Zaɓen Rasha: Mai goge-gogen da ta kunyata ɗan takarar Shugaba Putin zama Magajin Gari

Marina Udgodskaya

Asalin hoton, Yevgeny Zhuravlev / BBC

    • Marubuci, Daga Petr Kozlov
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian, Povalikhino

A baya dai Marina Udgodskaya, wata mai goge-goge ce a wani ofishin ƙaramar hukuma da ke wani ƙaramin ƙauyen Povalikhino, mai nisan kilomita 400 a arewa maso gabashin birnin Moscow.

Rayuwarta ta sauya a lokacin da aka buƙace ta da ta tsaya a zaɓen yankin a matsayin "cikon benci", saboda ya sa ƙuri'un su kasance daidai da tsarin dimokaraɗiyya.

Kamata ya yi a ce kawai a yi amfani da ita wajen cikon benci - a bisa doka, ya kamata a ce zaɓen kasar ta Rasha ya samu a ƙalla 'yan takara biyu a kan takardun kaɗa ƙuri'ar- amma kuma ta samu galaba da gagarumin rinjaye, don haka za ta jagoranci wannan ƙaramar gunduma.

Wakilin BBC a kasar ta Rasha Petr Kozlov ya yi bulaguro zuwa ƙauyen na Povalikhino don gano yadda to Udgodskaya ta tashi daga mai goge-gogen Magajin Gari zuwa mulkar ofishin.

Marina Udgodskaya approaches the office

Asalin hoton, Yevgeny Zhuravlev / BBC

Kauyen Povalikhino ba wuri ne da yake kama da inda za a samu sauyin dimokraɗiyya ba. Shi ne tsakiyar wasu rukunin ƙauyuka a yankin Kostroma, inda da yawansu babu mazauna sosai a ciki.

Wasu mutane na samun kudaden shiga ta hanyar sana'ar sarrafa itacen timber, wasu kuma suna noma da harkokin yawon bude ido a tafkin Chukhloma da ke kusa. Wuri ne da babu hayaniya kuma karkare ce - ba a samun sigina a wayar salula.

Amma kuma wannan wuri ne da babu zato babu tsammani mutanen yankin suka zaɓi mace wacce ta tsaya takara ne kawai don saboda magajin garin yankin mai ci ya nemi ta tsaya.

Marina Udgodskaya ta samu horo ne a fannin mataimakiyar mai sayar da kaya a shaguna, amma ba ta samu irin wannan aikin a kauyen na Povalikhino ba - ƙananan shaguna biyu ne kawai a ƙauyen.

Tun bayan da ta kammala karatu, tana lura da iyalanta har ma da daukacin gidanta da lambu da kuma kiwon dabbobi - tana da agwagi da ƙwa-ƙwa da kaji da zomaye, har ma da karnuka da maguba.

Ducks and geese

Asalin hoton, Yevgeny Zhuravlev / BBC

Tana kuma aiki a matsayin mai goge-goge a ofishin karamar hukuma, kana a lokacin hunturu a matsayin mai lura da makamashi, tana tabbatar da cewa murhun ƙona itacen da ke ofishin magajin garin na ci sosai.

Abin mamaki ne a gare ta bayan da ta ce ba ta taɓa gwada yaƙin neman zaɓe ba, kuma ba ta taɓa tsammanin za ta samu galaba ba.

Wani dan jam'iyar adawa Dmitry Gudkov ya taya Udgodskaya murnar samun galaba a zaɓen a wani shafin rubuce-rubucensa na yanar gizo na, inda ya ce wannan na nuna cewa masu kada ƙuri'a a yankin sun dawo daga rakiyar jam'iyar United Russia, ta Shugaba Putin.

'Yar takarar ba-zata

Ex-mayor Nikolai Loktev

Asalin hoton, Yevgeny Zhuravlev / BBC

Abin mamakin shi ne, magajin garin mai ci mai shekaru 53 Nikolai Loktev, shi ne ya ɗauko ta a matsayin abokiyar karawarsa don cika ƙa'idar doka, yayin da yake shirin sake tsayawa a zaɓen watan Satumbar.

Wani tsohon ɗan sanda, Loktev ya kasance magajin gari na yankin karamar hukumar har na tsawon shekara biyar.

Mutane da dama na ganin kimar shi a ƙauyen, sun kuma yi amanna cewa yana tafiyar da mulkin yankin yadda ya kamata.

"Kwarai, ni na ce Marina Udgodskaya ta tsaya takara," ya bayyana wa BBC.

"A ƙashin gaskiya, na buƙaci wasu mutanen ma, amma suka ƙi amincewa- idan da a ce akwai wata hanya ta daban, da ban buƙaci ta tsaya ba.

