Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Trump da Biden: Yadda ta kaya a muhawarar zaɓen Amurka na 2020 ta farko
An kammala muhawarar farko cikin muhawarori uku tsakanin Donald Trump na jam'iyyar Republican da Joe Biden 'yan takarar muƙamin shugaban ƙasar Amurka na shekarar 2020.
Tun kafin a je ko'ina, 'yan takarar biyu suka far wa juna, inda suka kaure da baƙaƙen maganganu da zage-zagen juna.
Mr Biden ya bayyana Shugaba Trump a matsayin "shashasha" sannan ya ce masa "rufe bakinka". Mr Trump ya bijiro da batun shan ƙwayoyin ɗan gidan Biden.
Ra'ayoyin jama'a sun nuna cewa Mr Biden ya yi nasara a muhawarar da kashi 48, yayin da Mr Trump ya samu kashi 41, sannan kashi 10 suka ce 'yan takarar biyu sun yi kankankan.
Babban ɗan jarida Chris Wallace na tashar talabijin na Fox ne ya jagoranci muhawarar, kuma ya tambayi 'yan takararar tambayoyi shida-shida cikin batutuwa shida, inda aka ba su minti 15 domin amsa tambayoyin da mayar da martani.
Mutane ƙalilan ne aka bari suka halarci zaman, ciki har da iyalan 'yan takarar na kusa da su. Matar Mista Trump Melani da matar Joe Biden Jill sun harci muhawarar.
Ba a amincewa wadanda ke cikin ɗakin taron yin magana ko shewa ba domin nuna goyon bayansa ga wanda suke goyoin baya.
Saboda cutar korona an hana 'yan takarar gaisawa da juna, kuma an tabbatar da tazara tsakaninsu.
Wannan ce muhawara ta farko cikin ukun da za su yi gabanin zaɓen shugaban Amurka ranar 3 ga watan Nuwamba.
Tambayar farko: Kotun Ƙolin Amurka
Wanda ya jagoranci muhawara, ɗan jarida Chris Wallace ya buɗe muhawarar da tambayarsu dalilin da ya sa za a amince ma Mista Trump ya naɗa sabuwar alƙalin Kotun Ƙolin Amurka da za ta maye gurbin wadda ta mutu ana daf da zaɓe.
Mista Trump: "Saboda mu ne muka lashe zaɓen shugaban ƙasa. Cin zabe na da tasiri."
"Mu ne muka lashe zaɓen saboda haka mu ke da damar naɗa alkalin kotun ƙolin".
Amma Mista Biden ya buƙaci a ƙyale Amurkawa su bayyana ra'ayinsu a lokacin wannan zaɓen, inda ya ce wanda ya lashe zaɓen ne ke da hurumin naɗa sabuwar alkalin.
"Wannan ce kawai hanyar da Amurkawa za su iya bayyana ra'ayinsu - ta zabar wanda suka amince ya jagoranci kasar nan a mukamin shugaban kasa da mataimakinsa."
Trump ya kara da Chris Wallace
Amma ba a jima ba abubuwa suka rincaɓe, bayan da Chris Wallace ya sanar da Mista Trump cewa bai bayyana shirin samar da kiwon lafiya da ya ce zai bayyana ba wanda ya daɗe yana gaya wa Amurkawa zai yi tun hawan sa karagar mulki.
Mista Trump ya amsa da cewa: "Na yi mana. Lallai na yi."
"Ni ne mai jagorantar wannan muhawarar kuma ina buƙatar ka da ka amsa tambayar da na yi maka," in ji Mista Wallace, kuma ya soki wata dokar shugaban kasa da Mista Trump ya rattaba hannu a kai a farkon wannan watan.
Daga nan ne fa Mista Trump ya mayar wa Mista Wallace da magana, "Da alama ni da kai za mu yi wannan muhawarar, ba ni da Joe Biden ba, amma ba komai."
Biden ga Trump - 'Rufe mana baki, Mallam'
A ɗaya ɓangaren kuwa, shi ma Joe Biden ya fusata da halayyar Mista Trump ta cin dunduniyarsa yayin da yake magana da kuma yadda yake ƙoƙarin amsa tambayar da aka yi masa.
Lamarin ya kai ga sai da Joe Biden ya cewa Mista Trump: "Rufe mana baki kai wannan mutumin," kuma ya ƙ ara da cewa "Ci gaba da ɓaɓatu Malam".
Covid-19 - tasirin annobar korona
Yayin da aka tabbatar cewa fiye da mutum miliyan bakwai ne suka kamu da cutar a Amurka, kuma fiye da mutum 200,000 sun rasa rayukansu, Wallace ya tambayi 'yan takarar abin da kowannensu zai yi a shekara mai zuwa domin kawo ƙ arshen annobar.
Mista Biden ya ce: "Shugaban ƙasar nan ba shi da shirin tunkarar matsalar."
Wallace ga 'yan takarar: Ku daina cacar-baki
Bayan sa'a guda da fara muhawarar - wadda cacar-baki da taƙaddama da zage-zage suka mamaye - Chris Wallace ya roki 'yan takarar biyu su saka wa bakunansu linzami.
"Haba malamai! Na ƙ i jinin ɗaga muryata, saboda haka ya zan iya bambanta kaina da ku?"
Ya kuma ce kasar za ta fi amfana idan suka nuna dattaku. Amma duk da haka sai da Mista Trump ya katse shi, lamarin da ya tilasta masa cewa shi ne babban mai laifi idan aka kwatanta shi da Mista Biden.
'Na biya miliyoyin daloli na haraji'
Kan batun tattalin arziki kuwa, an taɓo batun harajin Mista Trump.
Wallace ya tambayi Trump kai tsaye: "Da gaske ne $750 kacal ka biya a matsayin haraji a shekarar 2017 da 2016?
"Miliyoyin daloli na biya", in ji Trump. "Na biya dala miliyan 38 a shekara ɗaya, a wata shekarar kuma na biya dala miliyan 27."
Sai dai Biden ya ƙalubalance shi da ya bayyana harajin nasa, kuma Trump ya ce za ka ga bayanan bayan an kammala aiki a kansu.
Ra'ayin jama'a: Biden ne ke kan gaba. Amma Amurka ce ta yi rashi.
Wani ra'ayin jama'a da tashar talabijin ta CBS News da BBC News suka gudanar jim kadan bayan an kammala muhawarar ya tabbatar da JOe BIden a matsayin wanda yayi nasara a wannan muhawarar ta farko.
Kashi 48 cikin 100 na wadanda aka tambaya sun ce Biden ne ke kan gaba, kashi 41 cikin 100 kuwa sun ce Trump ne ya lashe muhawarar, inda kashi 10 cikin 100 suka ce babu wanda ya sami galaba cikin 'yan takarar biyu.
Amma masu sharhi kan al'amuran siyasar Amurka na ganin wannan ƙazamar muhawara ce da ta raunata Amurka - kuma wannan ya tabbatar da ra'ayin al'ummar ƙasar da aka ɗauka.