Muhammadu Buhari: Shugaban Najeriya ya ce gwamnatinsa ba ta cin hanci

Buhari

Asalin hoton, Presidency

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu kamshin gaskiya a rahoton da ƙungiyar Transparency ta fitar da ke cewa kasarsa ce ta biyu da ta fi cin hanci da rashawa a Afirka ta Yamma.

Mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu, wanda ya bayyana hakan a sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce duk wani bincike da za a yi a kan doron gaskiya zai nuna cewa gwamnatin Buhari tana cin galaba a yakin da take yi da hanci da rashawa.

Ya ce ba a yi musu adalci ba a rahotan, domin duk wanda ya san ƙasar da abubuwan da ke faruwa ya san gwamnatinsu na kokari matuka.

A cewarsa: "Gwamnatin Buhari ta cancanci yabo wajen kawar da cin hanci a ayyukan gwamnati kuma za ta ci gaba da yin aiki tukuru domin goyon bayan hana cin hanci da hukunta masu yinsa da kuma wayar da kan jama'a da hukumomin yaki da cin hanci suke yi.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Rahoton Transparency ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta biyu cikin ƙasashen da aka fi tafka rashawa a yammacin Afirka a shekara ta 2020.

Wannan na nuna cewa rashawar da ake tafkawa a ƙasar ta karu cikin shekaru biyu.

Najeriya dai na bin Guinea Bissau wacce ita ce ta ɗaya a ƙasashen da aka fi tafka rashawa a yankin kudu da hamadar saharar Afirka.

Sai dai Garba Shehu ya ce suna nazari kan hujjojin da ƙungiyar ta yi amfani da su wajen fitar da rahotonta.

Ya kuma bayyana irin nasarar da ya ce suna samu a yaƙi da rashawa da kuɗaɗen da aka ƙwato da matsayin da gwamnatinsu ke kai a yanzu

Rahoton, wanda aka fitar tare da hadin-gwiwar kungiyar da ke fafutukar inganta harkokin majalisun dokoki ta CISLAC, ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta samu koma-baya dangane da yadda al`ummar kasar ke kallon yakin da take yi da cin hanci da rashawa.

Rahoton ya ce matsalar rashawa ta yi wa kasar tarnaki, saboda ta dabaibaye aikin gwamnati da sauran bangarorin rayuwa.

Rahoton ya kuma nuna yadda annobar korona ya bankado irin wadanan rashawar da gibin da ake dashi a fannin lafiya da yada aka rinƙa handame kuɗaɗen tallafin gaggawa.

Mallam Awwal Musa Rafsanjani, wakilin kungiyar Transparency International a Najeriya ya ce "Cin hanci da rashawa a harkar tsaro ya ja har aka yi zanga-zangar #EndSars.

zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan Oktobar 2020 ne matasa a Najeriya suka yi zanga-zangar nuna adawa da cin zarafin da ake zargin 'yan sanda na aikatawa

"Sannan wannan annobar ma kanta, ana cin hanci da rashawa da ita. Kayan abinci da ya kamata a rabawa mutane a rage masu radadin annobar, an ki ba su," a cewar Awwal Musa Rafsanjani.

Rafsanjani ya ce duk da arziƙin da Najeriya ke da shi, cin hanci da rashawa ya sa tana fuskantar koma-baya.

Ya ce gwamnatin Najeriya ba ta yaki da cin hanci da rashawa yadda ya kamata.

"Muna da jihohi 36 a ƙasar nan amma ba su ma san ana yaƙin ba, ministoci ba su san da wanann tsarin ba a ma'aikatunsu, ai wannan ba yaƙi da cin hanci da rashawa ba ne," a cewarsa.

Ya zargi gwanatin da amfani da taken 'Yaƙi da cin-hanci da rashawa ne kawai a matsayin wani salo na cin zaɓe.

Ya ce Najeriya na iya magance wannan matsala ta hanyar saka dokokin kariya ga masu bankaɗo masu cin hanci da rashawa.

Sannan ya ce idan aka sa dokoki kan dukiyar Najeriya da aka sace aka adana a ƙasashen waje, ana iya ganin sauyi mai kyau a yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.