2013.

Mr Putin's daughter Katerina Tikhonova dancing rock 'n' roll

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Miss Tikhonova ta samu matsayinta ba tare da an kira ta da sunan 'yar Shugaba Putin ba

A cikin wannan shekarar ne, ta auri Kirill Shamalov, dan dadadden abokin Shugaba Putin.

An kuma yi bikin aurensu a wani kasaitaccen wurin shakatawa a kusa da birnin St Petersburg.

Ma'aikatan wurin sun ce ma'auratan sin isa wurin a cikin wani keken doki da fararen dawakai uku suka ja.

Amurka ta aza wa Mista Shamalov takunkumi a shekarar 2018 kan rawa da ya taka a bangaren makamashin kasar Rasha.

Baitulmalin Amurka ta bayyana cewa "ya kara azurta cikin lokaci kankane bayan auren".

Tuni dai ma'auratan suka rabu.

Bayan mamayar kasar Russia a Ukraine, an cafke masu fafutika biyu kan mallakar manyan gidajen alfarma a garin Biarritz da aka bayyana na Mista Shamalov ne.

Yanzu haka Miss Tikhonova malamar jami'a ce kuma 'yar kasuwa.

A shekarar 2018 ne ta bayyana a kafar yada labaran kasar don yin magana a game da nazarin fasahar ƙwaƙwalwa kan kuma a wani taron kasuwanci a shekarar 2021.

Ba a taba bayyana dangantakarta da shugaban kasa ba a duka tarukan biyu.

Babu daya daga cikin 'yayan mata biyu da suka taba shafe lokaci mai tsawo tare da Shugaba Putin.

Mista Putin yana kuma da jikoki. Ya yi magana a kan su cikin wata tattaunawa ta wayar tarho a shekarar 2017, amma bai bayyana ko nawa yake da sub a ko kuma wacece a cikin 'ya'yansa mata ta haife su.

"Game da jikokina, daya tuni ta fara karatu a makarantar renon kananan yara.

"Don Allah ku fahimta, bana so su Irma kamar wasu gimbiyoyi 'yayan sarakuna. Ina so su girma kamar sauran mutane," a cewarsa.