Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Ukraine: Wadanne takunkumai ake kakaba wa Russia?
Kasashen yammacin Turai na shirin kakaba wa Rasha takunkumai masu tsauri saboda harin da ta kai kan Ukraine.
An shirya matakan ne domin su ragargaza tattalin arzikin Rasha kuma su tilastawa Shugaba Vladimir Putin ya janye dakarun kasarsa daga Ukraine.
Mene ne takunkumi?
Takunkumi wani nau'in ladabtarwa ne da wata kasa ke sanya wa wata kasar, yawanci akan yi haka ne domin a hana ta daukan wasu matakai na nuna fin karfi ko na taka dokokin kasa da kasa.
Ana amfani da takunkumai ne domin a yi wa tattalin arzikin kasa illa, ko a hana wani jami'i ko dan siyasa damar amfana da kudaden da ya tara a wata kasa. Akan kuma hada da hana wasu 'yan kasar yin tafiye-tafiye baya ga daina sayar wa kasar da makamai.
Sune matakai mafi tsauri da kasa kan iya amfani da su idan dai ba yaki ta shiga ba.
Wadanne takunkumai kasashen yammacin Turai suka saka wa Rasha?
Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce zai kakaba wa Rasha wadannan jerin takunkuman:
- Birtaniya za ta hana dukkan bankunan Rasha damar taba kudaden ajiyarsu a kasar, kuma za a hana su yin duk wata hada-hada da bankunan kasar. Wannan ya shafi bankin VTB Bank na Rasha.
- Za a kafa dokokin da za su hana manyan kamfanonin Rasha, har ma da gwamantin kasar neman kudade kamar na zuba jari ko na bashi a kasuwannin hannayen jarin Birtaniya.
- Za a dode asusun ajiyar wasu mutum 100 tare da hukumomin Rasha
- Za a hana kamfanin jirgin saman Rasha Aeroflot daga sauka a Birtaniya
- Za a soke wasu kwangiloli na sayen kayayyakin da Rasha ke iya amfani da su domin kera makamai
- Za a tsayar da cinikayya kan kayayyakin fasahar zamani da na tace man fetur a Rasha
- Za a takaita yawan kudin da Rashawa za su iya ajiyewa a bankunan Birtaniya
Firaministan ya ce "attajirai 'yan Rasha mazauna Landan ba su da wurin buya."
Kasar Belarus ma za ta fuskanci irin wadannan matakan ladabtarwan saboda rawar da ta taka yayin da Rasha ta afka wa Ukraine, inji shi.
Shugaban Amurka Joe Biden daga baya ya sanar da zai dauki irin wadannan matakan, yana cewa tun da Rasha ta "zabi wannan yakin" saboda haka za ta dandana kudarta:
- Amurka za ta hana wasu manyan bankunan Rasha hudu damar amfani da kadarorinsu da ke kasar kuma ba za su iya yin cinikin dalar Amurka ba
- Za a kuma saka wa wasu Rashawa masu alaka da Fadar Kremlin takunkumai
- Amurka da kawayenta za su hana Rasha samun fiye da rabin kayayyaki na kimiyya da na fasahar zamani domin a hana kasar zamanantar da rundunar sojojinta
Tarayyar Turai ma ta ce ta amince da wasu jerin matakai da za su "yi gagarumin tasiri" kan Rasha.
Akwai wasu takunkuman da za a saka wa Rasha?
Kasashen yammacin Turai na rige-rigen kakaba wa Rasha takunkumai. Cikin matakan da za su iya dauka akwai:
Hana Rasha amfana da tsarin aikawa da kudade na kasa da kasa mai suna SWIFT
Wannan mataki ne Ukraine ta bukaci kasashen yammacin Turai su dauka nan take kan Rasha.
Swift na ba kasashe damar aikawa da kudade cikin hanzari kuma akwai kamfanoni da bankuna fiye da 11,000 a kasashe 200 da ke amfani da tsarin a duniya.
Hana Rasha amfani da wannan tsarin zai sa ta fuskanci jinkiri idan an biya ta kudaden man fetur da isakar gas da ta sayar wa kasashen waje.
Sai dai wani sanata a majalisar Rasha ya gargadi Turai cewa idan ta kuskura ta dauki wannan matakin, lallai Rasha za ta daina tura wa nahiyar iskar gas din da take sayarwa.
Kuma Rasha na iya amfani da wasu hanyoyin na daban domin ta karbi kudinta - a misali tana iya amfani da wanda China ta samar mai suna Cross-Border Interbank Payment System.
Daina sayen iskar gas da man fetur da Rasha ke fitarwa
Man fetur da iskar gas na samar wa Rasha kashi daya cikin biyar na kudaden shiga da take amfana da su.
Saboda haka kin sayen wadannan kayan zai iya yin illa ga Rasha.
Sai dai zai yi wa kasashen da ke dogara da iskar gas din mummunar illa saboda babu wata kasuwa nan kusa da za su koma gare ta.
Rasha ce ke samarwa kasashen Tarayyar Turai kashi 26 cikin 100 na gurbataccen mai da kashi 38 na iskar gas din da suke amfani da su. Saboda haka ko dakatarwa ta wani takaitaccen lokaci zai janyo hauhawar farashin albarkatun mai.
Hana Rasha hulda da kasashen duniya
Amurka na iya hana Rasha yin cinikayyar da ta shafi amfani da dalar Amurka ta hanyar saka matakai kamar haraji kan dukkan hada-hadar da ta shiga. Birtaniya ma ta yi barazanar hana kamfanonin Rasha amfani da takardar fam na Birtaniya.
Kasashen yammacin Turai na iya daina sayen kayayyaki daga Rasha, a misali na'urorin hada komfuta.
Wannan na iya shafar bangarorin tsaro da na tafiye-tafiye zuwa sararin samaniya da masana'antun kere-keren motoci.
Amurka da Tarayyar Turai da Birtaniya tuni suka dauki matakan ladabtarwa kan wasu bankunan Rasha.
Girman tasirin takunkuman kan kasashen Yammacin Turai
Amma akwai wani hanzar ba gudu ba. Dukkan matakan da kasashen yammacin Turai ke dauka na iya shafar nasu tattalin arzikin.
Hana bankunan Rasha shiga kasuwannin duniya na iya yin illa ga kamfanonin yammacin Turai da ke yin kasuwanci a kasar, ko wadanda suka zuba kadarori a bankunan.
Daina sayen kayayyakin fasahar zamani da na kimiyya daga Rasha zai yi wa kamfanoni a kasashen yammacin Turai mummunar illa.
Sannan, abu mafi muhimmanci shi ne, Turai ta dogara ne sosai kan iskar gas daga Rasha, wanda ya kai kashi 40 cikin 100 na dukkan gas din da kasashen nahiyar ke bukata.
Ma'aikatar harkokin waje ta Rasha ta yi barazanar daukan matakan ladabtarwa nata kan kasashen yammacin Turai. Cikin takukuman, akwai rage yawan iskar gas ko daina sayar wa kasashen na Turai gas din baki daya.