Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kotu ta yanke hukuncin kisa kan mutumin da ke kashe mata da zanin gado a Fatakwal
Kotu ta yanke wa wani mutum wanda ke kashe mata masu zaman kansu, bayan ya gama kwanciya da su hukuncin kisa a birnin Fatakwal da ke kudancin Najeriya.
Mutumin mai suna Garacious David-West ɗan shekara 26, masu gabatar da ƙara sun ce yana aikata kisan ne ta hanyar maƙure ko shaƙe wuyan matan a ɗakin otel ɗin da yake kwanciya da su.
Tsakanin watan Yuli zuwa Satumba 2019 ya kashe mata 15.
Tara daga cikin kisan ya aikata su ne a jihar Ribas da ke kudancin Najeriya inda aka gudanar da shari'ar.
Alkali Adolphus Enebeli ya ce za a kashe shi ta hanyar rataya. Ɗaya daga cikin matan ta tsira daga harinsa, amma ba ta kasance shaida a lokacin shari'ar ba.
Mahukunta sun ce an neme ta an rasa duk da gargaɗin da aka yi mata kar ta fita daga jihar.
Ƴan sanda sun ce salon kisan iri guda ne - yana aikata zina da matan sannan sai ya ɗaure musu hannu da ƙafa da farin zanin gado.
Sannan yana kashe su ta hanyar shaƙesu da zanin gado, kamar yadda aka shaida wa kotun.
Ta yaya aka kama shi?
A farkon shigar da ƙara wanda babu wakilcin lauya daga ɓangarensa, David-West ya amsa ya aikata abin da ake tuhumarsa da shi, sai dai alƙali ya buƙaci a yi shari'a saboda ''girma laifin da ya aikata".
A lokacin, hukumomi sun yi tunanin akwai waɗanda yake aiki tare da su amma sai ya kasance ba a samu wata hujjar da ke tabbatar da hakan ba, yayin sauraron shari'ar.
Lokacin da kashe-kashen ya ƙaru a Satumba shekarar da ta gabata, al'umma sun fusata a Fatakwal don haka suka fito zanga-zangar buƙatar mahukunta su ɗau mataki.
A ranar 19 ga watan Satumba aka damƙe shi lokacin da yake ƙoƙarin fice wa daga Fatakwal yayin da masu bincike suka isa gare shi.
Na'urar naɗar hoto ta CCTV ta nuna shi lokacin da yake ƙoƙarin fice wa daga otel kuma hoton ya yi ta yawo a kafofin sada zumunta.
Jami'an tsaro sun gano shi a wata motar bas ta haya da ke hanyar zuwa Uyo daga jahar Akwa Ibom, mai nisan daƙiƙa 45 daga birnin Fatakwal.
Wane ne wannan mai kisan?
An haifi Gracious David-West a wani yankin masunta da ake kira Buguma a jihar Ribas, mai arziƙin mai.
Garin na da tarihin mahara da ke sata ko fasa bututan mai, ƴan sanda sun ce David-West mamba ne na wata ƙungiyar mafia da ake kira Greenlanders - wanda ake kuma kiran su da Dey Gbam, suna aiki tare da ƙungiyoyi masu ɗauke da bindigogi.
Waɗanda suka san shi sun shaida wa BBC cewa, shi kaɗai mahaifinsa ya haifa duk da cewa yana da mata da yawa, sai dai shi da mahaifiyarsa gida daban suke zaune.
A shekara ta 2003 mahaifiyarsa ta rasu, kuma tun daga wannan lokacin ba a san inda yake zaune ba.
Mahukunta sun ce an taɓa kama shi sau guda bisa laifin sata amma ba a tuhume shi ba.
"Ba mu sake ganinsa ba sai lokacin da hotuna ke yawo a shafukan sada zumunta a matsayin mai aikata kisa a Fatakwal," kamar yadda wasu daga Buguma suka shaida wa BBC.
Wadanda suka ganshi a kotu sun bayyana shi a matsayin mutumin da ba a gane shi.
"Yana da saurin fushi, da yawan yi wa alƙali kutse, sannan yana ƙoƙarin kare kansa duk da cewa yana da lauya," a cewar ɗan jarida Alwell Ene.
Yana amfani da otel mai araha, wanda babu tsaro mai ƙarfi da na'urar ɗaukar hoto na CCTV, a tsakiyar gari da ke birnin Fatakwal, a cewar ƴan sanda.
Akwai lokacin da ya kashe wata mace mai zaman kanta a wani ƙaramin otel da ke unguwar Rumuola a Fatakwal, wani fitaccen wuri mai haɗari a birnin.
Su waye suka faɗa a tarkonsa?
