Tarihin sabbin manyan hafsoshin sojin Najeriya

sabbin manyan hafsoshin sojin Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da naɗa sabbin manyan hafsoshin soji bayan sallamar waɗanda ya naɗa bayan hawan mulkinsa.

Janar Leo Irabor ne aka naɗa babban hafsan tsaro; Janar I. Attahiru a matsayin babban hafsan sojan ƙasa.

Rear Admiral A.Z Gambo aka naɗa babban hafsan sojan ruwa sai Air-Vice Marshal I.O Alao a matsayin babban hafsan sojan sama.

Manjo Janar Attahiru - Babban hafsan sojan ƙasa

Manjo Janar Attahiru

Asalin hoton, Presidency

Manjo Janar Ibrahim Attahiru shi ne ya maye gurbin Janar Tukur Buratai babban hafsan sojan ƙasa.

Janar Attahiru ɗan asalin jihar Kaduna ne a arewacin Najeriya.

Kafin ba shi wannan muƙamin, Manjo Janar Attahiru shi ne shugaban runduna ta 82 a rundunar sojin Najeriya.

Ya taba jagorantar yaƙi da ƙungiyar Boko Haram amma a shekarar 2017 ne Janar Tukur Buratai ya sauke shi daga muƙamin bayan wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai inda aka kashe wasu mutane 50 a lokacin da suke sallah a masallaci.

Dama dai Buratai ya ba shi wa'adin kamo shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a mace ko a raye.

Janar Nicholas Rogers ne ya maye gurbinsa.

Manjo Janar Leo Irabor - Babban hafsan tsaro

Manjo Janar Leo Irabor

Asalin hoton, Presidency

Manjo Janar Leo Irabor wanda Buhari ya naɗa babban hafsan tsaro ya taɓa riƙe muƙamin kwamandan Operation Lafiya Dole, rundunar da ke yaƙi da ƙungiyar Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya.

A shekarar 2017 ne aka cire shi kuma Manjo Janar I Attahiru ne ya maye gurbinsa.

Daga nan ne kuma Irabor ya zama babban kwamanda na Rundunar Hadin Gwiwa ta kasashen tafkin Chadi da ke fama da matsalar Boko Haram wato Najeriya da Nijar da Kamaru da Benin da Chadi.

Air-Vice Marshal I.O Amao - Babban hafsan sojan sama

Air-Vice Marshal Isiaka Oladayo Amao

Asalin hoton, Presidency

Air-Vice Marshal Isiaka Oladayo Amao sabon babban hafsan sojan sama ya maye gurbin Air Marshal Sadique Abubakar ne.

Babban jami'in sojan na sama ya samu horon sojan sama a ƙasashe India da China da kuma Pakistan.

Rear Admiral A.Z Gambo - Babban hafsan sojan ruwa

Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo

Asalin hoton, Presidency

Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo kafin naɗa shi babban hafsan sojan ruwa, ƙwararre ne a aikin tsaron ruwa da leƙen asiri.

Ɗan asalin jihar Nasarawa ne a yankin arewa ta tsakiya. Babban jami'in ya samu horon aikin sojan ruwa a Jaji da Afirka ta Kudu.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Wannan layi ne