Daliban Kankara: Shin rufe makarantun boko a arewa nasara ce ga Boko Haram?

Asalin hoton, Getty Images
Rufe makarantu a arewacin Najeriya ya haifar da saɓanin ra'ayi tsakanin masana inda wasu ke ganin matakin "fargar jaji ne" wasu kuma suna ganin babu wani zaɓi.
Sace ɗaliban makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina da ƴan bindiga suka yi ya tayar da hankalin Najeriya da duniya, dalilin da ya sa wasu jihohin arewa da ke fama da matsalar tsaro suka sanar da rufe ƙanana da manyan makarantunsu.
Gwamnatocin Katsina da Zamfara da Kano sun rufe makarantun ne saboda dalilin tsaro, yayin da kuma Kaduna da Jigawa suka ce saboda dalilai na annobar korona.
Sai dai masana sha'anin tsaro, da masu sharhi kan lamuran yau da kullum na ganin cewa gwamnatocin jihohin na arewa maso yammacin Najeriya sun yi gaggawa wajen rufe makarantun.
Ta wata fuskar kuma, masana na ganin gwamnonin ba su da zaɓi domin sace ɗaliban wani babban tashin hankali ne kuma rufe makarantun mataki ne da ya dace saboda rashin tabbas kan abin da zai iya biyo wa baya bayan abin da ya faru a Kanƙara.
Boko Haram ta yi iƙirarin ɗaukar alhakin sace daliban, a wani saƙon bidiyo da shugaban ƙungiyar ya fitar, ko da yake gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya musanta iƙirarin na Boko Haram.

Rufe makarantu ba alheri ba ne

Asalin hoton, Getty Images
Masu sukar matakin na ganin rufe makarantun ba zai haifar da alheri ba, musamman idan aka yi la'akari da cewa wasu daga cikin jihohin sun kasance koma-baya a ɓangaren ilimi.
Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin harkokin tsaro a Najeriya da yankin Sahel, ya ce maimakon rufe makarantun ya kamata a ce gwamnatocin jihohin sun aiwatar da wani ƙudiri na tabbatar da tsaron makarantun.
A cewar masanin tsaron ya kamata gwamnatocin su haɗa gwiwa da ƴan majalisun dokoki wajen zartar da wasu ƙudurori na ƙasa da ƙasa da aka tsara don kare lafiyar ɗalibai da harkokin ilimi, wato Save schools Declaration.
Ya ce ƙudirin abubuwa uku yake son cimma, tsaro da kare rayukansu ɗalibai da masu koyarwa da kuma ma'aikata da garuruwan da makarantun suke zaune wanda ya kamata a inganta tsaronsu.
"Don haka rufe makarantu ba zai haifar da alheri ba," in ji shi.
Dr Abubakar Kari na jami'ar Abuja a nasa ra'ayin yana ganin matakin tabbatar da tsaro yana da muhimmanci ƙwarai da gaske kuma babu wani abin da za a iya cimma idan babu tsaro.
Sai dai ya ce tun kafin abin da ya faru a Kanƙara akwai barazana ta tsaro daban-daban - kuma za a iya cewa ɗaya daga cikin dalilin barazanar shi ne rashin kin ɗaukar mataki a lokacin da ya dace ko matakin da ya kamata gwamnonin su ɗauka.
"Za a iya cewa matakin rufe makarantun fargar jaji ne ko kuma gwamnonin sun makara domin da daɗewa ya kamata su ɗauki matakan da zai hana wannan yanayi na satar ɗalibai har ya kai ga rufe makarantu."
Amma a ra'ayinsa Dr Suleiman Amu Suleiman na ABTI a Yola ya shaida wa BBC cewa, matakin da gwamnonin suka dauka ya dace saboda harkar tsaro ba a hannunsu take ba tana hannun gwamnatin Tarayya.
"Kana gwamna ka wayi gari an ɗibi yara 600 a wata makaranta a jiharka hankalinka zai tashi - ba kuma wanda ya san me zai iya biyo baya bayan abin da ya faru, don haka ba su da zaɓi," in ji shi.
Abin da ya faru faru a Chibok da Dapchi ya kamata ace gwamnatin Najeriya ta ɗauki darasi kafin sake faruwan hakan a Dapchi, kuma wannan ya sa aka fito da wani kuɗiri wanda da ya zayyana dalla-dalla matakan da ya kamata gwamnatoci su ɗauka don tabbatar da tsaro a makarantunsu.
A cewar Dr Kari kusan duk jihohi ba su aiwatar da matakan ba sai dai kawai a takarda. "Muna ganin da a ce an ɗauki matakan da abin da ya faru a Kanƙara ba zai faru ba kuma da yanzu bai kai ga rufe makarantu ba."

