Ta yaya Ukraine za ta iya kare kanta daga farmakin Rasha?

Tankar yakin Rasha na tafi kan titin Donetsk

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Daga Jonathan Beale
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakili kan shanin tsaro, BBC News

Yanzu da yake kasar Rasha ta fara kai farmaki, shin wane irin fama ne kasar Ukraine za ta sha wajen kare kanta?

Dakta Jack Watling, na cibiyar Royal United Services ya bayyana cewa: "Ina ga 'yan kasar Ukraine na cikin tsaka mai wuya.''

Bai jima da dawowa daga kasar ta Ukrain ba kuma ya ce yanzu shugabannin rundunar sojin kasar na fuskantar ''zabi mai wuyar gaske''.

Mahukuntan kasashen Yammaci sun kididdige cewa Rash ana da dakaru kusan 190,000 a kan iyakar kasar Ukraine - fiye da yawan daukacin dakarun sojin kasar Ukraine da aka saba na 125,600.

Dakarun kasar Russia sun riga sun ketara kan iyaka daga kusurwowu da dama.

Bakin hayaki na tashi daga filin jirgin saman soji a Chuhuyev kusa da Kharkiv ranar 24, Fabrairu 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rasha ta fara kai hari wani filin jirgin saman soji a Kharkiv

Ukraine za ta yi faman gaske wajen kare dubban mil da wurarenta - daga kasar Belarus a arewaci har ya zuwa yankin Crimea a kudanci. Idan kuna kallon Ukraine a matsayin mai tabukawa a ko wane lokaci, Rasha za ta iya kaddamar da hare-hare daga karfe 10 zuwa karfe bakwai.

Ben Barry, na Cibiyar Koyon Dabarun Mulki ta kasa da kasa (IISS) kuma tsohon jami'in rundunar sojin Birtaniya yace, mawuyacin hali ne mai matukar wahala ga mai neman kare kansa''.

Ya kara jaddada cewa, ana yi wa Ukraine barazana da dama, kuma dakarunsu da aka baza kadan ne'', Jack Watling na Cibiyar Royal United Services Institute (RUSI) ya bayyana.

Mamayar Rasha a sararin samaniya

Amma banbanci na ainin tsakanin dakarun Russia da Ukraine a sararin samaniya ne.

Ukraine na da jiragen yaki 105 a kan iyaka idan aka kwatanta da na Rasha 300, Mista Watling ya bayyana.

Dakarun Rasha, ya yi hasashe,'' ''za su yi saurin samun galaba ta sama''.

Kayan yakin kasar Rasha masu bayar da kariya ta sama, kamar su makamai masu linzami na S-400 su ma sun bai wa dakarun karin wata dama.

Idan aka kwatanta, Ukraine na da mafi dadaddu ka kuma karancin kariya ta sama.

Mista Watling ya bayar da misalin Isra'ila da ta iya kare kan ta daga ko wace kusurwa. Amma ya kara da cewa ta iya yin hakan saboda karfin sojin da ta ke da shi a sararin samaniya. Wannan wani abu ne da Ukraine ba ta da shi.

Moscow ta kirkiri na ta irin ''karfin soji ta sama'' da manyan makamai masu linzami da na harba rokoki masu cin dogon zango,'' in ji Ben Barry.

Zai bai wa dakarun Rasha kai har ikan cibiyoyin tsaron Ukraine, da wuraren ajiyar makamai, da cibiyoyin tsaron sama da na kasa daga nesa.

Da alamu an fara hakan da kai hare-hare da makamai mazu linzami da tsananin gudu a kan yankunan kusa da Kyiv babban birnin kasar.

Mista Watling ya ce Rasha na da manyan wuraren ajiyar makamai na zamani da kuma karfin da Ukraine ba za ta iya bayar da amsa ga - kamar makaman Iskander da makamai masu linzami.

Ukraine ba ta jima da samun tallafin makamai masu guba daga Amurka da Birtaniya, amma akasari wadannan masu gajeren zango ne da masu harbo makaman tankokin yaki.

A takaice, Rasha ta fi kasar Ukraine karfin makamai masu cin dogon zango.

Rasha
1px transparent line

Da irin karfin soji ta saman da Rasha ke da shi da kuma makamai masu cin dogon zango, hadarin da dakarun Ukraine ke fuskanta shi ne nan ba da dadewa ba za a murkushe su.

Za a iya hana dakaraun Ukraine iya yin goijiya tare da sake shiri na fuskantar nausawar Rasha daga sauran kusurwoyi, Mista Watling ya yi amanna.

Akasarin dakarun Ukraine da suka samu horo mai kyau da kuma kayan aiki na gabashin kasar - a kusa fa yankunan Luhansk da Donetsk - inda aka rika gwabza fada tun a shekarar 2014.

Jami'an hukumar leken asiri na kasashen Yammaci sun shaida wa BBC cewa akwai damuwa ta sosai cewa Rasha za ta iya yi musu kawanya.

Amma kuma dakarun kasar Ukraine sun samu horo sosai da kuma makamai fiye da yadda suke a baya lokacin da kasar Rasha ta kutsa yankin Crimea.

Mista Barry ya bayyana cewa sojojin sun samu gogewar yaki daga fadan da suka yi da mayakan 'ya aware masu samun goyon bayan Rasha a gabashin kasar.

Fada a cikin birane

Muddin fadan ya shiga cikin garuruwa da biranen Ukraine hakan zai bai wa dakarun Ukaine wata dama.

Duk wani mai kare kan sa da ya shirya zai iya sa fada a cikin birni ya zo wa da duk wani mai kai hari matukar wahala - kamar yadda yan una a yakin Stalingrad na lokacin Yakin Duniya na Biyu, da kuma na baya bayan nan a birnin Mosul na kasar Iraqi.

Wata gyatuma ta na gyara gidanta, bayan makamin atilarin da aka harbo daga yankin Donetsk da ke karkashin 'yan tawaye magoya bayan Rasha ya fado gidanta da ke Donbas a Ukraine, ranar 23, Fabrairu 2022

Asalin hoton, Anadolu Agency via Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata na gyara gidanta da harin atilari ya fasa wa gilasai a Donetsk

Ben Barry ya yi amanna cewa dakarun kasar Rasha me yiwuwa da farko sun yi kokarin wuce ta bayan garuruwan da biranen.

Amma kuma ya yi amanna ba lallai ba ne cewa dakarun Rasha za su iya kaucewa fadan cikin birni, ba kamar a Kyiv ba saboda muhimmancin da ta ke da shi a siyasance.

Jack Watling y ace muddin Ukraine za ta iya kare biranenta sosai, za su dade suna jan daka har na tsawon lokaci.

Rasha ba za ta iya dogara kadai da hare-hare ta sama ba wajen cin galaba a garuruwa da birane.

Yanzu kasar Ukraine na fadan kare kan ta ne.

Ta shafe shekaru tana fafatawa da dakarun da ke samun goyon bayan kasar Rasha a gabashi, amma yanzu barazanar ga daukacin kasar a bayyane ta ke.

Da yake bai dade da dawowa daga Ukraine ba, Mista Watling ya ce akwai jajicewa ta dole don samun tsira a matsayin kasa, amma akwai shaidar da ke nuna cewa sun fi karfinsu, kana akwai yiwuwar mummunan zub da jini''.