Rikicin Ukraine da tasirinsa a kan Afirka, batun fetur da ɗalibai da burodi

Shugaban Rasha Vladimir Putin (hagu) da shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu, lolkacin taron koli na farko tsakanin kasashen Rasha da Afirka ta Kudu, a urin shakatawa na Sirius Park of Science and Art

Asalin hoton, Getty Images

Yakin da ake yi a Ukraine ka iya yin mummunan tasiri a ƙasashen Afirka da barazana ga tattalin arziki, yayin da gwamnatoci za su fuskanci matsin lambar diflomasiyya domin nuna bangaren da suke marawa baya tsakanin Rasha da ƙasashen yammacin duniya.

Kamar yadda aka ambato wata makala da kamfanin dillancin labaran Afirka ta Kudu ya bayyana, hatta mutanen da ke kauyukan kasar Afirka ta Kudu da duniya baki daya sai sun ji a jikinsu idan ana yaki a kasashen Turai.

"Tun ma kafin a fara harba makami mai linzamin farko, wannan yakin ya fara mummunan tasiri: ta hanyar karkatar da miliyoyin daloli domin sayen makamai.

Ya kuma dauke hankali daga bakin talaucin da ake son magancewa, da annobar korona, da fannin ilimi, da daidaito, da matsalar sauyin yanayi da akai fama da su a wannan shekarar," kamar yadda Mark Heywood ya rubuta.

Mene ne martanin Afirka kan yakin?

Kasar Afirka ta Kudu, wadda ta fi kowacce tattalin arzikin masana'antu a nahiyar, ta yi kira ga Rasha ta gaggauta janye dakarunta daga Ukraine, tare da cewa za a iya magance matsalar cikin nutsuwa.

Wata sanarwa da gwamnati ta fitar, ta nuna damuwa kan halin da ake ciki; "Yaki da makamai babu abin da zai yi ga rayuwar dan adam face dagula lamura.

"Wannan abu ba Ukraine kadai ya shafa ba, zai shafi duniya baki daya. Babu wata kasa da ta ke da kariya daga wannan bala'i da ake ciki.''

Wannan matsaya ta Afirka Ta Kudu babban koma baya ne ga Rasha, wadda babbar aminiya ce ga ƙasarr.

Kasashen biyu na da kyakkyawar alakar kasuwanci, waɗanda dukkansu mabobi ne na kungiyar kasashen da tattalin arzikinsu ke haɓaka cikin sauri.

Afirka ta Kudu ta zuba hannun jari a Rasha na Ran kusan dala biliyan 80, wato dala bliyan biyar kenan, yayin da Rasha kuma ta zuba jarin kusan Ran biliyan 23.

Ita ma Kenya - mai karfin tattalin arziki a gabashin Afirka, wadda ba mamba ta dindindin ba ce a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ta bi sahun kasashe wajen Allah-wadai da harin na Rasha.

A wani jawabi da ya yi a zauren kwamitin tsaro na MDD, jakadan Kenya Martin Kimani, ya ce: "An tauye hakki da 'yancin Ukraine baki dayanta. Majalisar Dinkin Duniya ba za ta zuba ido ta ga hakan na ci gaba da tafiya ba."

Kasashen Ghana da Gabon - da ke zauren majalisar sun yi Allah-wadai da Rasha.

Kawo yanzu babu wata kasar Afirka da ta fito ta nuna goyon baya ga mamayar Rasha a Ukraine, ciki har da kassahen Mali da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, inda dakarun Rasha ke taimaka wa gwamnatocinsu yaƙi da masu tsattsauran ra'ayi.

Butum-butumin sojojin Rasha
Bayanan hoto, Butum-butumin dakarun Rasha da aka girke a babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Kudu Bangui, a shekarar da ta gabata

Sai dai a wani mataki da ya zo da ban mamaki daga gwamnatin sojin Sudan, babban kwamandan sojin kasar mai karfin fada a ji, Janaral Mohamed Hamdan "Hemeti" Dagolo, ya isa birnin Moscow, a daidai lokacin da Rashar ta fara yaƙi a Ukraine.

Balaguron nasa na yauƙaƙa dangantaka ne tsakanin ƙasarsa da Rasha, a daidai lokacin da kasashen yamma ke kallon Sudan a matsayin wadda ke yi wa dimukradiyya zagon kasa, bayan hamɓarar da mulkin Omar al-Bashir, da ya mulki kasar na gwamman shekaru.

A bangare guda, jakadan Rasha a jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, ya ce a shirye Moscow take ta taimaka wa kasar magance matsalar kungiyoyi masu dauke da makamai da ke cin kare babu babbaka a tsakiyar kasar.

Ta yaya yakin zai shafi 'yan Afirka?

Tuni farashin ɗanyen mai ya yi tashin gwauron zabi, kowacce ganga daya ta haura dala 100, abin da ba a taba gani ba cikin shekaru bakwai.

Ta yiwu kasafin kudin kasashen Najeriya da Angola su samu tagomashi, sakamakon tashin farashin man, sai dai mutanen kasashen za su fuskanci karuwar farashin sufuri. Wannan zai yi tasiri kan kusan duk kayan da ake saidawa na yau da kullum.

