Sauyin Yanayi: Ranakun da ake samun tsananin zafi sun ninka a duniya

- Marubuci, Daga Becky Dale da Nassos Stylianou
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Ƴan jaridar tattara alƙalumma
Yawan kwanakin da a ke shafewa ana tabka tsananin zafi a duniya ya ninka a shekara tun daga shekarar 1980, kamar yadda wani binciken BBC ya gano.
Yanzu tsananin zafin har ya haura maki 50 a ma'aunin salshiyos, kuma yana ƙara fadada zuwa wasu yankunan duniya da a baya babu zafi sosai.
Binciken ya nuna cewa hakan na shafar lafiyar al'umma da kuma yadda za su gudanar da rayuwa a wannan yanayi.
An kuma gano cewa a tsakanin shekarun 1980 da 2009, tsananin zafi ya haura maki 50 da kwanaki 14 a duk shekara.
Kazalika kwanakin sun karu zuwa kwanaki 26 a tsakanin 2010 zuwa 2019.
A dan tsakanin an samu makin tsananin zafi sama da 45 a duk bayan mako biyu.
"Tururin iskar danyen man fetur da ake hakowa zai iya mamaye kaso 100 na dalilin da ya sa ake samun tsananin zafin," a cewar Dr Friederike Otto na kwalejin sauyin yanayi da ke Jam'iar Oxford a Birtaniya.
Bugu da kari matsawar duniya ta dumama, hakan na nufin akwai yiwuwar samun sauyin yanayin zafi, wanda zai yi illa ga bil'adama har ma da gine-gine da hanyoyi da sha'anin lantarki.
Yankunan Gabas Ta Tsakiya da kuma Gulf ne suka fi fuskantar tsananin zafi da ke haura sama da maki 50.
Kuma bayan fuskantar zafi da ya kai maki 48.8 a Italiya da 49.6 a Canada a bana, masana kimiyya suka yi gargadin cewa za a samu maki sama da 50 a wasu wurare matsawar ba a dakatar da fitar da tururin iskar danyen man fetur ba.
"Akwai bukatar mu dauki mataki da gaggawa kafin lamarin ya fi karfinmu," a cewar Dr Sihan Li, wani mai bincike kan sauyin yanayi a Jami'ar Oxford ta Birtaniya.

''Matsawar za a ci gaba da samun tururin wuta ba tare daukar mataki ba, to tabbas halin da za a shiga a gaba zai yi wahalar magancewa''. In ji Dr Li.
Binciken BBC ya kuma gano cewa a baya bayan nan ana samun karuwar yanayin zafi a Gabashin Turai da Kudancin Afrika da kuma Brazil.
Haka ma lamarin na dada karuwa a yankin Arctic da kuma Gabas ta Tsakiya.
A yanzu masana sun fara kira ga Shugabannin kasashen duniya kan daukar matakin gaggawa a taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a birnin Glasgow na Scotland a watan Nuwamba.
Ana sa ran shugabannin za su yi magana da murya daya wurin lalubo sabbin hanyoyin dakile yaduwar tururin zafin daga ma'aikatu a fadin duniya.
Tasirin tsananin zafi
An kaddamar da bidiyo kan binciken na BBC da aka saka wa suna 'Rayuwa a cikin tsakanin zafi sama da maki 50', wanda ya nuna yadda tsanani zafin ke shafar rayuwa a fadin duniya.
Ko a kasa da kashi 50, zafi na illa babba ga lafiyar bil'adama.

Kusan mutun biliyan 1.2 ne za su iya fuskantar zafi mai muni daga nan zuwa shekarar 2100, idan har duniya ta rika dumama kamar yadda ake fuskanta a halin yanzu, kamar yadda binciken jami'ar Rutgers da ke Amurka ya nuna.
Binciken na nufin adadin wadanda tsananin zafi zai shafa zai ninka har sau hudu.

Sheikh Kazem Al Kaabi manomin alkama ne a wani kauye da ke tsakiyar Iraki. Gonarsa na da kasa da ke da kyawon noma da yake cin moriya shi da makwabtansa, amma a hankali ta rika bushewa.
"A da gonata gwanin ban sha'awa da danyen ganye ko ina, amma yanzu ta zama fako ta bushe", in ji Kazem.
Kusan duka mutanen da ke kauyen su Kazem sun yi hijira don neman aiki a wasu gundumomi.
"Ina kewar kanina da abokaina da makwabta da ba su tare da ni yanzu. Duk sun tafi sun bar ni saboda rashin damar noma a nan," a cewar Kazim.
Inda aka samu alkaluman bincike
BBC ta yi amfani da alkaluman hasashen yanayi da take fitarwa a kullum da ta ke samowa daga ma'aikatar hasashen yanayi ta Copernicus Climate Change Service.
Ana amfani da alkaluman CCCS akai-akai wurin yin hasashen yanayi a fadin duniya.
Yadda muka aiwatar da bincikenmu
BBC ta hada alkaluman ranaku mafi zafi tun daga shekarar 1980 zuwa 2020, inda ta gano cewa yanayin na haura maki 50 a mafi yawan lokuta.
Mun kirga ranaku da kuma wuraren da hakan ke faruwa a duk shekara, wanda ya sa muka gano inda matsalar ta fi kamari tsawon shekaru.
Gudunmuwa
Mun samu damar amfani da binciken Dr Sihah Li na sashen nazarin kasa da muhalli da ke Jami'ar Oxford a Burtaniya.
Akwai kuma Dr Zeke Hausfather na cibiyar Berkeley Earth and Carbon Brief.
Mun kuma samu bita daga European Center for Medium-Range Weather Forecasts (ECMWF) da dai sauransu.












