Coronavirus: Abubuwa 4 da har yanzu ba mu sani ba game da riga-kafin korona

    • Marubuci, José Carlos Cueto
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo

Ana gaggawa domin kada lokaci ya kure.

Wannan ita ce hanyar da za mu iya kamanta kokarin yadda za a gudanar da allurar riga-kafin korona ga al'ummar duniya, da kuma sake dawo da yanayin rayuwa ya tafi yadda ya kamata ba tare da bata lokaci ba.

Daga ranar 23 ga watan Janairu, mutane fiye da miliyan 60 ne aka riga aka yi wa allurar riga-kafin wannan cutar.

Amma yayin da karin wasu kasashen suka fara gudanar da gangaminsu na riga-kafin, akwai abubuwa da dama da har yanzu ba a sani ba.

Har yanzu ba a san tsawon lokacin da garkuwar da alluran riga-kafin suka samar zai kai, ko kuma idan sabon nau'in kwayar cutar da ta bulla a fadin duniya ya bijire ta kuma karya lagonsu ba.

Kusan watanni biyu bayan shirin gagarumin riga-kafin a tarihinmu ya fara, mun duba muhimman tambayoyi hudu da har yanzu ba a san amsarsu ba.

1. Tsawon wane lokaci ne alluran riga-kafin za su kai suna bayar da garkuwa?

Yanayin garkuwar da muka samu bayan kamuwa da cutar korona ko kuma samun riga-kafin na daya daga cikin tambayoyin da muka fi tambayar kanmu a watannin baya-bayan nan.

Shekara daya bayan barkewar annobar, an riga an wallafa binciken farko game da batun garkuwar jikin a cikin matsakaici da dogon zango.

Bincike a wannan bangare ya takaita kasancewar ba a dade ana gudanar da shi ba, saboda tsawon lokacin da aka dauka kafin a kirkiro alluran riga-kafin, amma kamar yadda cibiyar nazari kan garkuwar jikin dan adam ta La Jolla da ke jihar California ta bayyana, karfin garkuwar jikin bayan karawa da kwayar cutar kan ci gaba da kasancewa da karfinsu har na tsawon kusan watanni shida.

Wannan daidai yake da sakamakon binciken cibiyra kula da lafiyar al'umma ta Ingila, wacce ta bayar da shawarar cewa wadanda suka kamu da cutar korona na samun kariya ta akalla watanni biyar.

Bayan yin la'akari da cewa kamuwar farko da kwayoyin cutar ba su dauki tsawon lokaci ba kafin wannan, wasu masana kimiyya na da karfin gwiwar cewa garkuwar jikin za ta iya kai har tsawon lokaci, har ma shekaru.

Ko shakka babu, hakan ba lallai ya kasance daya da duka wadanda da suka kamu ba. Ko wanne zai iya yiwuwa ya samu kariya fiye da ko kuma kasa da yadda ake bayyana, kana yiwuwar sake kamuwa da cutar zai danganta ga hakan.

"Yana da wahala a fadi tsawon lokacin da garkuwar jikin za ta kai saboda yanzu muka fara gudanar da riga-kafin, kuma zai iya kasancewa da banbanci don ya danganta ga maras lafiyar da kuma irin allurar rigakafin, amma me yiwuwa tsakanin watanni shida zuwa sha biyu,'' Dr Julian Tang, kwararre a fannin kwayoyin cuta a Jami'ar Leicester da ke Birtaniya ya shaida wa BBC.

Dr Andrew Badley, farfesan harhada magunguna a asibitin Mayo Clinic da ke Amurka yana cike da fata: "Ina da karfin gwiwar cewa karfin alluran riga-kafin zai yi tasiri sosai kan garkuwar jikin har na tsawon shekaru.

"Yana kuma da muhimmanci a yi cikakken nazari kan wadanda suka kamu da sabuwar nau'in cutar kana a lura da yadda marasa lafiyar ke murmurewa daga alluran.''

2. Shin akwai yiwuwar sake kamuwa da cutar korona bayan yin riga-kafin?

Kwarai, zai iya yiwuwa, kuma a bisa dalilai da dama.

Ba farko shi ne, kariyar da akasarin alluran riga-kafin za su bayar yana daukar tsawon makonni biyu zuwa uku bayan yi wa mutane kafin su fara aiki, ya danganta kuma da irin ruwan allurar riga-kafin.

