Yadda rashin Facebook da Whatsapp da Instagram ya 'gigita' 'yan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Shafukan sada zumunta da muhawara na Facebook da WhatsApp da Instagram sun dawo aiki bayan matsalar daukewa da aka samu wadda ta kai tsawon kusan sa'a shida in ji kamfanin Facebook.
Kamfanin ya dora alhakin matsalar a kan wata tangarda daga wurinsu.
An kasa samun dukkanin shafukan uku mallakin Facebook a kan wayoyin hannu da intanet.
Lamarin ya shafi manyan kasahen duniya da ma masu tasowa ciki har da Najeriya.
A Najeriyar mutane sun fara farga da abin da ke faruwa ne da misalin karfe biyar na yammacin ranar Litinin.
Na'urar bin diddigi wadda ta gano matsalar katsewar ta nuna cewa, wannan ita ce katsewa mafi girma da suka taɓa gani inda aka samu rahoton matsalar miliyan 10.6 a fadin duniya.
Matsalar ta faru ne da kusan karfe hudu na yamma agogon GMT, biyar na yamma agogon Najeriya amma kuma a kusan karfe goma na dare agogon na GMT aka fara samun shafukan.
A wata sanarwa da Facebook ya fitar ranar Talata ya ce matsalar sauyin da aka samu wadda ta haddasa katsewar ta shafi na'urorin aikin kamfanin, wanda hakan ya rikita kokarin magance matsalar.
Kamfanin ya ƙara da cewa babu wata sheda da ke nuna cewa katsewar ta jefa bayanan masu amfanin da shafukan cikin hadarin sacewa ko wani abu makamancin haka
Tun da farko mai kamfanin na Facebook Mark Zuckerberg, ya nemi gafarar wadanda matsalar ta shafa.
Babu karin bayanai
Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.Karshen labarin da aka sa a Facebook
Samun matsala mai girman wannan, ba abu ne da ke faruwa ba sosai. Wata katsewa da ta taba samun Facebook a 2019 da sauran manhajojinsa, yawanci aka kasa samun shafin a sassan duniya tsawon sama da sa'a 14.
Shafuka da dama na intanet da suka hada da Reddit da Twitter, sun rika shagube a kan matsalar ta Facebook da sauran shafukan mallakarsa abin da ya jawo martani daga shafukan da matsalar ta shafa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Yaya 'yan Najeriya da wasu suka ji da lamarin?
Wasu masu amfani da shafukan na Facebook da WhatsApp da kuma Instagram a wasu kasashe sun shiga rudani bayan da suka fara ganin matsalar. Wasu sun dauka wayarsu ce ta samu matsala yayin da wasu suka dauka kudin intanet dinsu ne (wato data) ya kare.
Lamarin ya sa wasu suka rika kashe wayoyinsu su sake kunnawa, ko za su samu amma idan abu ya ci tura sai suka rika tuntubar ƴan uwa da abokanai da sauran jama'a domin sanin ko suma sun gamu da matsalar.
Bayan da wasu kafofin yada labaran a duniya ne suka sanya labarin katsewar a shafin Tuwita, sannan wasu suka san inda matsalar ta samo asali, cewa ba daga wayoyinsu ba ne.
Wannan matsala ba shakka ba ta yi wa masu amafani da shafukan dadi ba, kasancewar su ne manyan kafafen da mutane da yawa a yanzu suka dogara a kansu wajen samun labarai da sada zumunta da muhawara.
Matsalar ta sa mutane da yawa sun rika tattauna ta a Tuwita, tun daga lokacin da ta faru har kusan zuwa yanzu duk da cewa har yanzu shafin na karkashin haramcin da gwamnatin Najeriya ta saka masa, inda ake kewayewa ta bayan fage a shiga.
Wasu kuma da yawa sun rika amfani da wasu shafukan na intanet abokan gogayyar Facebook da WhatsApp da Instagram din, irin su Telegram da Imo, ko da yake wadannan ba a saba da su ba sosai kamar wadancan.
Ga irin yadda wasu suka bayyana ra'ayinsu kan matsalar a shafinmu na BBC Hausa Facebook, duk da cewa waɗanda abin ya "gigita" sun fi yawa sosai a cikin masu tsokacin.