Abin da rufe makarantu zai haifar

Duk da saɓanin ra'ayi tsakanin masana kan matakin rufe makarantun amma suna ganin an shiga yanayi na rashin tabbas na ranar buɗe wanda zai haifar da cikas ga ilimi baki ɗaya da kuma harkar koyarwa da sauransu .
Akwai abubuwa da dama da masanan ke ganin za su iya faruwa sakamakon rufe makarantun.
Wasu iyaye za su iya amfani da wannan dalili su cire yayansu daga makaranta - ba za su bar ƴaƴansu su koma makaranta ba saboda babu tsaro.
Wasu za su iya aurar da yayansu mata saboda yanayin ilimin da aka shiga na rashin tsaro.
Rufe makarantun zai kara haifar da munanan sakamako kamar zaman banza da kashe wando da aikata laifuka da sace-sace da shaye-shaye tsakanin samari.
Sannan yadda harakokin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa ko an buɗe makarantun babu wani tanadi na tsaro da aka yi don haka babu tabbas akan abin da ya faru a baya ba zai sake faruwa ba, musamman a Chibok da Dapchi da kuma Kanƙara.
Wannan yanayin na matsalar tsaro zai daɗa jefa yankin arewacin ƙasar cikin koma baya a harakar ilimi.
"Rashin tsaro da ake samu zai kara taɓarɓare harakar karatu a arewa. Kila ma yanzu tsaikun da aka samu idan yaro ya kamata ya ƙare firamare a shekara biyar yanzu sai ya kara shekara biyu a karatunsa," in ji Dr Amu.
Ya kuma ce hakan zai shafi tsarin jarabawa ta kammala sakandare.

Taɓarɓarewar Ilimi a arewa

Asalin hoton, Getty Images
Masanan na ganin wannan wani mummunan koma-baya ne ƙwarai da gaske game da harkar ilimi domin idan an rufe makarantu ba maganar karatu kuma babu maganar ilimi.
Dr Kari ya ce rufe makarantun cikas ne musamman ganin jihohin arewa suna fama da matsanancin taɓarɓarewar ilimi. Kuma yankin na fama da yaran ba su karatu waɗanda ya kamata a ce suna makaranta.
"Ba shakka harakar ilimi za ta samu nakasu ƙwarai da gaske tun da an yi wata da watanni babu karatu saboda matsalar korona kuma an buɗe na wata biyu amma yanzu an rufe ba a san ranar da za a buɗe ba."
"Wannan mummunan koma-baya ne ga harakar ilimi," in ji masanin.
Harkar ilimi a waɗannan jihohi za a iya cewa ta samu kanta a wani mawuyacin hali, kasancewar ba su kammala warwarewa ba bayan rufe wa da aka yi a sakamakon annobar korona, sai ga shi lamarin tsaro ya sake jefa yankin cikin halin rashin tabbas.

Ilimin Boko a arewa - Boko Haram
Matakin rufe makarantun wasu na ganin kamar miƙa wuya ne ga ɗa'awar Boko Haram da ke adawa da ilimin karatun boko a Najeriya.
Kuma yankin can dama yana fama waɗanda karatun boko bai dame su ba - kamar mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki dama wasu na neman dalili kuma yanzu sun samu damar cire ƴaƴansu.
Masharhanta na ganin, sakamakon abin da ya faru na rufe makarantu tamkar ya zama boko haram - tun da barazana ta sa an rufe makarantu don haka ba maganar boko kenan.
"Waɗanda ke da aƙida ta Boko Haram da niyya da mafutarta ta samu nasara kenan a kaikaice," in ji Dr Kari.

Mafita
Duk lokacin da aka ce akwai matsala dole gwamnati ta bayar da muhimmacnci wajen dau matakai na nan take- maganar tsaro dole ace gwamnati ta tura jami'an tsaro tare da basu kayan aiki.
Masana na ganin samar da jami`an tsaro a makarantu abu ne mai wuya, amma jami'an tsaro za su iya rarraba al'ummomi zuwa yanki-yanki sannan su duba yadda za su yi ƙawanya wajen kare su.
Kamar yadda jihar Kano ta mika wani kaso na dazukanta ga sojoji suka kafa sansanoni a dazukanta, a cewar Dr Kabiru Adamu ya kamata gwamnonin jihohin Katsina da Zamfara su ɗauki irin matakin.
Sannan hakkin gwamnati ta tabbatar da cewa duk ta magance matsalolin da ke addabar al'ummarta - "duk wani mataki da ya kamata gwamanti ta ɗauka ta kawar da wannan yanayi na rashi tsaro da barazana na ayyukan ta'addanci ya kamata ta ɗauki dau matakai nan take.
"Idan har gwamnatida gaske take za ta iya yin haka kuma abu ne da ya kamata a yi a gaggawa. abin da ya faru a Kankara da Chibok da Dapchi abin takaci ne da nuna gazawa," in ji Dr Kari na Jami'ar Abuja.












