Saudiyya ta musanta 'ganawar sirri tsakanin Netanyahu da Yarima mai jiran gado' Mohamed bin Salman

Asalin hoton, Reuters
Ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan, ya musanta rahotannin da ke cewa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gana da Yarima mai jiran gado a Saudiyya Mohammed bin Salman.
Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce Mista Benjamin Netanyahu, ya tafi Saudiyya a asirce a ranar Lahadi don gana wa da Mohammed bin Salman da kuma sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo.
"Babu wata ganawa irin wannan da ta faru," a cewar sakon da Yarima Faisal bin Farhan Al Saud ya wallafa a Twitter.
Mr Netanyahu ya ki cewa komai kan bayanan bin diddigin zirga-zirgar jiragen sama da suka nuna cewa wani jirgin da Mista Netanyahu ke amfani da shi ya tafi birnin Neom, inda a can shi da Yariman da Mista Pompeo suka tattaunawa.
Ganawar ita ce irinta ta farko tsakanin shugabannin ƙasashen da suke da daɗaɗɗen tarihin gaba da juna, waɗanda a yanzu Amurka ke son shirya su.
A baya-bayan nan ne Shugaba Trump ya jagoranci sasanta tsakanin Isra'ila da ƙasashen UAE da Bahrain da Sudan.
Saudiyya ta yi taka tsan-tsan wajen yin maraba da lamarin, amma ta nuna cewa ba za ta bi sahu ba har sau an cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa.
A yanzu dai gwamnatin Trump na son janyo ra'ayin Saudiyya ta shirya da Isra'ila.
Wani ɗan jarida a Isra'ila Kan da wasu kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewa Mista Netanyahu da shugaban hukumar leƙen asiri ta Mossad, Yossi Cohen, sun tattauna da Yarima Mai Jiran Gado Mohammed da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo.
An yi ganawar ne a birnin Neom, wani tsararren waje na fasaha da yawon buɗe ido a gaɓar Kogin Maliya da ke arewacin Saudiyya, mai nisan kilomita 70 kacal daga kudancin Isra'ila, a cewar majiyoyi.
Bayanan bin diddigin zirga-zirgar jiragen sama na shafin FlightRadar24.com, an ga tashin jirgi daga filin jiragen sama na Ben Gurion da ke Tel Aviv a ranar Lahadi da rana, sannan jirgin ya bi ta kudu ta wajen gaɓar tekun yankin Sinai na Masar kafin ya bi ta Kogin Maliya ya shiga Saudiyya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Jirgin ya sauƙa a Neom jim kaɗan bayan ƙrfe 6.30 agogon GMT ya kuma shafe lokaci har zuwa ƙarfe 9.50 na dare a cewar bayanan. DAga nan sai ya koma birnin Tel Aviv ta hanyar da ya bi a yayin zuwa.
Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce jirgin na wani ɗan kasuwa ne a Isra'ila Udi Angel, kuma Mista Netnyahu ya sha amfani da shi wajen tafiye-tafiye zuwa wasu ƙasashen.
Ofishin Netanyahu bai tabbatar da rahoton ziyarar ba.
Amma wani ministansa Zeev Elkin ya shaida wa kafar yaɗa labaran Army Radio cewa: "Ba na cikin jirgin da ya je Saudiyyan."
Mai bai wa Netanyahu shawara kan kafofin yaɗa labarai Topaz Luk, ya wallafa wani saƙo a Tuwita mai nuna alamun lamarin ya tabbata: Gantz na wasa da hankali yayin da firaminista ke wanzar da zaman lafiya."

Asalin hoton, Reuters
Kafofin yada labaran Saudiyya sun ruwaito cewa Yarima Mohammed ya gana da Mista Pompeo a ranar Lahadi, amma ba su ambaci komai dangane da ziyarar Netanyahu ba.
Shugaba Trump ya ce yana fatan Saudiyya za ta shirya da Isra'ila amma wannan wani abu ne da ke fuskantar matsala.











