Yakin Ukraine: Me ya ragewa ɗaliban Najeriya da rikici ya koro daga Ukraine?

    • Marubuci, Daga Soraya Ali
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Desmond Chinaza Muokwudo, ɗalibi ɗan Najeriya mai shekara 30 da ya tsere wa rikicin Ukraine, ya shafe shekaru 11 yana tara kuɗin tafiya karatu a Turai.

Matashin, wanda a baya yake aikin walda ɗan asalin jihar Anambra, burinsu shi ne karatu a fannin da ya shafi huldar kasa da kasa - sai dai ya yi fama da rashin aiki ana tsaka da fuskantar matsalolin tabarbarewar tattalin arziki a 2016.

A wannan lokaci iyayensa suka yanke hukuncin sayar da ɗan karamin filin da suka mallaka domin aika shi Turai ya cimma burinsa.

A shekarar da ta gabata ya shiga jami'a, sai dai kasa da watanni uku da isa Ukraine sai ga shi Rasha ta kaddamar da hari.

"Babu wani abin da ya ragewa iyayena, ba za su iya taimakamin ba," kamar yadda ya fada a wata hira da aka yi da shi ta wayar tarho daga inda ya samu matsuguni a Berlin na Jamus, yana cikin yanayi na karaya.

"Gwamnatin kasata ta ce na dawo gida, amma babu wani tanadi da aka yi da ke jirana a Najeriya."

Mista Muokwudo na ɗaya daga cikin 'yan Afirka 16,000 ɗalibai da ke rayuwa a Ukraine kuma a yanzu suke laluben hanyar ci gaba da karatunsu.

Wasu da dama daga cikinsu sun shiga ukubu wajen tserewa, yayin da rahotanni suka rika bayyana cin zarafi saboda wariyar launin fata da suka rinka cin karo da su a iyaka.

Daruruwa sun dawo gida a jiragen da suka kwaso mutane, duk da cewa babu bayanan da ke fayyace hakikanin yawansu, sai dai dubbai kamar su Muokwudo sun zabi su ci gaba da fafutuka a Turai.

"Na sadaukar da abubuwa da dama kafin na iya zuwa nan. Dole na zauna a Turai, kuma dole na nemi ilimi a nan," a cewar Mista Muokwudo.

Jami'o'i a sassan duniya sun mika tayin taimako ga ɗaliban da suka tsere wa rikicin Ukraine, sun yi alkawarin ba su damar ci gaba da karatu a farashi mai rahusa da sassauta dokokin samun biza.

Jami'an Afirka kuma sun himmatu wajen samun daidaituwar diflomasiyya kan dalibansu, inda ake samun tattaunawa tsakanin ministocin ketare da takwarorinsu na Turai domin cimma yarjejeniya.

An bai wa ɗaliban Ghana da ke karatun likitanci gurabe 250 a Jami'ar Likitanci da ke Hungary da kuma gurabe 200 a Jami'ar St George da ke Grenada.

Jami'ar Semmelweid ta Hungary, da ta bai wa ɗaliban da ke karatun likitanci damar ci gaba da karatunsu kyauta har zuwa lokacin kawo karshen yakin, ta ce a yanzu ta karbi takardun mutane 200 cikin makwanni kalilan, akasari 'yan Afrika.

Sai dai ɗalibai da dama na cewa wannan tayin karatun ba ya kai wa ga kowa. Akasari yakan dogara ne kan abin da dalibi ke karantawa, da kuma yawan shekarun da suka rage masa na kammala karatu da kuma abin da suke iya ci gaba da biya nan gaba.

Mista Muokwudo na korafin cewa akwai jami'o'in da ba sa daukar wadanda ba 'yan Ukraine ba.

"Muna daukar mutanen da suka kasance 'yan Ukraine ne kadai, abin da aka shaida min kenan," a cewarsa, yana magana kan tsarin Jami'ar Tallinn na Estonia.

Jami'ar ta tabbatar da cewa 'yan Ukraine kaɗai ke iya neman izinin ci gaba da karatu bisa tsarin da bai shafi bin hanyoyin neman gurbi ba sai dai sun ce suma daliban wasu kasashen na ketare na iya gwada sa'arsu.

Azuzuwan Intanet

Yaƙin ya jefa ɗalibai da dama cikin yanayi mai sarkakiya - da jefa wasu cikin yanayi na rashin cancanta.

Najeriya ta yi wa sama da mutum duba ɗaya maraba, akasarinsu ɗalibai, daga Ukraine, a cewar bayanan gwamnati.

Cikinsu akwai wani ɗalibi mai shekara 22 da ke karatun likitanci Fehintola Moses Damiloli, wanda ke makale a birnin da ake yi wa luguden-wuta na Sumy tsawon makwanni.

"Ina cikin farin-cikin dawowa lafiya da tarar da iyayena," a cewarsa, a tattaunawarsa da BBC daga gidansu da ke jihar Oyo.

Wannan shi ne ziyarata ta farko zuwa gida bayan sama da shekara biyar - kuma zango ɗaya ya rage mun na zama cikakken likita.

