Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Amurka na 2020: Yaushe ake bayyana sakamakon zaɓen Amurka?
Yau ake kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban Amurka. Kun shafe awa 10 a gaban talabijin kuna kuma da shige da fice a shafukan zumunta.
A gefe guda kuma, daga Trump har Biden ɗin kowannensu ya ƙi ya amsa shan kaye. Zuƙatan Amurkawa sun fara harzuƙa a zaɓe mai cike da ce-ce-ku-ce.
Tuni aka kai ƙara kan ƙuri'un da aka soke sannan kuma zanga-zanga ta ɓarke a ɗaukacin ƙasar. Nan gaba kaɗan kuma za a kai ƙra kotu domin raba gardama kan sakamakon zaɓen shugaban ƙsa.
Sai dai hakan ba za ta faru ba idan Amurkawa suka haƙura aka suka jira sakamako. Amma har zuwa yaushe za su jira? Wannan shi ne abin tambayar.
Mene ne na jira?
Ƙuri'un da aka kaɗa ta gidan waya.
A zaɓen 2016 na shugaban Amurka, mutum miliyan 33 ne suka jefa ƙuri'a ta akwatun gidan waya. A wannan karon saboda annobar korona, miliyan 82 ne suka nemi su kaɗa ƙuri'a ta gidan waya.
Amma da yake saura kwana ɗaya, jihohin ƙasar da dama na faɗi-tashin yadda za su yi da dokokin shekaru aru-aru da suka tsara lokacin da za a buɗe rumfar zaɓe ta gidan waya da sanda za a karɓa da sanda za a ƙirga su.
Misali, a Michigan - jihar da za a fafata sosai, inda kowanne ɗan takara ka iya lashewa - ana tsammanin mutum miliyan uku ne za su yi zaɓe ta gidan waya.
Sai dai kuma, ganin cewa sai ƙarfe 7:00 na safiyar ranar zaɓe za su fara ƙirga ƙuri'a, zai ɗuki jihar kwanaki kafin ta sanar da sakamako.
Tuni Trump ya dakatar da kasafin kuɗi na hukumar gidan waya ta US Postal Service bayan ya yi iƙirarin cewa zaɓe ta gian waya ka iya raunata yaƙin neman zaɓensa.
Bincike ya nuna cewa 'yan Democrats - jam'iyyar adawa - za su fi jefa ƙuri'a ta gidan waya.
Matsala ta gaba ita ce shari'a a gaban kotu.
Idan aka kusa bayyana sakamako, jihohi da dama za su fuskanci shari'o'i a gaban kotu game da wacce ƙuri'a ce aka soke, abin da zai sake kawo tsaikon faɗar sakamako.
Babban dalilin da ke sa a soke ƙuri'a shi ne idan ta zo a makare ta yadda ba za a iya ƙirga ta ba. Sauran dalilan sun haɗa da saka hannun da bai yi daidai ba ko kuma idan babu shafi na biyu a jikin ambulan ɗin.
A zaɓen 2016, Trump ya lashe jihar Michigan da ƙuri'u ƙalilan da ba su wuce 11,000 ba.
Idan ƙuri'un da aka ci zaɓe da su ba su da yawa, za a samu hatsaniya game da ƙuri'un da aka soke a jihohin da babu wanda yake da rinjayen magoya baya.
Ko za a iya samun sakamako a daren da aka gama kaɗa ƙuri'a?
Ƙwarai, duk irin jan ƙafa a kan ƙuri'un gidan waya. Zai yiwu wani ya samu nasara a daren. Amma fa tazarar ba za ta yi yawa ba.
Kafin mutum ya yi nasarar zama shugaban Amurka, dole ne sai ɗan takara ya bayar da tazarar ƙuri'ar musamman 270.
Hakan na faruwa ne saboda ba da zallar ƙuri'un da aka kaɗa ake cin zaɓe ba.
Ana bai wa kowacce jiha adadin ƙuri'ar musamman gwagwadon yawan al'ummarta - haka ake yin zaɓen a jihohi, saboda haka duk ɗan takarar da ya samu waɗannan ƙuri'u za su yi masa amfani sosai.
Yayin da ya rage saura kwana ɗaya, tuni Amurkawa milyan 69.5 suka jefa ƙuri'unsu ta gidan waya ko kuma da hannunsu.