"Idan ka yi mu'amala da wanda ya kamu da kwayar cutar kwana daya ko mako guda bayan an yi maka allurar riga-kafin, duk da haka kana cikin hadarin kamuwa da cutar kuma za ka iya yadawa sauran mutane,'' Tang ya yi wa BBC karin bayani.

Amma ko da a ce mutum ya yi mu'amala da wadanda suka kamu makonni da dama bayan yin riga-kafin akwai yiwuwar ya kamun.

"Wasu bayanai da aka riga aka tattara sun nuna cewa daidaikun mutane ka iya cigaba da kamuwa da cutar korona, duk da cewa kwayar cutar ba za ta zama da karfi a jikinsu ba, kana ba za su yi rashin lafiya mai karfi ba, fiye da wadanda bas u kamu ba ko kuma ba a yiwa riga-kafin ba,'' in ji Dr Badley.

Don haka, akwai yarjejeniyar cewa alluran riga-kafin za su iya bayar da kariya ga daidakun mutane sosai, amma kuma har yanzu akwai ayar rambaya game da girman aikin za su yi wajen hana kamuwa da kwayar cutar.

3. Shin alluran riga-kafin za su iya bayar da kariya daga sabuwar nau'in cutar ta korona?

Wannan babban abin damuwa ne.

Kwayoyin cutar suna yawan sauya fasali kana wasu lokuta suna yin hakan ne don su kara samun karfin bijire wa alluran riga-kafin, don haka suna bukatar sabunta kansu.

Sabuwar nau'in kwayar cutar korona a aka gano a Afirka ta Kudu ko a Birtaniya ta riga ta bazu zuwa wasu kasashen kuma sun yi kaka-gida saboda yawan adadin wadanda suka kamu.

Cibiyar harhada magunguna ta Moderna ta sanar a ranar Litinin cewa alluran rigakafinta har yanzu suna da karfi kan sabuwar na'uin kwayar cutar ta korona ta Birtaniyar da Afirka ta Kudu.

Kamfanin harhada magunguna na Pfizer/BioNTech shi ma ya yi ikirarin cewa alluran rigakafinsa na zai yi tasiri sosai kan sabuwar kwayar cutar.

"Dole a yi la'akari da cewa duk da alluran rigakafin da aka riga aka amince da su suna da inganci, bas u kai ingancin da za a ce dari bisa dari ba kan sabuwar nau'in cutar ta korona, ko kuma ma ta farkon ," in ji Dr Badley.

"Kariyar da alluran rigakafin za su bayar, ta danganta da sabuwar nau'in kwayar cutar ta banbanta da tsohuwar,'' Dr Tanga ya yi karin bayani.

A takaice, ya kamata gwamnatoci da ma'aikatun kiwon lafiya su bukaci sa ido da gano sabbin nau'ikan kwayoyin cutar da ka iya barkewa su yi nazari ko alluran rigakafin da ke hannu suna da tasiri a kan su.

4. Sau nawa kuma zuwa tsawon wane lokaci ya kamata a rika yin riga-kafin?

An bayar da kashi biyu na ruwan alluran rigakafin kamfanonin harhada magunguna na Pfizer da Moderna da kuma AstraZeneca na Jami'ar Oxford.

Da farkon fari, a bisa yanayin gwaje-gwajen alluran da aka yi, an shaida wa mutane cewa za yi musu riga-kafin karo na biyu makonni uku zuwa hudu bayan na farkon.

Amma a karshen shekarar 2020, Birtaniya ta sanar da cewa za ta fi bayar da fifiko wajen yi wa mutane da dama rigakafin kashi na farko kana za ta bayar da kasha na biyu watanni uku bayan na farkon.

An bayar da kashi biyu na ruwan alluran riga-kafin kamfanonin harhada magunguna na Pfizer da Moderna da kuma AstraZeneca na Jami'ar Oxford.

Da farkon fari, a bisa yanayin gwaje-gwajen alluran da aka yi, an shaida wa mutane cewa za yi musu rigakafin karo na biyu makonni uku zuwa hudu bayan na farkon.

Amma a karshen shekarar 2020, Birtaniya ta sanar da cewa za ta fi bayar da fifiko wajen yi wa mutane da dama riga-kafin kashi na farko kana za ta bayar da kasha na biyu watanni uku bayan na farkon.