An kara zamanantar da na'urar gane makaryata

Asalin hoton, Tomer Neuberg
- Marubuci, Daga Natalie Lisbona
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter, Tel Aviv
Farfesa Yael Hanein ta makala min wasu wayoyi a kuncin hagu.
"Sai ta ce min, "motsa idanunki sannan ki kifta, kuma ki yi murmushi. Nan ba da jimawa ba za mu gane ko kin iya karya ko ba ki iya ba."
Farfesa Hanein da abokin aikinta Farfesa Dino Levy ne ke jagorantar wasu masu bincike a jami'ar Tel Aviv ta kasar Isra'ila da suka samar da wata sabuwar fasahar gane mai shirga karya.
Sun ce bincikensu ya sa sun gano makaryata iri biyu - wadanda ke motsa girarsu yayin da suke fadin karya ko sun ki ko sun so, da wadanda ba sa iya hana wani motsin da labbansu ke yi yayin da suka taba kuncinsu.
Manhajar da suka kirkira na iya bankado kashi 73 cikin 100 na karerayin da ake furtawa kuma suna da niyyar inganta ta. "Idan mutum ya yi kokarin boye karyar da ya yi, daya daga cikin abubuwan da yakan yi shi ne hana jikinsa motsawa kamar yadda aka saba," in ji ta.
Farfesa Levy ta kara da cewa: "Sai dai abu ne mai matukar wahala mutum ya iya boye karyar da ya sharara idan aka yi amfani da wannan fasahar."

Asalin hoton, Getty Images
Hanyoyin gane an sharara karya kusan sun dade kamar ita kan ta karyar. Wani tsohon misali da aka adana a tarihi shi ne wanda aka samo daga China a shekara ta 1000 kafin zuwan Annabi Isa, inda wanda ake bukatar mutumin da ake tuhuma ya cika bakinsa da busasshiyar shinkafa.
Bayan wani lokaci sai a duba kwayoyin shinkafar kuma idan sun kasance a bushe sai a ce mutumin ya aikata laifi da ake tuhumarsa da aikatawa. Hikimar a nan ita ce idan lallai mutumin ya shara karya, to zai tsorata ko zai zama cikin damuwa, matakin da zai sa bakinsa ya bushe.
A farkon karni na 20 aka fara kera na'urori masu gane makaryata. Mafi shahara cikinsu shi ne "analogue plygraph", wanda ke da allurai uku zuwa hudu da ke cike da tawada wadanda ke yin zane a kan wata takarda mai wucewa.
Ana makala wa mutumin da ake tuhuma da yin karya wasu wayoyi a yatsunsa, da hannayensa da kuma a jikinsa kuma na'urar na auna saurin numfashinsa da bugawar jininsa da yawa zufa da ke fitowa a jikinsa yayin da yake amsa tambayoyin da ake yi ma sa.
Sai dai an dade an tababa kan sahihancin wadannan na'urorin da kuma hasashen da wasu ke yi cewa ana iya rikita na'urar har ta kasa gane ko ana karya ko uma gaskiya ake fadi.
Saboda wannan ne masu bincike da kamfanoni masu kere-keren kayan fasahar zamani ke kokari kera wasu sababbin na'urori na zamani da suka fi na shekaru baya.

Asalin hoton, Getty Images
A Jami'ar Erasmus ta birin Rotterdam da ke kasar Netherlands, Dakta Sebastian Speer da masu taimaka masa na amfani da na'urar MRI (magnetic resonance imaging) domin gane idan wani na yin karya ko yana cutar da wani. Suna yin haka ne ta hanyar kallo sauyin launuka a hotunan da kwakwalwarsa ke yi yayin da suke amsa tambayoyi.
"A takaice muna kallon bagarori daban-daban na kwakwalwa da suka fi motsawa a hotunan da na'urar ta MRI ke dauka a duk lokacin da mutumin ya yanke shawarar yi karya ko kuma ya fadi gaskiya", in ji Dokta Speer.
Daya daga cikin sababbin na'urorin ita ce EyeDetect wadda kamfanin Converus ta jihar Utah ta Amurka ke kerawa. Ta kan nadi bayanai ne a duk lokacin da mutum ya kifta idanunsa domin gane ko yana sharota ne.

Asalin hoton, EyeDetect
Kamfanin Converus ya ce ana amfani da na'urar EyeDetect a fiye da wurare 600 cikin kasashe 50, cikinsu har da hukumomin shari'a 65 na Amurka kuma kusan 100 a duniya.
Jami'an 'yan sanda na iya amfani da EyeDetect domin tambayar wadanda ake tuhuma da aikata laifuka.

Asalin hoton, Christopher Burgess
Sai dai wani tsohon jami'in hukumar leke asiri ta Amurka CIA, Christopher Burgess ya gargadi mutane kan dogara kacokan kan wadannan hanyoyin binciken domin gane gaskiya ko rashinta ga wadanda ake tuhuma.
"Wannan hanya ce daya tilo - amma tabbacin sahihancinta shi ne yadda na'urar za ta gano mugun iri da wadanda ke cutar da al'uma," inji shi.

Asalin hoton, Natalie Lisbona
Bayan da aka kammala bincike kai na, sai na tambayi Farfesa Yael Hanein ko na yi nasarar tsallake binciken.
Sai farfesoshin biyu suka yi murmushi suka ce min, "Gaskiya ba ki iya boye karya ba samsam."