''Amma ni ban ga wani abun ban mamaki ba ko kuma ba kasafai ba a galabar da ta samu. Na jinjina mata! Na yi matuƙar farin ciki cewa ta tsaya takara kuma don mutane sun mara mata baya - ai ba damuwa.''

Ya ce yana tunanin barin ƙauyen ya koma wani ƙaramin gari ya nemi aiki a can. Loktev ya yi ta kaucewa yin magana a kan batun halin da ake ciki a siyasance yana mai dada kaucewa da batun da ake cewa wannan wani ci baya ne ga Jam'iyyar United Russia, ta Shugaba Vladimir Putin.

"Babu daya daga cikinmu (Ugodskaya da shi kansa da dan wata jam'iyya ce.''

Amma duk da haka, ya tsaya zaɓe a matsayin wakili a jami'iyyar ta United Russia, wacce ta mamaye ɗaukacin tsarin siyasar kasar.

Labarin ɗaukakarta

The BBC's Petr Kozlov holds a microphone towards Marina Udgodskaya with other journalists around

Asalin hoton, Yevgeny Zhuravlev / BBC

An rantsar da Udgodskaya a matsayin magajin garin ƙauyen Povalikhino da kuma kewayen gundumar.

'Yan jaridun yankin da kadan daga cikin wakilan kafafen yada labarai na Birnin Moscow da suka yi tururuwa zuwa ƙauyen don su yi tozali da tauraruwar siyasar kasar Rasha da Allah ya yi wa luɗufi.

Ta tsaya a nutse tana amsa tambayoyi da dama daga manema labarai; ''Ina jin dadi, babu wata damuwa. Da farko na ɗan shiga rudani, amma yanzu ina ji na sumul.

Ga takardarta ta shaidar zama magajin gari. Sam, zancen barin muƙamin bai taso ba, babu wanda ya tilasta ni in tsaya, ni na amince da kaina. Idan dai mutane ne suka zaɓe ni - zan yi musu aiki,'' ta ce.

Mintoci kadan bayan rantsar da ita, ta kame a bayan mota wanda direban ƙaramar hukumar ke tuƙawa.

'Yan jarida su bi ta a baya, inda farfajiyar gidan mai goyon bayan Marina ta zama dandalin ɗaukar hotuna.

Marina Udgodskaya (right) and a woman who voted for her

Asalin hoton, Yevgeny Zhuravlev / BBC

Da alama wannan mata ta dokanta ta ga Udgodskaya ta fara gudanar da aikinta.

"Shakka babu, na zaɓi Marina, mu duka mun yarda da ita. Tana da basira kuma za ta kai ga nasara!'' in ji ta.

Ba da jimawa ba Udgodskaya za ta fara samun horo kan harkokin mulki, za ta koyi yadda kasafin kuɗin yankin yake aiki da kuma mulkin ƙaramar gundumarta.

Menene ra'ayin mutanen ƙauyen?

Mun yi tattaki a kewayen Povalikhino don auna ra'ayoyin mutanen kauyen. A wani shagon yankin na fara tattaunawa da wata dattijuwa mai sanye da kwat mai ruwan ɗorawa wacce abin mamaki ashe tana da dangantaka da Udgodskaya.

Kozlov holds a microphone towards Udgodskaya's mother-in-law

Asalin hoton, Yevgeny Zhuravlev / BBC

"Wannan yarinyar macen surukata ce,'' ta ce, ''Na tabbata za ta iya wannan aiki sosai, ya kamata ta yi shi ta kuma ci gaba da yi. In ba haka ba - dole ta tafi,'' ta sake jadddawa.

Wata mata sanye da ɗankwali kaya ruwan hoda ta bayyana cewa tana matuƙar fari ciki cewa Marina ta samu galaba.

A woman who supports Udgodskaya speaks to the camera

Asalin hoton, Yevgeny Zhuravlev / BBC

"Muna buƙatar sabbin fuskoki. Yana da kyau cewa za ta samu damar sauya wani abu, ta gwada sa'arta wajen mulkar ƙauyenmu!'' ta ce.

Wani mutum da ake kira Mikhail wanda ke ta cin wata gyaɗa yayin da yake magana da ni, ya ƙara jaddada batun nata da ƙarfin murya.

An Udgodskaya supporter stands by a roadside

Asalin hoton, Yevgeny Zhuravlev / BBC

"Za ta samu gogewa sannu a hankali! Za ta koyi komai. Tana da ƙuruciya da kyau da kuma fara'a,'' ya ce.

"A cikin diflomasiyya, ya kuma ƙara da cewa shi ma Nikolai Loktev mutumin kirki ne.''

