Masana kimiyya sun gano farar da ba kasafai ake ganin irinta ba a rayuwa

Asalin hoton, Anglia Ruskin University
Masanin kimiyyar wanda ya gano farar yana ganinta ya san cewa wannan wani kwaro ne na daban.
Dr Alvin Helden na jami'ar Anglia Ruskin University da ke Cambridge, wanda ke jagorantar wasu dalibai a wani bincike da suke yi a gandun daji na Kibale da ke yammacin Uganda ya ga farar.
Daga nan sai ya rada wa farar mai launin ruwan kasa da zaiba-zaiba suna "Phlogis kibalensis."
Dr Helden ya ce farar ta fito ne daga wani rukuni na nau'in farar da har yanzu ba a san kusan komai game da halittarsu ba.

Asalin hoton, Anglia Ruskin University
Rabon da a ga wata fara ta irin wannan rukuni ko nau'i tun a 1969 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Dr Helden, (the university's Applied Ecology Research Group,) ya ce: "Fara irin wannan, da danginta, wadanda kamanninsu daban yake, ba kasafai ake samun irinsu ba.
Ya kara da cewa "Kusan ba mu san komai ba game da wannan fara, (Phlogis kibalensis), sabon nau'in da na gano, da irin tsirran da ke ci da ma rawar da take takawa a rayuwar halittun yankin da muka ganta.
Farar wadda ko tsawon rabin inci ba ta kai ba (0.24in) kamar dai sauran nau'in fara namijinta yana da wata irin al'aura wadda za a iya cewa ta yi kama da siffar ganye.

Asalin hoton, Anglia Ruskin University
Dr Helden ya jima yana jagorantar tawagar dalibai da ke zuwa bincike a gandun dajin Kibale tun 2015 kuma yana daga cikin irin ayyukansa ya tatta bayanai a kan kwarin da ke gandun, da samar da hotuna na malam-buda-mana-littafi da sauran kwari daban-daban na gandun.
Ya ce: "Muna son saka wa mutanen Uganda wadanda suke kyautatawa tare da taimaka wa tawagar jami'ar Anglia Ruskin a ayuyukan da muke yi na bincike.
Duk da cewa gandun daji, wuri ne mai ban mamaki da sha'awa, abin takaicin shi ne ana barnatar da wasu sassansa sosai, abin da masanin kimiyyar ya ce yana fargabar cewa wasu kwari ko halittun za su iya bacewa tun kafin a gano su.

Asalin hoton, Anglia Ruskin University
To amma kuma masanin ya kara da cewa: "Samun irin wannan nau'in farar, wani abu ne da ba kasafai ake gani ba a rayuwa, domin farar da za a iya cewa ta dan kusa kama da ita, an ganta ne a wata kasar ba Uganda ba a sama da shekara 50.
Cikin murna da farin ciki, ya ce :"Ina ganinta na san cewa lalle wannan wani abu ne na musamman."
An wallafa bayanin wannan fara ta musamman a mujallar Zootaxa sannan kuma an bayar da ita ga dakin adana dabbobi da kwari na jami'ar Cambridge (Cambridge University's Museum of Zoology.)

Find BBC News: East of England on Facebook, Instagram and Twitter. If you have a story suggestion email [email protected]










