Yakin Ukraine: Amurka ta sanya wa 'ya'yan Putin mata takunkumai

Asalin hoton, Alamy
Amurka ta ƙaƙaba wa na hannun daman Shugaba Vladimir Putin na Rasha takunkumai, ciki har da ƴaƴansa mata.
A cikin jerin mutanen da abin ya shafa har da iyalan Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov da wasu manyan bankunan ƙasar.
Matakan sun biyo bayan sabbin bayanan da suka yaɗu ne na cin zalin da dakarun Rasha suka yi a Ukraine, da suka haɗa da hotunan gawarwakin fararen hula da aka gani barbaje a kan titunan garin Bucha, da ke kusa da babban birnin ƙasar Kyiv.
Rasha ba tare da gabatar da wata shaida ba ta ce, jami'an Kyiv ne suka tsara hotunan.
Duk da cewa hotunan da tauraron ɗan adam ya ɗauka, sun nuna yadda aka kashe fararen hula a lokacin da Rashawa ke iko da Bucha.
A ranar Laraba Shugaba Muotin ya bayyana lamarin a matsayin "wani mugun abu na takala da gwamnatin Kyiv ke yi."
Takunkuman da Amurka ta sanya sun haɗa da:
- takunkuman tattalin arziki da za su haramtawa Rasha sabbin zuba jari
- matsanantan takunkuman tattalin arziki a kan banki mafi girma na Rasha, Alfa Bank, da kuma babban bankin ƙasar Sberbank
- takunkumai na matsi a kan kamfanoni masu zaman kansu
- takunkumai a kan jami'an gwamnatin Rasha da iyalansu
Ana sa ran ita ma Tarayyar Turai za ta hana shigar da makamashin kwal daga Rasha kan zarginta da rura wutar aikata miyagun laifuka.


Kafin a sanya sabbin takunkuman a Washington, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce, ba zai iya amincewa da duk wani rashin ɗaukar mataki ba.

Asalin hoton, AFP
Da yake magana a gaban majalisar dokokin Ireland a ranar Laraba, ya ce har yanzu akwai buƙatar a fahimtar da wasu al'ummar Turai da suke ganin cewa "yaƙi da laifukan yaƙi ba su kai asarar dukiya firgitarwa ba" da su goyi bayan sanya matsanantan takunkumai.

Asalin hoton, PA Media
Ya ƙara da cewa "Man fetur ɗin Rasha ba zai iya isar buƙatar tankokin yaƙin Rashar ba, inda shi kuma ministan harkokin wajen Rasha ya ce akwai buƙatar sanya takunkumin iskar gas da man fetur don su yi matuƙar tasiri a kan tattalin arzikin Rasha wajen yin yaƙin.
A wani lamarin daban a ranar Larabar, shi ma babban jami'in diflomasiyya na EU Josep Borrell, ya yarda cewa kuɗaɗen da aka taimaka wa Ukraine a yaƙin nan tun farkon kutsen, bai kama ƙafar dala biliyan 1.09 da Turai ta dinga kashewa a kowace rana a kan harkar makamashin Rasha ba.
Wasu ƙasashen Turai da suka haɗa da Jamus, sun dogara kacokan a kan makamashin Rasha kuma suna jan ƙafa wajen sanya takunkumi a kan wannan fannin.

Asalin hoton, Reuters










