Abu biyar da 'yan Najeriya suka yi kewa game da Twitter

Asalin hoton, Getty Images
Bayan kwashe kimanin watanni bakwai da dakatar da Twitter a Najeriya sakamakon haramcin da gwamnatin kasar ta sanya, a karshe dai an samu daidaito tsakanin bangarorin biyu.
Fahimtar junan da aka samu ta kai ga bude manhajar wadda a baya 'yan kasar suke matukar amfani da ita wajen gudanar da al'amuransu na yau da kullum.
Mafi yawan 'yan Najeriya sai da Twitter ya zamar musu wajen kwashe rabin lokutansu na rayuwa domin suna samun abin da suke so, ko dai ga bangaren nishadantarwa ko kasuwanci ko neman 'yanci ko kuma bayyana ra'ayoyinsu (na siyasa, addini ko kabilanci) kamar dai sauran mutane a fadin duniya.
Rashin samun wadannan abubuwan ya sa wasu suka ji rayuwar ba ta yi musu dadi.
BBC ta yi duba kan abubuwa biyar da 'yan kasar suka yi kewa bayan kulle ayyukan Twitter a kasar:
Gatse da raha
Gabanin rufe wannan manhaja, matasa har ma da wadanda shekarunsu suka ja a Najeriya suna zuwa dandalin saboda raha wadda ke da alaƙa da irin gatsen da ake yi a shafin idan mutum ya wallafa wani abu.
Wannan gatsen da ake magana bai bar kowa ba, domin kuwa ana yi wa shugabanni, sannan ana yi wa malamai da jami'an tsaro da dai sauransu.
Daidaikun mutane ba su tsira ba, saboda irin yadda ake mayar da martani kan duk wani abu da bai yi wa masu aiki da shafin dadi ba.
Har ma wani maudu'i ake amfani da shi a ko yaushe a shafin don alakanta kalaman gatse da shi wato #SavageReplies.
Raha kuwa dama wani ɓangare ne na shika-shikan kafafen sada zumunta, mutane da yawa sukan bude nasu shafuka ba don su yi komai ba sai don nishadantar da kansu da rahar da mutane ke yi.

Kasuwanci
A lokutan baya masu tallan hajojinsu a Twitter sai da suka gane mutanen da idan suka wallafa abu, mabiyansu suna yi musu tsokaci mai yawa cikin kankanin lokacin, sai su je su tallata abin da suke sayarwa a wajen.
Akwai fitattun mutane daga bangaren hukumomi da bangaren masu wasannin da na daidaikun mutane da komai suka yi sai an yi ta ce-ce-ku-ce a kai, hakan wata dama ce ga masu talla su bayyana abin da suke siyarwa, kuma da dama suna samun ciniki ta dalilin hakan.
Duk da cewa wasu ba su jin dadin yadda idan ana tsakiyar muhawara masu talla ke nasu aikin, amma dole a fadi cewa suna amfana da wannan mahaja.

Sukar hukumomi
Da yake shafukan sada zumunta suna ba da kafar mutum ya bude shafinsa da ɓoyayyun bayanai, ko kuma da bayanan wani mutum na daba, hakan na bai wa da dama wajen caccakar shugabannin da da sauran hukumomi.
Wani lokacin sukar da gwamnati ke fuskanta na zuwa ne daga 'yan adawa ko fitattun masu rajin kare hakkin dan adam ko kuma wadanda idanunsu suka kyekyashe ba su tsoron kowa.
Akan yada irin abubuwan da suke fada a sauran kafafen sada zumunta irin su facebook da Instagram da Whatsapp da dai sauransu bayan an dauki hoton daidai inda suka yi bayani.

'Yan siyasa ma sun yi rashin kafa
Da yawa daga cikin 'yan siyasar Najeriya suna amfani da wannan kafa domin yada manufoinsu na siyasa.
Bare kuma a ce an kada gangar siyasa to a komai suka yi sai sun wallafa a wannan shafi, ko taimako suka yi sai sun sanya, in tafiya suka yi ma haka.
Sukan yi amfani da shafukan musamman lokacin da suke yunkurin sauya sheka a siyasance ko kuma fitar da matsayarsu a lokutan da aka samu turka-turkar siyasa.
Ita kanta gwamnati tafi amfani da wannan kafa domin sanar da duk wasu matakanta.

Yaɗa labarai da samun sa
Daya daga cikin wuraren da kafafen yada labarai ke samun manyan labaransu a ciki.
Tun da aka ce tanan 'yan siyasa ke wallafe-wallafe kuma an hana su wannan dama bayan rufe aikin shafukan to kuwa hakan zai shafi aikin masu yada labarai, saboda labaran siyasa na taimaka wa kafafen yada labarai.
Bayan matsayin manhajar ta inda ake samun labarai, ta dayan fuskar kuma ana yada labarai a kanta.
Sai dai shafin ya samu rashin jituwa da gwamnatin Najeriya ne biyo bayan zanga-zangar EndSars da aka yi, da kuma goge sakon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya yi wanda ya ce ya saba ka'idojin shafin.












