Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko alaƙar Isra'ila da ƙasashen Larabawa za ta janyo bazuwar makamai?
- Marubuci, Daga Tom Bateman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC na Gabas Ta Tsakiya, Jerusalem
Wata farfajiyar Fadar White House mai ciyayi nan ne wajen da Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana shirinsa na sabon "Zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya", wanda ya ce an cimma "ba tare da zubar da jini ba".
Wannan sabuwar yarjejeniyar za ta gida wata hulɗar kasuwanci tsakanin Isra'ila da ƙasashen Larabawa uku a karon farko cikin tarihi, ta kuma kawar da tsohuwar gaba.
Amma wannan yarjejeniya za ta samar da wasu abubuwan da ba yanzu za a gane alfanunsu ba a yanzu, kamar yadda firaiministan Isra'ila ya bayyana.
A gefe ɗaya kuma za ta mayar da hankali kan harkar kasuwancin makamai tsakaninsu.
Kasar farko da ta fara sanya hannu kan wannan yarjejeniyar ita ce Haɗaddiyar Daular Larabawa, za ta samu kyautar jirgin saman yaƙi daga Amurka.
Sannan Isra'ila, wadda ta fi kowace ƙasa a yankin karfin dakarun soji, za ta iya zuwa da wasu sabbin hulɗar makaman.
Gwamnatin Amurka na kallan wannan hulɗar kasuwancin a matsayin abin da zai taimaka wajen daidaitar karfin iko ga kawayenta da Iran ke yiwa barazana, wadda kuma ake matsa kallon barazana ga duniya baki daya.
Har yanzu tana da shakku a Gabas Ta Tsakiya, tare da tsoron bazuwar makamai da tsoron ci gaba da zubar da jini a yankin da manyan ƙasashen duniya ke yaƙin goyon bayan wasu.
Ta yaya zaman lafiya zai samu ta harkokin makamai?
Al'amarin Martaba
Wani jirgin yaƙi mai suna F-35 da ma'aikatar tsaron Amurka ta samar, na daya daga cikin makaman da suke da wuyar samu.
Haɗaddiyar Daular Larabawa ta yi ta ƙoƙarin sayan jirgin na tsawon shekara shida amma ba ta samu wannan damar ba daga Amurka, sai dai a yanzu ita ce ta farko a yankin larabawa da za ta fara mallakar makamin.
"Nan da shekara 20 sojojin saman za su rika yin abubuwan mamaki da jirgin yaki F-35, wadanda ba mu taba tunani ba a yau," in ji Mista Bronk wani babban jami'i a Amurka,
Ya ce samun wannan jirgin samunfurin F-35 ba ƙaramar martaba ba ce ga 'yan ƙasar Haɗaddiyar Daular Larabawa.
A ranar Alhamis, kafafen yaɗa labarai na Amurka sun rawaito gwamnatin Trump ta shaida wa majalisar dokokin kasar cewa za ta sayar wa da Hadaddiyar Daular Larabawa jiragen yaƙi na dala miliyan 10.
Wannan ba karamar nasara ba ce ga Hadaddiyar Daular Larabawa bayan shekaru da ta kwashe tana kokarin sayen jirgin.
Kawo ƙarshen matsaloli
Wannan yarjejeniyar da Trump ya jagoranta a watan Agusta ta sanya UAE ta zama daya daga cikin uku, kuma ta farko daga cikin yankin Gulf da suka sabunta alaƙarsu da Isra'ila.
A wajen Isra'ila kuwa, wannan wani ci gaba ne a tarihinta na karbuwar da ta yi a yankin, ga kuma bangaren alakar kasuwanci, wanda hakan yana nufin ci gaban tattalin arziki ne kuma samun wani iko ne ga harkokin tsaron wajen.
Falasdinawa na kallon wannan mataki a matsayin cin amana ga hadin kan kasashen Larabawa ɗan tabbatar mata da samun kasarsu.
Haka kuma an ci gaba da taso da wasu al'amura na daba a lokacin.
Minisatan harkokin wajen UAE Anwar Gargash ya ce yarjejeniyar za ta kawo karshen matsalolin da suke fuskanta wajen sayan jirgin yakin F-35 daga Amurka, yayin da yake cewa babu alaƙa tsakanin yarjejeniyar da wannan ciniki.
Hukumomin UAE sun ce babu wata alaƙar dakarun soji tsakaninsu da Isra'ila.