"Dukan zai zamo biyu, ga tashin farashin kayan abinci a duniya, ga kuma tashin farashin makamashi da zai janyo tsadar rayuwa.

Idan kuma manyan bankunan kasashen suka kara kudin ruwa, zai zamo duka uku a lokaci guda," in ji Charlie Robertson, mai sharhi kan sha'anin tattalin arzikin duniya.

Sai dai editan jaridar Africa Confidential Publication mai cibiya a Birtaniya, Patrick Smith, ya ce yaƙin zai budewa kasashe masu arzikin mai da iskar gas wasu damarmaki.

Ya kara da cewa; "Turai za ta yi saurin neman wanda zai maye mata gurbin Rasha a fannin iskar gas, kuma yawancin inda ake da tabbacin samu shi ne nahiyar Afirka.

Don haka wannan babbar dama ce ga kasashen Afirka, su sa kai domin gaggauta ƙulla huldar kasuwanci mai riba."

Wani Bamasare ya na tallan burodi a kusa da masallacin al-Azhar da ke Masar, 8 Disamba 2017

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana nuna damuwa kan tashin farashin burodi

Ya ce babban hadarin da Afirka ka iya fuskanta shi ne tashin farashin burodi, saboda kasashen Rasha da Ukraine ne ke samar da kusan kashi 30 cikin 100 na alkamar da duniya ke amfani da ita.

"Farashin burodi na daga cikin makaman yaƙin da ake amfani da su har a dambarwar siyasa, wanda yana daga cikin abin da ya kaɗa guguwar sauyi a kasashen Gabas ta Tsakiya.

Kasashen yankin Maghreb kamar Masar da Tunisiya da Moroko da Libya da Algeriya da suka dogara kacokam kan alkama, za su fi kowacce jin jiki idan aka samu raguwarta da ƙara mata farashi," in ji Mr Smith.

Kenya ma na cike da damuwa kan yadda yakin zai shafe ta, da takunkumin da aka sanya wa Rasha shi ma abin damuwa ne, wanda zai shafi kamfanonin samar da ganyen shayi.

Kuma Rasha na daya daga cikin manyan kasashe biyar da ke taimaka wa Kenya samun kudaden kasashen waje.

Wata mace 'yar Kenya ta na aiki a gonar ganyen shayi da ke mazabar Mathioya da ke Muranga, a Kenya ranar 20 ga watan Agustan 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kenya ce a sahun gaba wajen samar da ganyen shayi

Wanne hali 'yan Afirka ke ciki a Ukraine?

Sakamakon saukin kudin makaranta, da alaka mai kyau da Afirka tun zamanin Daular Sabiya, Ukraine ta zamo kasa mafi sauƙin karatu ga daliban Afirka, inda dubbai ke karatu a jami'o'i daban-daban da ke kasar musamman masu karatun fannin likita.

Sannan akwai 'yan Afirka da dama da ke zaune a Ukraine. Yayin da yaƙin ya ɓarke, ana cike da fargabar halin da za su tsinci kan su a ciki.

Ministan harkokin wajen Ghana ya bukaci sama da 'yan kasarsa 1,000 su gaggauta fakewa a gidajensu ko kuma wuraren da gwamnati ta bude domin bai wa farar hula kariya.

Sai dai kungiyar daliban Ghana ta yi kira ga gwamnati ta gaggauta shirya yadda za a mayar da su gida, tare da cewa yaƙin ka iya rikiɗewa ya jefa mutane cikin mawuyacin hali kwatankwacin irin wanda aka shiga lokacin da annobar korona ta ɓarke.

"Mun yi amanna za a yi amfani da hanyoyin da suka dace kamar yadda aka yi lokacin da aka kwashe dalibai daga China, daidai lokacin da korona ke kan ganiyarta, don haka a yi amfani da irin wannan salon domin mayar da mu gida," in ji wata sanarwa.

Kasashen Afirkar da suke da dalibai masu yawa a Ukraine sun hada da Moroko mai dalibai 8,000, sai Najeriya mai dalibai 4,000, da kasar Masar mai 3,500, su ne kusan kashi 20 na daliban kasashen waje da ke karatu a Ukraine a shekarar 2020.

Shi ma ministan harkokin wajen Najeriya ya ce labarin mamayar Rasha a Ukraine ya zo da ban mamaki, kuma suna daukar matakan da suka dace domin tabbatar da kare 'yan Najeriya da ke Ukraine.

Sannan suna shirin kwashe wadanda suke muradi zuwa gida, da zarar an bude filin tashin jiragen saman kasar.

Wata 'yar Najeriya da ke karantar fannin likita a Ukraine mai suna Fatima Halilu, ta shaida wa BBC cewa kusan makwanni biyu da suka gabata ta bar birnin Kyiv.

"Sai dai dukkan ƙawayena su na Kyiv. Ba su san yadda za su yi ba, suna cikin ɗimuwa da tashin hankali," in ji ɗalibar mai shekara 18.