Najeriya ce ƙasa ta biyu da aka fi tafka rashawa a yammacin Afirka - Transparency

Asalin hoton, Presidency
Najeriya ce ƙasa ta biyu cikin ƙasashen da aka fi tafka rashawa a yammacin Afirka a shekara ta 2020, a cewar ƙungiyar Transparency International.
Wannan na nuna cewa rashawar da ake tafkawa a ƙasar ya karu kamar yadda rahotanta ke nunawa cikin shekaru biyu.
Najeriya dai na bin Guinea Bissau wacce ita ce ta ɗaya a ƙasashen da aka fi tafka rashawa a yankin kudu da hamadar saharar Afirka.
Rahoton wanda aka fitar tare da hadin-gwiwar kungiyar da ke fafutukar inganta harkokin majalisun dokoki ta CISLAC ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta samu koma-baya dangane da yadda al`ummar kasar ke kallon yakin da take yi da cin hanci da rashawa.
Rahoton ya ce matsalar rashawa ta yi wa kasar tarnaki, saboda ta dabaibaye aikin gwamnati da sauran bangarorin rayuwa.
Rahoton ya kuma nuna yadda annobar korona ya bankado irin wadanan rashawar da gibin da ake dashi a fanin lafiya da yada aka rinƙa handame kuɗaɗen tallafin gaggawa.
Mallam Awwal Musa Rafsanjani, wakilin kungiyar Transparency International a Najeriya ya ce "Cin hanci da rashawa a harkar tsaro ya ja har aka yi zanga-zangar #EndSars.

Asalin hoton, Getty Images
"Sannan wannan annobar ma kanta, ana cin hanci da rashawa da ita. Kayan abinci da ya kamata a rabawa mutane a rage masu radadin annobar, an ki ba su," a cewar Awwal Musa Rafsanjani.
Rafsanjani ya ce duk da arziƙin da Najeriya ke da shi, cin hanci da rashawa ya sa tana fuskantar koma-baya.
Ya ce gwamnatin Najeriya ba ta yaki da cin hanci da rashawa yadda ya kamata.
"Muna da jihohi 36 a ƙasar nan amma ba su ma san ana yaƙin ba, ministoci ba su san da wanann tsarin ba a ma'aikatunsu, ai wannan ba yaƙi da cin hanci da rashawa ba ne," a cewarsa.
Ya zargi gwanatin da amfani da taken 'Yaƙi da cin-hanci da rashawa ne kawai a matsayin wani salo na cin zaɓe.
Ya ce Najeriya na iya magance wannan matsala ta hanyar saka dokokin kariya ga masu bankaɗo masu cin hanci da rashawa.
Sannan ya ce idan aka sa dokoki kan dukiyar Najeriya da aka sace aka adana a ƙasashen waje, ana iya ganin sauyi mai kyau a yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.