Wani mutumin ƙauyen, Ivan shi yana cikin 'yan '' a- jira -a gani ne'' ne. Ya ce bai kaɗa ƙuri'a ba, kuma bai damu da tsohon magajin garin ba.

"Duk abinda ya kamata ya yi (Loktev) shi ne ya kunna fitilun kan titinan ƙauyenmu a kan lokaci Amma bai iya yin hakan ba'' Ivan ya ce.

A man talks to a reporter in a boatyard

Asalin hoton, Yevgeny Zhuravlev / BBC

Lokacin da na tambayi Ivan, me yasa bai kaɗa ƙuri'a ba, ya ce ya taɓa mara wa wata jam'iya baya a farkon shekarar 1990 kan alƙawarin da ya yi na rage farashin barasar Vodka.

"Amma daga bisani ashe ba da gaske suke yi ba'' ya ce, yana girgiza kansa cikin nuna rashin jin daɗi.

Amma kuma, Ivan ya bayyana gaskiyar cewa ya daina shan giya tun daga lokacin. Yanzu ya fi ƙaunar ɗaukar faya-fayen bidiyo da ƙera kwale-kwalen da masu yawon bude idon ke amfani da su a kan tafkin Chukhloma, da ke yankin.

Me hakan yake nufi ga jam'iyyar Shugaba Putin?

Jam'iyyar adawar kasar Rasha da wuri ta fito ta bayyana galabar da Udgodskaya ta samu a matsayin koma baya ga jam'iyya mai mulki ta United Russia.

Ko shakka babu an sha mamaki, bayan da labari ya bazu kamar wutar daji cewa mai goge-goge, kuma mace a wata ƙaramar gunduma ta kayar da magajin garin yankin mai ci wanda ya tsaya a jam'iyyar Shugaba Putin - kuma ba tare da ta yi wani yaƙin neman zaɓe ba.

BBC ta gano cewa wasu an gudanar da wasu muhimman bincike a yankin karamar hukumar mulki a Kostroma, inda gwamnan lardin ke yin nuni ga darasin da za a koya daga wannan babban kaye.

Labarin ya kai ga birnin Moscow kuma shugabar hukumar zaben kasar ta Russia (CEC) ta mayar da martani.

"Haka ne, ita (Udgodskaya) ta tsaya takara a matsayin'' cikon benci,'' in ji shugabar Ella Pamfilova, "amma babu babu wani abin damuwa kan haka.

"Mutanen ƙauyenta sun zaɓe ta, a matsayinta na mai aikin goge-goge, ban taɓa tsammani ba.''

A dog outside a house in a rural Russian village

Asalin hoton, Yevgeny Zhuravlev / BBC

A daidai wannan lokaci kuma, shugaban yankin na jam'iyyar United Russia Galina Poliakova ya shaida wa BBC cewa duk da wannan hali na ''ba kasafai ba'', ba za a samu wata matsala ba.

"Marina za ta samu mai saka ta a hanya, kamar yadda sauran shugabannin gundumomi suka samu. Ƙwarai, ba abu ne da aka saba gani ba, amma ba abin baƘin ciki ba ne, in ji Poliakova.

"Babu wani abin bakin ciki ga faduwar Ɗan takarar jam'iYyar United Russia - mutane kan zaƁi mutum ne, ba jam'iyya ba.

''Me yiwuwa, tana da mu'amala mai kyau da jama'a tana kuma da basirar kasuwanciSu. Kana tsohon magajin garin bai gano dabarar ba.''

Dabarun zaɓe

An office building with a Russian flag flying outside

Asalin hoton, Yevgeny Zhuravlev / BBC

Duk da batun dabarun zaɓe - mara wa duk wani ɗan takara baya da ba na jam'iyyar United Russia ba - abu ne da ɗan jam'iyyar adawa Alexei Navalny ya amince cewa zai sauya yanayin mulki.

Karfafa dabarun zaɓe shi ne daya daga cikin burin tafiyarsa zuwa birnin Tomsk, na ƙasar Siberia inda aka saka wa Navalny guba a cikin watan Agusta, inda ya tsallake rijiya da baya.

Tuni ya zari Shugaba Vladimir Putin ta hannu wajen saka masa gubar.

Povalikhino, da ke yankin Kostroma, ka iya mara wa siyasar Alexei Navalny baya ko kuwa akasin haka.

Amma gaskiyar lamarin - wannan ƙaramar gunduma ta zaɓi sabuwar fuska, Marina Udgodskaya, inda ta samu gagarumin rinjaye fiye da yadda ake tsammani.

Trees surround the buildings in a small Russian village

Asalin hoton, Yevgeny Zhuravlev / BBC

Ko sauran 'yan garuruwa da ƙauyukan ƙasar ta Rasha za su bi sahun wannan hanya da ta kawo sauyi?