Baya ga sunayen mata tara da aka shaida, saura ba a san da su ba.
An same shi da laifi kan kisan matan tara a jihar Ribas tunda babu shaidu masu ƙarfi kan sauran mace-macen, a cewar mahukunta.
"Babu wanda ya fito daga ɓangaren sauran matan shida," mai gabatar da kara Chidi Eke ya faɗa wa BBC.
Amma ƴan sanda sun ce ya amsa shida daga cikin irin wannan kisa da ya aikata a Abia da Edo da Oyo da Imo da Legas.
- Babu dangi
- Babu abokai
- Matan da ya kashe a Fatakwal
- Maureen Ewuru
- Jennifer Nwokocha
- Linda Waripa
- Dorcas Francis
- Blessing Effiong
- Rose Samuel
- Kelechi Bridget Onuoha
- Patience Hamo
- Antonia Ibe
Wakiliyar BBC Karina Igonikon ta Fatakwal ta ce abokai da ƴan uwa mamatan ba su taɓa halartar zaman kotu ba, sai uban mutum guda da ya zo a rana ta farko ta shari'ar.
"Sai ya kasance kamar ba su da kowa, babu adireshi, babu wani abu da za a iya gano su da shi," a cewarta.
An samu saɓani kan bayanan matan, da kuma yadda suka rinƙa bin sa otel yana kashe su.
Masu bincike sun ce yana yaudarar waɗanɗa suka faɗa tarkonsa ta hanyar shaida musu cewa shi jami'in soja ne, da alƙawarta ba su kuɗi mai yawa idan suka amince da shi.
Ana daraja sojoji a Najeriya saboda karfin da suke da shi da facakar da wasu kan yi da kuɗaɗe.
Ɗaya daga cikin matan, Jennifer Nwokocha an ce ta iso Fatakwal ne daga Legas domin budirin zagayowar ranar haihuwarta.
"Sun haɗu a otel ɗin da take zama suka sha lemu tare da musayar lambar waya, sannan daga baya suka sake haɗuwa da dare inda ta gamu da mutuwarta," wani mai bincike ya shaida wa BBC.
Ƴan sanda sun ce yana yi wa matan barazana da wuƙa da hana su wata alamar ankararwa.
Kafin ya kashe su yana kwashe musu kuɗi da katin ATM da sauran abubuwa masu muhimmanci.
"Mun gano matan tsirara, a lanƙwashe da farar ƙyale an ɗaure musu wuya da hannu da ƙafa.
"Duk da cewa babu ƙwaƙarar hujja da ke nuna kisan na da alaƙa da tsafi, Ni dai ina gani akwai alaƙa," Mr Eke ya shaida wa BBC.
Wacce ta tsallake rijiya da baya
Benita Etim wata mai zaman kanta ce ƴar shekara 23 da ta tsallake rijiya da baya a irin wannan dare da yake kashe mata.
Sai dai ba ta halarta a gaban kotu ba domin ba da shaida, yayin da masu gabatar da ƙara suka ce ta tsere daga jihar Ribas bayan bayanan da ta bai wa ƴan sanda.
An faɗa mata cewa wataƙila a buƙace ta a kotu domin ba da shaida.
A wata tattaunawa da BBC a watan Satumban bara, ta ba da labarin yadda wani mutum da suka haɗu a ranar 18 ga watan Aguta ya ɗaure ta a ɗakin otel.
Babu sahihan bayanai da ke tabbatar da ko mutumin David-West ne, amma dai salon labarinta da abin da ta shaida ta gani - farin zanin gado, wuƙa da sata na da kamanceceniya da abin da ya ke aikatawa.
Bayananta na ƙabilarsa da halittarsa ya yi kama da na bayanan ƴan sanda.
Ta ba da labarin yadda ya yi mata fyaɗe babu kwaroron roba, kafin daga bisani ya yi mata barazana da wuƙa da ɗaure ta a jikin kujera.
"Ya kekketa zanin gado ƙyalle-ƙyalle sai ya haɗe hannu na wuri guda ya ɗaure da ƙafata a jikin kujera sai ya yi amfani da sauran ƙyalen ya ɗaure mun baki.
"Na yi ta ihu amma babu wanda ya ji ni saboda ya ƙure muryar talabijin sannan akwai injin janerato kusa da ɗakin, a cewarta. "Na roke shi kada ya kashe ni."
A wannan lokaci sai ya fice daga ɗakin da wayarta kuma bai sake dawowa ba.
Ma'aikatan otel ɗin sun gano ta washe gari bayan ta yi ƙoƙari da dabaru ta cire ƙyallen da ya ɗaure bakinta da shi sannan ta rinƙa ihun a kawo mata ɗauki.