Akwai kuma yiwuwar burinsa ya cika saboda ya taki sa'a ganin cewa ya dogara da azuzuwan da ake dauka ta intanet, wanda duk da yaƙin da ake tafkawa akwai wasu jami'o'in Ukraine da suka ci gaba da bada darasi ta intanet kamar yada aka gani a lokacin kullen korona.

A jihar Kaduna da ke Najeriya, akwai Firdausi Mohammed Usman da ita ma ta ci gaba da karatunta ta intanet. Ɗalibar 'yar shekara 22 da ke karatun likitanci tana cikin shekara ta biyar a Jami'ar likitanci ta Kharkiv, da ke gabashin Ukraine.

Ta ce malamansu na basu darrusa ta intanet wasu kuma na fitowa har a bidiyo suna musu darrusa.

Malamanta suna da fahimta sosai sai dai ba su son nuna daga ina suke bada wadannan darrusa saboda dalilai na tsaro. Wasu sun tsere daga ƙasar, wasu kuma na zaune har yanzu a Ukraine kuma akwai masu mafaka a ginin karkashin kasa da ke bada kariya daga harin bam kuma suna bada darrusa.

"Basa son mu bar makarantar ko mu sauya zuwa wata kasar - don jami'ar na da zabin iya rufe wa baki-ɗaya. Ba za mu iya samun sakamakon jarabawarmu ba don haka wannan shi ne zabi mafi a'ala a yanzu".

'Bana son na koma baya'

Mista Damilola, wanda shi ne shugaban ɗaliban Najeriya mazauna Sumy, ya jaddada muhimmancin karatu a intanet musamman ga daliban da ke karatun likitanci kuma suka kai matakin karshe kamarsa.

"Yana iya kasancewa yanayi mai wahala ta intanet, amma zango ɗaya ya rage mun kuma zance gaskiya ba zan iya ɗawainiyar sako karatuna ba," kamar yada ya shaidamana ta sakon murya a kafar WhatsApp.

Ya ce ai kokarin kammala karatunsa a Najeriya tamkar ya koma baya ne baki-ɗaya a karatu.

Marcel Chidera, ɗan Jihar Enugu daga Najeriya, ya ci gaba da karatunsa a Poland, bayan kin bi jirgin kwaso ɗaliban da Najeriya ta aike musu.

Ba shi kadai ba ne. Angola ta aike ita ma jirage ga 'yan ƙasarta domin su koma gida daga Warsaw. Jirgin ya shirya kwaso mutane 277, amma mutum 30 ne suka amince su dawo.

"Komawa gida babu karatun digiri ba zaɓi bane a yanzu," a cewar Mista Chidera daga idan yake samun matsugunin wucen gadi a birnin Poland.

Ɗalibin mai shekara 25 na ganin ya yi sa a matuƙa ganin ya kammala karatun harshen Ukraine don haka ya samu damar iya sake digirinsa.

Kwasa-kwasai da dama a Poland ana yinsu ne ta harshen Turancin Ingilishi kuma hakan na bai wa ɗalibai daga ƙetare dama, amma tsadar kudin makarantar ta bambanta da Ukraine.

Ya samu jami'ar Poland da zai iya karatu a farashi mai rahusa - kuma yana ganin yafi wasu da dama a daginsa na Najeriya inda malaman jami'o'i ke yajin aiki sai baba ta gani tun 14 ga watan Fabarairu.

"'Yan uwana na karatu a Najeriya yanzu. Ba sa zuwa makaranta kwata-kwata saboda yajin aiki malamai," a cewarsa.

Dama ga 'yan Afirka

Karatun gaba da sakandare na fuskantar babban kalubale a sassan Afirka inda galibi ake fama da karancin kudi da ma'aikata masu inganci da fuskantar koma baya a fanin bincike da ci gaba, a cewar kungiyoyi masu zaman kansu da Majalisar Dinkin Duniya.

Jami'o'in Afirka 60 kadai ne suka iya shiga jeren manyan jami'i'o 1,500 na duniya, kamar yada jadawalin jami'o'in duniya ya nuna.

Afirka ta Kudu, kasar da ake da jami'o'i mafi shahara a Afirka, ta matsa kaimi wajen taimakwa ɗalibanta da su dawo.

Dr Mamphela Ramphele, tsohuwar shugabar jami'ar Cape Town, wanda ke na ɗaya cikin jami'o'in Afirka, ta ce wannan na nufin a sake nazartar hanyoyin inganta bai wa matasa taimako.

Irin wannan tunani ya shiga zukatan ɗalibai irinsu Zoe Inutu na Zambia, da ke laluben zabin da ya rage musu a gida. Ta shiga shekara ta biyu na karantun digirinta a Zaporizhzhia, da ke kudu maso gabashin Ukraine, lokacin da yaƙin ya soma.

"Takardun bayanan karatuna sun makale a Ukraine, don haka dole watakil na soma wani sabon digirin," a cewarta.,

"Zan je duk inda za a bani gurbi, ko da a Afirka ne, matukar zan samu tsaro."