Mohammed bin Salman: Yaƙi uku da yariman Saudiyya ba zai taɓa samun galaba a kai ba

A handout photo shows Saudi Arabia's Crown Prince Mohammed bin Salman at the G20 Riyadh Summit, Riyadh, Saudi Arabia (21 November 2020)

Asalin hoton, EPA

    • Marubuci, Daga Frank Gardner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan sha'anin tsaro

A 'yan kwanakin nan dai, Saudiyya ba ta cikin sukuni musamman ma yarimanta mai jiran gado Mohammed bin Salman.

A ƙasar ta Saudiyya, Yariman ya yi fice, amma a ƙasashen ƙetare, ya kasa goge tabon zargin da ake yi masa na hannu a kisan ɗan jaridar nan Jamal Khasoggi a 2018.

Amma a halin yanzu, sabuwar gwamnatin Amurka na shirin shiga Fadar White House inda zaɓaɓɓen shugaban, Joe Biden ya bayyana a fili kan cewa zai ɗauki tsauraran matakai fiye da na wanda zai gada kan batun Saudiyya.

Waɗanne abubuwa ne a ƙasa a yanzu kuma me ya sa suke da muhimmanci ga Amurka da Saudiyya?

Yaƙin Yemen

Wannan yaƙin ya kasance bala'i ga duk wanda ya shafa, musamman talakawan Yemen da ke cikin hali na yunwa.

Ba Saudiyya ba ce ta fara wannan yaƙin - 'yan tawayen Houthi ne suka fara a lokacin da suka yi tattaki har cikin Sana'a babban birnin ƙasar a 2014 inda suka hamɓarar da gwamnatin ƙasar mai cikakken iko.

Houthi dai wata ƙabila ce daga tsaunin da ke arewacin ƙasar inda suke da kashi 15 cikin 100 na adadin jama'ar ƙasar.

A 2015, Yarima Mohammed bin Salman wanda a lokacin shi ne ministan tsaro na ƙasar, cikin sirri ya haɗa gamayyar wasu ƙasashen Larabawa inda ya ƙaddamar da yaƙi mai ƙarfi ta sama kan Yemen ɗin, inda a lokacin ya yi zaton cikin watanni kaɗan 'yan tawayen na Houthi za su yi saranda.

Sama da shekara shida, an kashe dubban mutane tare da raba da dama da muhallansu, inda kuma duka ɓangarorin suka aikata laifukan yaƙi, amma duk da haka Saudiyya ta kasa fatattakar 'yan tawayen na Houthi daga Sana'a da kuma akasarin yammacin ƙasar ta Yemen.

Da taimakon Iran, 'yan tawayen na Houthi na ci gaba da tura makaman roka da kuma ababen fashewa kan Saudiyya inda suke lalata wasu kayayyakin man fetur na ƙasar.

.

Asalin hoton, Reuters

A yaƙin dai na Yemen, yarjejeniyar zaman lafiya da dama da aka cimmawa ta rushe ɗaya bayan ɗaya.

Yaƙin na Yemen na kashe 'yan ƙasar tare da lashe aljihun Saudiyya, inda kuma mutane da dama a ƙasashen ƙetare ke caccakar wannan lamari.

.

Asalin hoton, Reuters

Sai dai lokaci na neman ƙure wa Saudiyya a ƙoƙarinta kan wannan yaƙi.

A 2016, a lokacin ƙarshen wa'adinsa, Shugaba Barack Obama, tuni ya fara rage taimakon da Amurka ke bayarwa kan yaƙin. Sai dai Donald Trump ya sauya tsarin inda ya bai wa Saudiyya duka goyon baya da bayanan sirri da kayan aikin da take buƙata.

A yanzu dai Mista Biden ya nuna cewa ba lallai ya ci gaba da bayar da wannan taimakon ba.

A yanzu dai an kunno wuta domin kawo ƙarshen wannan yaƙin ko ta wace hanya.

Matan Saudiyya da aka kulle

Wannan lamari ya jawo wa Saudiyya ce-ce-ku-ce ga daga ƙasashen duniya kan yadda ake gudanar da abubuwa a ƙasar.

An rufe wasu matan Saudiyya 13 masu zanga-zangar lumana, inda aka bayar da rahoton jin zarafinsu ta wani fannin, inda ake zargin su da laifin neman 'yancin tuƙa mota da kuma neman a bai wa mata walwala ba tare da muharammi ba.

Mata da dama, ciki har da Loujain al-Hathloul aka kama a 2018, kafin a cire haramta tuƙin motar mata a ƙasar.

Jami'ai a Saudiyya sun zargi Ms Hathloul da laifin leƙen asiri da kuma "karɓar kuɗi daga ƙasashen waje" sai dai jami'an na Saudiyya sun kasa kawo wata hujja.

Abokanta sun bayyana cewa ba ta yi komai ba in ban da halartar wani taron 'yancin ɗan adam a ƙasar waje tare da neman aiki a Majalisar Ɗinkin Duniya.

Danginta sun bayar da labarin cewa an doke ta, an azabtar da ita ta hanyar amfani da lantarki tare da yunƙurin yi mata fyaɗe a lokacin da take a rufe, kuma ganin da suka yi mata na ƙarshe, tana kyarma ba ƙauƙautawa.

.

Asalin hoton, Reuters

Kamar dai yadda Saudiyyar ta saka kanta a cikin yaƙin Yemen, wannan wani rami ne ƙasar ta gina wa kanta kuma ta faɗa inda a yanzu take neman mafita.

Bayan riƙe matan na lokaci mai tsawo, ba tare da wata hujja da za a nuna a kotu ba a ƙasar mai ɓangaren shari'a mai zaman kansa, hanyar fita daga wannan lamari ita ce neman sulhu.

Ana tunanin gwamnatin Biden za ta taso da wannan batu a nan gaba.

2px presentational grey line

Ƙauracewa Qatar

A 2017, a lokacin da Shugaba Trump ya kai ziyara Riyadh, Saudiyya ta haɗa kai da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Bahrain da Masar domin ƙauracewa makwabciyarsu da ke yankin Gulf wato Qatar.

.

Asalin hoton, EPA

Wannan tafiya ta haɗa ƙasashe uku na yankin Gulf masu ra'ayin mazan jiya mabiya Sunni wato Saudiyya da UAE da Bahrain da kuma kawarsu Masar.

Dalilin da ƙasashen suka bayar shi ne zargin da suke yi wa Qatar ɗin na goyon bayan ƙungiyar IS da ke jawo ayyukan ta'addanci.

Daular Larabawan ta samar da wasu shaidu da takardu da ke nuna cewa wasu 'yan ta'adda na zama a ƙasar, sai dai ƙasar ta musanta goyon bayan ta'addanci.

Kamar yadda 'yan tawayen Houthi suka yi a Yemen, an yi ta tunanin cewa 'yan Qatar ɗin su ma za su ɓalle daga baya su bayar da kai bori ya hau.

Sai dai hakan bai yiwu ba, ganin cewa ƙasar na da arziƙin iskar gas tare da zuba jari na kusan fam biliyan 40 a tattalin arziƙin Birtaniya kaɗai - tare da goyon bayan Turkiyya da Iran.