Gwamnatin Najeriya ta janye haramcin da ta saka wa Twitter

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya janye haramcin da ya saka wa Twitter a ƙasar.
Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya tabbatar wa BBC da hakan.
Ranar 13 ga watan Janairun 2022 matakin na gwamnatin ƙasar ya soma aiki.
"Twitter ta amince ta hada kai da Najeriya don a yaki mutanen da ke amfani da kafafensu don jawo kiyayya, kyamar juna, fitina, addini, kabilanci da kuma kawo tashin hankali a kasar Najeriya baki daya." In ji Garba Shehu.
Ya kara da cewa " Twitter ta yadda za ta yi aiki da dukkan dokokin Najeriya, kuma za ta bude ofishi wanda zai yi rajista a nan Najeriya wanda yake ko da matsala ta faru tsakanin Twitter da 'yan Najeriya ga wakilinsu za a iya zama a tattauna."
Bugu da kari Malam Garba Shehu ya ce daga yanzu Twitter za ta rika biyan haraji kamar yadda suke biya a kasashen Turai.
Ya ce irin arzikin da kamfanin sada zumuntar ya samu a Najeriya ya dace a ce yana biyan kudaden haraji masu yawa, inda ya ce irin kudin da Twitter ke samu akwai inda "raba dai-dai suke yi da wasu gwamnatocin kasashen Turai."
Tun a watan Yunin 2021 ne gwamnatin Najeriya ta haramta amfani da Twitter a ƙasar bayan ta yi zargin cewa ana amfani da shafin wajen kokarin tarwatsa kasar ta hanyar yada labaran karya da ke iya haddasa ''tashe-tashen hankula''.
Hakan ya haifar da martani mai zafi daga 'yan Najeriya da dama da suke kallon matakin a matsayin taka hakkin bila dama, amma kuma gwamnati ba ta nuna wata damuwa ba, inda ta bar shafin na Twitter a kasar ya ci gaba da kasancewa a toshe.











