Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Sheikh Karibullah Nasir Kabara
Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Karibullah Nasir Kabara kuma shugaban ɗariƙar Ƙadiriyya ta Afirka ya ce yana da gashin Annabin Allah Muhammad SAW a ajiye a wajensa.
Malamin ya faɗi hakan ne a cikin shirin Ku San Malamanku na BBC Hausa, har ma kuma ya nuna wa Yusuf Ibrahim Yakasai gashin.
Sheikh ya ce wannan abu shi ne wanda ya fi saka shi farin ciki a duniya fiye da komai. Kuma ya samu gashin ne daga wajen wani babban malami da ya kai masa ziyara Kano daga ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Sheikh Karibullah ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambaya kan abin da ya fi saka shi farin ciki a duniya inda ya ce hakan na da alaƙa ne da wani mafarki da ya ta ba yi a lokacin bai wuce shekara 10 ba a duniya.
"Na taɓa yin mafarki wani babban malami daga cikin malamanmu ya ba ni wuƙar zinare a hannun dama, sai wani babban malamin ya sake ba ni wata wuƙar, na kasa mantawa da mafarkin har sai da Allah Ya kawo wani lokaci shekara tara da suka wuce.
"Allah Ya kawo wani babban bawan Allah daga ƙasar UAE ana ce masa As-Sheikh Ahmadul Khadraji, wannan bawan Allah gidansu ya yi fice tuntuni suna gadon mallakar gashin Annabi SAW.
"Wato tun kakannin kakanninsa, saboda a zamanin Annabi SAW idan ya yi aski ya kan raba wa sahabbansa gashin nasa, wasu ya ba su da yawa wasu kaɗan.
"To gashin Manzon Allah kuma yana da wata hususiya da komai daɗewar da zai yi ba ya lalacewa ko sauya kama. Ko kwanaki na ji wani shiri da BBC ta yi kan wasu kayayyakin Manzon Allah SAW da aka samu a Turkiyya shekara 1442 amma ba abin da suka yi," in ji Malam.
Ya ci gaba da cewa "wannan mafarki da na yi sai Allah Ya kawo wannan mutumin da ya gaji gashin nan ya ba ni sili ɗaya da ya sako shi a wata ma'ajiya da aka yi da gwal wacce ta kai tsawon hannuna haka. Ɗaya silin kuma aka sa irin ɗaya ma'ajiyar amma ta azurfa fara.
"To sai ya sako gashin ɗaya a mai kalar gwal ɗaya a mai kalar azurfa ya zo wajen taron Maulidin Ƙadiriyya ya ba ni kyautarsa.
"To gaskiya na kasa manta wannan abu. Wannan wuƙaƙen da na yi amfarki an ba ni ashe su ne ma'ajiyoyin nan guda biyu da aka sako gashin Manzon Allah SAW aka ba ni," a cewar Sheikh Kabara.
A ɓangaren abubuwan da Malam ya tsani gani kuwa ya ce ba su wuce biyu ba.
"Na farko na tsani na ga an saki layin da aka san matasan Musulmai a kai. Na biyu ba na jin daɗi idan na ga abubuwa na rashin daɗi suna faɗaɗa wanda kuma haƙƙi ne na hukuma amma ba a yi ƙoƙarin shawo kansu ba da za su iya jawo wa ƙasa koma baya."
Asalin malam
Sheikh Karibullah Nasir Kabara haifaffen birnin Kano ne kuma ɗa ne ga marigayi Sheikh Nasir Kabara shugaban ɗariƙar Ƙadiriyya na Afirka Ta Yamma.
Bayan rasuwar mahaifinsa sai ya gaje shi inda ya ɗare shugabancin ƙungiyar ta Ƙadriyya kusan shekara 25 kenan a yanzu.
Ya fara karatu a gaban mahaifinsa a nan cikin unguwar Kabara sannan ya halarci makarantu da suka haɗa da ta Ma'ahadid Din ta mahaifinsa.
Sannan ya yi makarantar addinin Musulunci ta Aliya a Shahuci, daga bisani kuma ya je Jami'ar Bayero da ke Kano inda ya karanta Arabiyya.
Wace sura malam ya fi so a ƙur'ani?
Al-Ƙur'ani dukkaninsa zinare ne amma Sheikh ya ce yana matuƙar son Suratu Yusufa saboda ta bayar da ilimi iri-iri, "daga cikin abin da yake ba ni sha'awa da ita Allah Ya bayar da darasin da za a samu ilimi a kan dukkan wata rayuwa ta duniya.
"Na amfanu da yawa musamman a lokutan da na samu kaina a wannan nauyi da wannan amanar da Allah Ya ɗora min, da yawa abubuwan da suke faruwa ko na samu wata matsala ko damuwa to a ciki nake samun mafita."
Shugaban na ɗariƙar Ƙadiriyya a Afirka ya kuma ce ya rubuta litattafai da dama, musamman kan darikun sufaye a Najeriya, da kuma shigar musulunci yankin Najeriya darurwan shekaru gabanin zuwan Shehu Usmanu Dan Fodiyo.
Wasanni na ƙuruciya
Malam ya ce shi bai samu lokacin yin wasanni na yara sosai ba a lokacin ƙuruciyarsa don ko yaushe yana tare da babansa, "duk inda zai motsa tare muke tafiya tun daga lokacin da na kai shekara biyar."
Ya ƙara da cewa sai dai ɗan abin da ba a rasa ba a wasu lokuta da ba su da yawa.
Kan batun abincin da ya fi so kuwa Sheikh ya ce yana matuƙar son shinkafa da dankalin Turawa da naman kaza da naman rago da tuffa da kuma rake.
Sheikh Ƙaribullah ya je ƙasashe da dama, wasu tare da mahaifinsa wasu kuma shi kaɗai. "A ƙasashen Larabawa Yemen ce kawai ƙasar da ban je ba. A sauran ƙasashen duniya kuwa nan gaba burina shi ne na je ƙasar Rasha."
Malam ya ce burinsa a nan gaba shi ne a kafa wani tsari a Najeriya na yadda za a tarbiyyantar da yara al'ummar Musulmai irin yadda addinin Musulunci yake a mataki sahihi.
Sheikh yana da mata uku da ƴaƴa 19.