Ƙaruwar da aka samu na nufin tuni aka kaɗa sama da ƙuri'un da aka kaɗa a baki ɗayan zaɓen 2016.
A 2016, Trump ya yi murnar lashe zaɓe tun da ƙarfe 7:30 na safe (agogon Najeriya) bayan jihar Wisconsin ta ba shi damar haura tazarar ƙuri'a 270 ta musamman da suke kira electoral votes wato kwamitocin masu zaben shugaban kasa.
Sai dai, ganin yawan ƙuri'un da aka samu a bana, jihohin da za a fafata ɗin ba lallai ne su iya bayyana sakamako ba a daren.
Michigan da Pennsylvania da Wisconsin na cikin jihohin da za a fafata sosai waɗanda kuma su kaɗai ne suke fara ƙirga ƙuri'u a ranar zaɓen.
Su ma za su fuskanci matsalolin gurfanarwa a gaban kotu ko kuma ta sake ƙirga ƙuri'un, idan har aka yi kankankan a sakamakon.
Sai dai, ana fatan samun samun sakamakon a jihar Florida.
A matsayinta na fagen daga - mai ƙuri'a 29 ta kwamitocin masu zaben shugaban kasa - Florida ce za ta tantance ko ɗan takara zai iya lashe zaben a daren.
Jihar na fara tantance ƙuri'un gidan waya kwana 40 kafin ranar zaɓe. Yayin da tuni suka ƙirga ƙuri'a miliyan 2.4, har yanzu akwai 'yan ƙuri'un da ba su kammala ƙirgawa ba, amma yiwuwar bayyana sakamakonsu ta fi yawa sama da sauran jihohin da za a fafata - wato inda kowane ɗan takara zai iya lashewa.
Idan Biden wanda ke kan gaba a ƙuri'un jin ra'ayin jama'a ya rasa Florida, to abu ne mawuyaci ya ci zaɓe a daren da aka kaɗa ƙuri'a.
Zai iya samun tazarar 270 idan aka haɗa da jihohin North Carolina da Arizona da Iowa da Ohio, amma fa cin zaɓe a wannan daren ya ta'allaƙa ne da sakamakon Florida.
Trump ne ke bin Biden a baya a ƙuri'ar jin ra'yin jama'a, saboda haka ko da ya ci Florida har yanzu sai ya jira sauran jihohin fafatawa da ba lallai ne su faɗi sakamako ba kafin ya yi nasara a daren.
Sai dai fa idan lissafin ba daidai ba ne. Wani bincike ya nuna cewa lissafin ka iya zama ba daidai ba.
Ko gidajen talabijin ɗin ƙasar za su iya bayyana sakamako a daren?
Ƙarfin da kafafen yaɗa labaran Amurka ke da shi a daren da aka kaɗa ƙuri'a abin tsoratarwa ne.
Gidajen talabijin na aiki da kamfanonin da ke bin masu kaɗa ƙuri'a domin tattara bayanai, saboda haka kowace kafa tana son ta zama ta farko da ta bayyana wanda ya yi nasara.
Da zarar gidajen talabijin sun sanar da wanda ya ci zaɓe, wanda aka kayar zai amsa shan kaye.
Amma ganin yadda aka kaɗa ƙuri'a ta gidan waya mai yawan gaske saboda annobar korona a bana, wajibi ne kafafen yaɗa labaran Amurka su yi jimirin tare da haƙuri a wannan daren.
Shekara 20 da suka gabata, duk da cewa an yi kankankan a ƙuri'un, gidajen talabiji da dama sun sanar da Gore a matsayin wanda ya lashe Florida ba Bush ba - kafin daga baya a ce Bush ne lashe.
Gore ya amsa shan kaye, amma daga baya sai aka gano cewa tazarar da ke tsakani ba ta da yawa. Gore ya janye kayen da ya sha.
Bayan kwana 36 da kuma hukuncin Kotun Ƙoli, Amurkawa sun gano cewa Gore ne ya lashe mafi yawan ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da shi kuma Bush ya lashe ƙuri'u na musamman da ake kira electoral college - saboda haka shi ne ya ci zaɓe.
Tuni annobar korona ta kassara Amurka a 2020 da kuma rarrabuwar kai kan fafutikar Black Lives Matter wato 'yancin baƙaƙen fata. Yanzu kuma wajibi ne su jira su ga sabon shugaban ƙasarsu.