Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jack Dorsey: Abin da ya sa shugaban Twitter yake jan hankalin ‘yan Najeriya
- Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Shugaban kamfanin dandalin zumunta na Twitter, Jack Dorsey, ya saba da ce-ce-ku-ce, amma a Najeriya ya sami kansa cikin rikita-rikita tsakanin matasan ƙasar da ke amfani da shafin da kuma gwamnati.
An sha yin amfani da dandalin nasa wajen haɗa zanga-zangar EndSars a shekarar da ta gabata, wadda ta zama wata ƙungiya mai adawa da cin zalin da 'yan sanda ke aikatawa daga baya kuma ta koma rikici tsakanin matasa da 'yan siyasa.
Sai dai kuma yanzu haka gwamnati ta garƙame dandalin nasa bayan Twitter ya goge wani saƙon Shugaba Buhari.
Jack Dorsey na burge 'yan Najeriya da dama. Ayyukansa na samar da filin faɗar ra'ayi da kasuwanci ya dace da muradun matasa da ke jin cewa ana muzguna musu.
Duk da toshewar da aka yi wa dandalin nasa, Mista Dorsey ya ci gaba da wallafa abubuwa game da Najeriya kuma hakan ya ja hankalin wasu da yawa.
Yayin da ake gudanar da bikin Ranar Dimokuraɗiyya sannan wasu suka fito zanga-zangar neman a buɗe Twitter, Jack ya wallafa tutar Najeriya da alamar musabaha da kuma maudu'in "#bitcoin".
Washegari kuma, ya yaɗa wata maƙala da ke kiran gwamnatin Najeriya ta bi tsarin kuɗin intanet na Bitcoin sannan ya ce "'yan Najeriya za su jagoranci harkar #bitcoin".
Wasu masana sun ce wannan ya nuna cewa Jack ɗan kasuwa ne kawai wanda ke neman tallata hajarsa.
Baya ga mallakar Twitter da aka fi saninsa da yi, kazalika shi ne ya mallaki manhajar Square and Cash App, wani kamfanin biyan kuɗi da ke harka da kuɗaɗen intanet musamman Bitcoin.
Hana amfani da kuɗin intanet
Kasuwar kuɗin intaent ta Najeriya, ita ce mafi girma a Afirka.
Hauhawar farashin kayan abinci da kuma faɗuwar darajar naira sun sa mutane da yawa sun koma amfani da kuɗin intanet, waɗanda wasu ke gani a matsayin mafi tsaro.
"A ko da yaushe sai an samu wata hanya da za ta bai wa 'yan Najeriya damar samun sauƙi da yin tattali a kuɗaɗen da ba naira ba," a cewar Faith Babafemi, wata ƙwararriya kan kuɗin intanet.
Ta ce akwai yanayin da kamfanonin Mista Jack za su amfana idan har aka ci gaba da amfani da kuɗin intanet a Najeriya.
Wasu labarai masu alaƙa
Sai dai kuma gwamnati ta haramta amfani da kuɗaɗen ne saboda abin da ta hanga na barazanar da suke kawo wa tattalin arzikin Najeriya.
Kamar yadda wasu suka bijire wa amfani da Twitter a ƙasar, haka nan an samu ƙaruwar masu sayayya da kuɗin ta ɓarauniyar hanya.
"Idan ka duba matakin hana amfani da kuɗin intanet da na toshe Twitter, ya fito ne daga gwamnati wadda ke tsoron cewa: 'Waɗanne irin ra'ayoyi za mu bar 'yan Najeriya su bayyana a intanet?', a cewar Senator Ihenyen, shugaban ƙungiyar masu amfani da kuɗin intanet.
Masu kare Mista Dorsey na cewa yayin da yake kare kasuwancinsa, haka ma yake da sha'awar Najeriya - duk da cewa bai zaɓe ta a matsayin hedikwatar kamfaninsa ba na Afirka, inda ya zaɓi Ghana a madadin haka.
Wasu labaran da za ku so ku karanta
Kantin sayar da komai da komai
Mista Mista Dorsey ya je Jihar Legas a wani ɓangare na ziyararsa a Afirka a Nuwamban 2019, sannan wani ɗan Najeriya mai suna Uche Adegbite na cikin manyan shugabannin Twitter.
Tsohuwar Ministar Kuɗin Najeriya kuma Shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya, Ngozi Okonjo-Iweala, ita ma ta taɓa zama a cikin majalisar shugbannin kamfanin.
Mamallakin kamfanin Co-Creation Hub a Legas, Bosun Tijani, wanda ya haɗu da Mista Jack a 2019, ya ce shugaban na Twitter ya yi imanin cewa kamfanin na matuƙar tasiri a Najeriya.
"Ƙasa ce da ke da ke matakai na shugabanci iri-iri amma Twitter na ɗaya daga cikin dandalin da ya bai wa mutane dama ba tare da duba matsayinsu ba domin tattauna matsalolin da suke faruwa a Najeriya waɗanda babu inda za ka same su," a cewarsa.
Hasali ma, Twitter ya wuce dandali. Wani kanti ne da ake sayar da komai - kamar tallata ayyukan yi da cigiyar waɗanda suka ɓata da kuma yekuwar saka wa jami'an gwamnati ido.
Wannan yanayi ya taka rawa babba yayin zanga-zangar EndSars a 2020 a lokacin da masu macin suka zaɓi Twitter a matsayin wurin tattara kan abokansu.
Sai dai kuma, zanga-zangar lumana ta rikiɗe zuwa tashin hankali, inda wasu 'yan daba suka lalata gine-ginen gwamnati a faɗin ƙasar.
Saboda wannan ne gwamnatin Najeriya ta zargi Jack da wasu jami'an "na da hannu" wajen yunƙurin cire Shugaba Buhari daga mulki.
Alaƙa ta sake lalacewa a makonnin da suka gabata lokacin da gwamnati ta haramta Twitter, tana mai zarginsa da hannu wajen yin amfani da shi "domin raba kan 'yan Najeriya" ta hanyar yaɗa labaran ƙarya da ke da tasiri "wajen haddasa tashin hankali".
Mamallakin kamfanin na Twitter bai fiya shiga harkokin siyasa a ƙasashen Afirka ba, abin da ya sa masu sukarsa ke ganin cewa ba kasuwancinsa kaɗai yake karewa ba, yana da manufa ta siyasa a Najeriya.
Yanzu haka 'yan Najeriya na amfani da dandalinsa su nemi sauyi na siyasa da tattalin arziki, abin da ke damun gwamnatin da ba ta fahimci harkar fasahar sadarwa da kyau ba.
"[Shugabannin gwamnati] sun fara kallon fasaha a matsayin wata hanya da ake amfani da ita domin yaƙar su waɗanda ba a taɓa yi ba a baya," a cewar Bosun Tijani.