Raheelat Ahmad Usman;
Toh jama'a haka mutuwa take zuwa Mana wallahi Bata re da mun shirya ba, lalle Muna da aiki ja agabanmu, yakamata mugyara tun yanzu kafun yazo ta iske mu batare da mun shirya ko munyi ban kwana da juna ba, Yah Allah ka karbi ranmu kana mai yarda damu😥
Gskya abun abun tsoro ne, haka kawai suddenly fah🥺🥺
Safiyyat Abdulhamid Daga kumasi Ghana;
,,, abin dai kam ba acewa komai,,, har na fara sallah dare,,sabooda da na taba wayar sai inji shiru garama da aka katse shi,, saboda yana Hana mu ibada yanda ya kamata,,da ma ance idan karshen duniya yazo duk wani technology da tse shi za ayi,,,ga alama Nan kuwa,, kowa sai ya Fara shiri duniya ta Zo karshe,, Kuma shima Mark Zuckerberg ya Dan Dana asara,, dama ance hannun da ya kirga riba shi zai kirga faduwa👌
Ukashat Suraj: "gaskiya naji dadi sosai Allah yasa mu Kara samu iren wannan yanayi anan gaba."
Hussaina Ibrahim Namagi;
Na dauka wayana ya samu damuwa ne baifi 15mins ba na rufe data, na dauko wayata barin duba wani abu nayi nayi fbook whatpp shuru har zufa nayi na bude na rufe har nagaji na tmbayi twins 6ter nah Hassana Ibrahim Namagi yah naki yanayi ne tace shuru ne fah yaki yi daga nan nayi ajiyar zuciya nace wannan kenan wata Rana kasa zata rufe idanun mu bamuda Daman rike wayar bare kuma shiga fbook da whtpp😭 Allah yasa muyi kyakkyawan karshe🙏
Musa Nuhu Kankia;
"Sai da na sanya datar N2000 na dauka takare. Kuma na goge WhatsApp nawa ina reinstalling yakai sau 5 wallahi. Nayi restarting waya na yafi a kirga. Na Kira MTN Customer Care sai dai a dauka inji shuuuuuuuuu! An cinye mun kati a banza Yan wahala. Allah ya Isa.

Matsalar ta faru ne kwana daya bayan wata tattanawa da aka yi da wata tsohuwar ma'aikaciyar Facebook wadda ta yi satar fitar da wasu takardun bayanai a kan kamfanin.
Frances Haugen ta gaya wa kafar CBS a ranar Lahadi cewa kamfanin ya fi bayar da fifiko a kan fadada maimakon kariya''.
A ranar Talata za ta bayar da bahasi a gaban karamin kwamiti na Majalisar Dattawan Amurka a kan wani zama da ya shafi ''kare yara a intanet'' game da abin da ya shafi binciken kamfanin a kan tasirin Instagram a kan kwakwalwa ko hankalin matasan da suke amfani da shi.


Yawanci a kan magance matsalolin katsewa da yawa cikin sauri. Yawanci sukan shafi wsu kasashe ne ko yankuna kawai, inda masu amfani da shafukan ba sa iya samunsu a wata kasar.
To amma wannan katsewar ta shafi duniya ne kuma ta shafi dukkanin saurn shafukan da ke da alaka da kamfanin na Facebook.
Haka lokacin da matsalar ta dauka ma ba a shawo kanta abu ne da ba a saba gani ba. Akwai rahotannin da ke cewa hankali ya tashi, an samu rudani a babban ofishin kamfanin na Facebook, inda ma'aikata suka rika kai-komo domin magance matsalar.
Za kuma a iya cewa a sanarwar da Kamfanin na Facebook ya rubuta ya yi hakan a tsanake, domin bai kawar da yuwuwar wata makarkashiya ba.
Ba shakka makon ya fara wa kamfanin da abubuwa marassa dadi - bayan da mai kwarmata sirrin kamfanin ta bayyana kanta a ranar Lahadi.
Lalle a iya cewa targade ya zama karaya kan wannan matsala ta kamfanin na Facebook idan aka yi la'akari da yadda ta faro da kuma irin tasirin yadda ta shammaci duniya.