Shugaba Trump ya ce buƙatar UAE tana gaban teburinsa domin duba yiyuwar amincewa da ita.
Bugu da ƙari, UAE ta kwashe shekaru tana son sayen jirgin mara matuki da amurka ta kera MQ-9, sai dai tana ta fuskantar tutsu saboda yarjejeniyar makai.
Shugabannin Isra'ila a gefe guda
Wasu a Isra'ila na adawa da cinikin jirgin F-35 ga UAE, suna nuna damuwa kan yiwuwar raguwar ƙarfin sojinsu a yankin.
Dalili kuwa shi ne kaf a Gabas Ta Tsakiya Isra'ila ce kawai ke da jiragen F-35 - wanda aka fara kai wa shekara hudu baya, kuma yanzu suka tasamma samun guda 50 nan da 2024, kan kudin da za su iya kai wa dala miliiyan 100.
A 2018, dakarun Isra'ila sun ce kasar ce kawai ke amfani da F-35 a aikace-aikacen sojin yankin - wanda za ta iya amfani da su kan Iraniyawan da ke Syria.
Wannan dai ya janyo rikici, bayan ɓullar wani bidiyo da ya nuna jiragen na shawagi a samaniyar babban birnin Lebanon, Beirut, yayin da ake tsaka da zaman ɗar-ɗar tsakanin kasashen biyu.
Benny Gantz, wanda shi ne ministan tsaro da kuma abokin hamayyarsa Mista Netanyahu, sun garzaya Washington domin neman mafita kan cinikin.
A yanzu gwamnatin Isra'ila ta janye duka adawar da take yi wa UAE kan cinikin jirgi.
Gantz ya ce matsalar ba ta Hadaddiyar Daular Larabawa ba ce, a'a me sauran kasashen Larabawan yankin za su samu," ya shaida wa wata jaridar Isra'ila Yedioth Ahronoth, yayin da ake tsaka da rahoton cewa Saudiyya wadda ba a kai ga sanya hannu kan yarjejeniyar ba ita ma na son sayan jirgin F-35.
Ita ma Qatar ta mika ƙoƙon bararta, kazalika Bahrain da ta sabunta yarjejeniyarta da Isra'ila ita ma, ana rawaito cewa tana sa ran sayen wasu kayayyakin soji daga Amurka.
Da yawa na fargabar cewa safarar makamai za ta ƙaru a yankin.
Alamun ba da damar cin zarafi
"Ita ma Amurka na ta fafutukar sayar da makamanta a Gabas Ta Tsakiya," in ji William Hartung na cibiyar tsare-tsare ta ƙasa da ƙasa da ke Amurka.
Ya kira wannan yarjejeniyar Abraham a matsayin yarjejeniyar "sayar da makamai" yana mai cewa idan irinsu Saudiyya suka shiga cikin yarjejeniyar da irin su Sudan, to fa za su yi tsammanin ƙaruwar cininkin da Amurka ke yi na makamai.
Sana'a
A gefe daya kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama sun nuna damuwa kan yadda aka lalata Yemen, a yakin da ake yi tsakanin dakarun Houthi da Iran ke goyon baya da kuma masu goyon bayan gwamnati da ƙawancen Saudiyya ke jagoranta cikin har da Hadaddiyar Daular Larabawa.
"Cinikin makaman zai iya kara ta'azzara lamarin cin zarafi" in ji Radhya Almutawakel, shugaban kungiyar kare hakin dan adam ta Mwatawa.
"Ba ma rubuta yawan hare-haren da ake kai wa ta sama da suke sauka kan fararen hula... muna da wadanda muka ajiye sama da 500. A wasu har ɓaraguzan makaman da aka yi amfani da su muka tsinta - kuma mafi yawa an ƙera su ne a Amurka da Burtaniya ko Italiya".
"Sun yi amannar Amurka za ta taimaka musu za ta aiko musu da makamai," in ji Amutawakel, wanda ya yi wa kwamitin tsaro na MDD bayani kan cin zarafin dan adam a Yemen.
Mista Bronk, wani mai sharhi kan Al amuran tsaro ya ce, an daɗe UAE na son samun jirage marasa matuƙa daga Amurka, doi amfani da su a Yemen, domin samun damar murƙushe dakarun Houthi.
Yemen na ƙara zama wani fagen gwajin jirage marasa matuƙa kamar yadda wata ƙungiya mai yaƙi da bazuwar makamai ta Netherland ta bayyana.
Sai dai ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta ya musanta kai hari kan fararen hula a kasar.