Farouk Lawan: Dan majalisar da ya haskaka a baya amma ya tafi kurkuku

A ranar Talata 23 ga watan Yunin 2021 ne wata Babbar Kotu a Najeriya ta zartar da hukuncin ɗaurin shekaru bakwai kan Farouk Lawan, tsohon shugaban kwamitin tallafin mai a majalisar wakilan kasar.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta same shi ne da laifin karbar cin hancin a wurin Mista Femi Otedola, wani hamshakin dan kasuwa, domin wanke kamfaninsa daga badaƙalar tallafin mai.
Tuni dai rahotanni suka tabbatar da cewa an kai Farouk Lawan gidan yarin Kuje da ke birnin tarayya Abuja.
An zargi Lawan ne da karɓar dala dubu 620 daga hannun Mista Otedola, a lokacin da shi Farouk Lawan din yake shugabantar kwamitin binciken badaƙalar kuɗaɗen tallafin mai a shekarar 2012.
Sannan kotun ta buƙaci ya dawo da dala 500,000 ga asusun gwamnatin Tarayyya.
Shekara tara kenan da wannan rikici da ya dabaibaye majalisar wakilan, sai dai ga matasa da dama ba lallai su san ainihin abin da ya faru ba, da kuma shin ma wane ne Farouk Lawan.
Wane ne Farouk Lawan?
Farouk Lawan ɗan asalin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ne.
An zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Ɓagwai/Shanono daga jihar Kano tun a shekarar 1999.
Sannan ya yi ta maimaitawa har sau huɗu wato tun daga zaɓukan 1999 har zuwa na 2015 ƙarƙashin jam'iyyar PDP da take mulki a waɗannan lokuta.
Sai dai ya sha kaye a zaɓen 2015, lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasarar farko a ƙasar.
Farouk Lawan ɗan majalisa ne mai matuƙar ƙarfin faɗa a ji a majalisar dokoki a wancan lokacin.
Ya taɓa zama shugaban Kwamitin Kuɗi na Majalisar Wakilai a lokacin da Aminu Bello Masari ke jagorantar ta.
Lawan ne ya jagoranci wata gamayya ta ƴan majalisa wato Integrity Group, masu son tabbatar da gaskiya da suka yi adawa da Shugabar Majalisa Patricia Etteh a lokacin da ta shiga wata badaƙalar cin hanci a 2007, wadda har ta yi sanadiyyar yin murabusa ɗinta.
A dalilin wannan lamari ne har aka ba shi laƙabin Mr Integrity a majalisar.
Shi ne kuma shugaban kwamitin da ya jagoranci duba kan yadda ake kashe kuɗaɗen tallafin mai.

Wasu labaran da za ku so ku karanta

Wace badaƙala ce ta kai Lawan yanayin da yake a yau?

Asalin hoton, INSTAGRAM - FEMI OTEDOLA
A watan Janairun 2012 ne Lawan ya jagoranci kwamitin bincike kan yadda ake kashe kuɗaɗen tallafin mai na gwamnati.
An kafa kwamitin ne a lokacin da gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ta janye tallafin man fetur abin da ya jawo ƙarin farashin man, lamarin da ya haifar da zanga-zangar da aka yi wa laƙabi da "Occupy Nigeria" a faɗin ƙasar.
Rahoton da kwamitin ya fitar a watan Afrilun shekarar ya bankaɗo gagarumar badaƙala a tsakanin kamfanonin man fetur a ƙasar na yadda ba sa biyan tallafin man da gwamnati ke biya na miliyoyin daloli.
An ƙiyasta cewa wannan badaƙala ta danne kuɗaɗen gwamnati ta jawowa Najeriya asarar dala biliyan 6.8 a wancan lokacin.
Daga baya shugaban ɗaya daga cikin kamfanonin man fetur din da ake zargi da hannu a badaƙalar wato Femi Otedola ya yi zargin cewa, ɗan majalisa, Farouk Lawan ya karɓi cin hanci domin fitar da kamfaninsa daga cikin jerin kamafonin da kwamitin majalisar wakilan ya bincika.
A watan Janairun 2013 aka tuhumi Farouk da zargin cin hanci na karɓar sama da dala dubu 600 a matsayin toshiyar baki domin ya rufa wa kamfanin mai na Mista Otedola asiri.
Otedola ya yi zargin cewa Lawan ne ya buƙaci cin hancin da niyyar rufa wa kamfanin nasa na Zenox asiri, don cire shi daga jerin kamfanonin da ake zargi da ha'intar Najeriya.
Rahotanni a lokacin sun yi zargin cewa da fari kuɗaɗen da gwamnati ke bin kamfanin ya kai dala miliyan ɗaya, amma daga baya sai aka cire shi daga cikin rahoton.

Karin labarai masu alaƙa

An yi zargin cewa Mista Otedola ne ya dasa kyamara don naɗar Lawan a lokacin da aka kai masa kuɗin "toshiyar bakin," inda kuma kyamarar ta ɗauke shi.
Bidiyon mai tsawon minti biyu ya yaɗu sosai a shafukan intanet a wancan lokacin (shekarar 2012).
Sai dai tun a sannan Farouk Lawan ke kare kansa da cewa ya karɓi kuɗaɗen ne ba da niyyar rufa wa kamfanin Zenox asiri ba, sai don ya ga iya gudun ruwansu tare da miƙa lamarin ga Hukumar Yaƙi Da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati, EFCC.
Otedola ya ce ya kai ƙorafi ne gaban Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya DSS cewa Lawan ya buƙaci ya ba shi cin hancin dala miliyan uku don rufa wa kamfaninsa asiri.
Sai hukumar DSS ta tura jami'anta suka dasa kyamara a inda za a gana da Lawan sannan aka miƙa masa ƙunshin kuɗin.
Lawan ya karɓa ya sanya a aljihu sannan ya riƙe ɗaya ƙunshin a hannu kamar yadda aka gani a bidiyon.

Me ya faru a kotun ranar Talata?
Sai dai duk da cewa an yanke wa Lawan ɗauri a gidan yari a matsayin mai karɓar cin hanci, ba a yanke wa Otedola da ya bayar hukunci ba, wani lamari da lauyoyi suka ce shari'a ba ta gano shi da laifi ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a lokacin zaman sauraron shari'ar Otedola ya ce ba shi ya bai wa Lawan kuɗi ba Hukumar DSS ce ta ba shi.
Mai shari'ar ta ce ta samu Lawan da laifuka masu alaƙa da cin hanci sosai, sannan ta ce ya gaza gabatar da wani Honorabul Ribadu ko wani ɗan majalisar da ke cikin kwamitin don ba da shaida kan ikirarinsa na cewa ya karɓi kuɗaɗen ne don ya kama Otedola dumu-dumu.
Daily Trust ta ambato mai shari'ar na cewa: "Laifi ɗaya cikin tuhume-tuhumen da ake yi masa ba a kan zargi ba ne, a kan ƙwaƙƙwarar shaida ce.
"Lawan ya nemi Otedola ya ba shi dala miliyan uku a matsayin cin hanci, sai aka ba shi dala 500,000 sau biyu."
Sannan ta yi watsi da ikirarin Lawan cewa ya karɓi dala 500,000 don samun hujjar cewa Otedola yana ba su cin hanci shi da ƴan kwamitinsa.
Daga nan ne sai ta yanke hukuncin ɗaurin shekara bakwai a gidan yari kan laifi na farko da na biyu, sannan zai yi shekara biyar kan laifi na uku. Amma zai yi su ne a lokaci guda, ma'ana zai yi shekara bakwai.












